Labari Da Ɗuminsa: Ƙungiyar Malaman Kwalejin Kimiyya Da Fasaha Ta Janye Yajin Aiki

Labari Da Ɗuminsa: Ƙungiyar Malaman Kwalejin Kimiyya Da Fasaha Ta Janye Yajin Aiki

- Malaman Kwalejojin Fasaha sun dakatar da yajin aikin da suke shafe watanni suna yi

- Malaman karkashin kungiyarsu ta ASUP sun dakatar da yajin aikin ne a ranar Laraba 9 ga watan Yuni

- ASUP ta ce ta dakatar da yajin aikin ne domin bawa gwamnati wa'adin watanni uku da cika alkawurran da ke cikin yarjejeniyar da suka rattba hannu a kai

Malaman Kwalejin Kimiyya da Fasaha karkashin kungiyarsu ta ASUP sun janye yajin aikin da suka kwashe kwanaki 65 suna yi.

Sakataren kungiyar ASUP na kasar, Abdullahi Yalwa ne ya sanar da hakan a ranar Talata, Daily Trust ta ruwaito.

Labari Da Ɗuminsa: Ƙungiyar Malaman Kwalejin Kimiyya Da Fasaha Ta Janye Yajin Aiki
Labari Da Ɗuminsa: Ƙungiyar Malaman Kwalejin Kimiyya Da Fasaha Ta Janye Yajin Aiki
Asali: Original

DUBA WANNAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Masu Garkuwa Sun Sace Malamar Makaranta a Abuja

Ya ce sun janye yajin aikin ne bayan bita kan rahotanni da ke nuna an fara aiwatar da abubuwan da ke cikin yarjejeniya da suka yi tsakanin su da gwamnatin tarayya.

A watan Afirilu ne malaman suka tafi yajin aikin domin neman a biya musu wasu bukatu da suka shafi rashin kayayyakin aiki da albashi da alawus da suke bi.

Da ya ke yi wa manema labarai jawabi a Abuja, Yalwa ya yi bayanin cewa ba janye yajin aikin suka yi ba, sun dakatar ne kawai na tsawon watanni uku domin bawa gwamnati daman aiwatar da abubuwan da ke cikin yarjejeniyar da suka rattaba hannu a kai a ranar 27 ga watan Afrilun 2021.

Kungiyar ta umurci mambobinta su koma aiki a ranar Alhamis, tana mai cewa ta yi la'akari ne da kiraye-kirayen da gwamnati, masu sarautun gargajiya, yan majalisa, shugabannin kwamitocin kwalejojin Fasaha da mutanen kasa suka yi game da batun.

DUBA WANNAN: Matar El-Rufai: A Shirye Nake In Mutu Hannun Masu Garkuwa, Kada a Biya Kuɗin Fansa Idan An Sace Ni

Ya kuma ce dokar da majalisa ta yi na kwana-kwanan nan na yin daidaito tsakanin kwalin HND da Digiri na cikin dalilan dakatar da yajin aikin.

Kungiyar ta ce tana fatan dakatarwar na watanni uku zai bawa gwamnati damar cika sauran abubuwan da ke cikin yarjejeniyar.

A wani rahoton daban kun ji cewa Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta dauki sabbin ma'aikata 10,000 a ma'aikatu da hukumomin jihar a yayin da ta ke rage yawan ma'aikata a wasu hukumomin, rahoton The Cable.

Muyiwa Adekeye, mashawarcin gwamna Nasir El-Rufai kan watsa labarai ne ya bada wannan sanarwar a ranar Litinin.

Adekeye ya ce za a dauki ma'aikatan ne cikin wadanda aka tantance yayin aikin daukan sabbin ma'aikata a jihar kamar yadda Sun News ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164