Oba Olakulehin: Babban Basarake a Najeriya da Ya Rasu Kwana 3 da Cika Shekaru 90
- Sarkin Ibadan, Oba Owolabi Olakulehin, ya rasu a ranar Litinin, 7 ga watan Yulin 2025, bayan kwana uku da cika shekaru 90 a duniya
- An rahoto cewa Olakulehin ya karɓi sandar mulki daga gwamnan Oyo, Seyi Makinde, a Yulin 2024, inda ya zama sarkin Ibadan na 43
- Za a ci gaba da tunawa da Oba Olakulehin kan hidimarsa ga al'umma, kiyaye al'adu, da kuma kokarinsa na ci gaban mutanen Ibadan
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ibadan – An shiga tsananin jimami a Oyo, yayin da sarkin kasar Ibadan, Oba Owolabi Olakulehin, ya rasu yana da shekaru 90 a duniya.
Oba Olakulehin, wanda ya hau gadon sarauta a watan Yulin 2024, ya rasu a safiyar Litinin, 7 ga Yulin 2025, bayan mulkinsa na shekara guda a matsayin sarki.

Source: Twitter
Rahoton jaridar Tribune ya nuna cewa an haifi marigayi Oba Olakulehin a ranar 5 ga Yulin 1935, kuma rasuwarsa ta zo ne kwana biyu kacal bayan cika shekaru 90 da haihuwarsa.
An ce a kwanaki biyu da suka gabata, an shirya wani gagarumin biki da manyan jiga-jigai daga faɗin Najeriya suka halarta domin taya sarkin murna.
Olubadan ya cika shekaru 90 kafin rasuwarsa
Oba Olakulehin ya karɓi sandar mulki daga gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, a ranar 12 ga Yulin 2024, inda ya zama sarkin Ibadan na 43 a wani gagarumin taro da aka shirya.
Ya hau gadon sarauta daga tsatson gidan sarautar Balogun, inda ya gaji Oba Moshood Lekan Balogun, wanda ya rasu yana da shekaru 81 a ranar 14 ga Maris, 2024.
Mulkinsa ya kasance cike da zaman lafiya, hikima, da kuma kwazo ga ci gaban Ibadan, inda ya samu yabo daga shugabanni kamar Shugaba Bola Tinubu kan rawar da ya taka wajen kiyaye al'adu.
An yi bikin cika shekaru 90 na Oba Olakulehin tare da yabo daga Gwamna Makinde, Sanata Sharafadeen Alli, da sauran su, waɗanda suka yaba da shugabancinsa mai tasiri da kuma kwazonsa ga haɗin kai.
Za a fara shirye-shiryen nadin sabon sarki
Daga cikin ayyukan hada kan al'umma da Olubadan ya gudanar akwai kafa kofin kwallon kafa na Olubadan Olakulehin, kuma ya bada shawarar gina bandakunan jama'a don rage yin ba-haya a bainar jama'a.

Source: UGC
Majalisar cibiyar ƴan asalin Ibadan ta bayyana Oba Olakulehin a matsayin alamar haɗin kai, wanda hikima da tawali'unsa suka haɓaka zaman lafiya da ci gaba a Ibadanland.
Yayin da Ibadan ke shirin yin zaman makoki, ana sa ran za a ci gaba da tunawa da Sarki Olakulehin da irin hidimarsa ga jama'a, kiyaye al'adu, da ci gaban al'umma.
Vanguard ta rahoto cewa nan ba da jimawa ba majalisar nada sarkin Ibadan za ta fara karbar bukatu daga masu sha'awar zama sarki don tantancewa tare da mikawa gwamna don ya amince.
Sarkin Ibadan, Lekan Balogun ya rasu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, sarkin ƙasar Ibadan, Olubadan na Ibadanland, Oba Lekan Balogun, ya rasu yana da shekaru 82 a duniya.

Kara karanta wannan
'Zuwansa alheri ne': Ribadu ya faɗi yadda Tinubu ya ceto Najeriya daga tarwatsewa
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa sarkin ya rasu ne a ranar Alhamis 14 ga Maris, 2024 a asibitin jami'ar UCH da ke Ibadan.
Gwamna Makinde ya aike da sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin, masarautar Ibadanland, majalisar sarakunan Oyo, da daukacin al’ummar jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

