Ana Tsaka da Rikicin Sarautar Kano, Gwamna Ya Naɗa Sabon Sarki Mai Martaba

Ana Tsaka da Rikicin Sarautar Kano, Gwamna Ya Naɗa Sabon Sarki Mai Martaba

  • Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya amince da naɗin Oba Owolabi Olakulehin a matsayin sabon sarkin ƙasar Ibadan watau Olubadan
  • Hakan ya biyo bayan rasuwar tsohon Olubadan, Oba Balogun, wanda Allah ya karɓi rayuwarsa ranar 14 ga watan Maris, 2024
  • A wurin taron da gwamnatinsa ta shirya, Makinde ya ce ya ga sakon majalisar naɗa sarki kuma ya amince da wanda suka zaɓa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Oyo - Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya bayyana cewa ya amince da naɗin, Oba Owolabi Olakulehin a matsayin sabon sarkin Ibadanland watau Olubadan.

Makinde ya amince da naɗin sabon sarkin mai daraja biyo bayan shawarin da ya karɓa daga majalisar masarautar.

Kara karanta wannan

Ministoci 3 da manyan jiga-jigai sun shiga taron kwamitin mafi ƙarancin albashi a Abuja

Gwamna Seyi Makinde.
Gwamna Makinde ya amince da nadin sabon Olubadan na Ibadanland a jihar Oyo Hoto: Seyi Makinde
Asali: Facebook

Gwamnan ya faɗi haka ne a wurin taro na musamman da gwamnatin Oyo ta shirya game da rasuwar marigayi Olubadan, Oba Olalekan Balogun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Leadership ta tattaro, Balogun ya rasu ne ranar 14 ga watan Maris, 2024 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Gwamma Makinde ya naɗa Olubadan

Gwamna Makinde ya ce ya ga shawarwarin da majalisar masu naɗin sarkin suka aiko masa kuma ya amince da wanda suka zaɓo, rahoton Tribune Nigeria.

"Na yarda da hakan kuma matuƙar Olubadan mai jiran gado, Oba Owolabi Olakulehin, yana cikin ƙoshin lafiya za a naɗa shi a karagar mulki tun da an bi ƙa'ida," in ji shi.

Gwamna ya tuna da Marigayi Balogun

Makinde ya ce marigayi Olubadan ya yi rayuwa mai gamsarwa, inda ya ƙara da cewa shi da marigayi sun yi abubuwan da mutane da yawa ke tunanin ba za su taba yiwuwa ba.

Kara karanta wannan

Sanusi II Vs Aminu: Jerin muhimman wurare 4 da Gwamnatin Abba ta yi kama da ta Ganduje

"Ni da Oba Balogun mun gyara dokar naɗin sarauta a Ibadan wanda ya haɗa har da naɗin Olubadan."

Tsohon babban hafsan sojojin ƙasa (COAS), Lt.-Gen. Tukur Yusuf Buratai (rtd), ya bayyana Balogun a matsayin mutumin kirki mai son taimakon jama’a.

Buratai ya ƙara da cewa Marigayi Balogun ya yi wa jihar Oyo da Najeriya baki ɗaya hidima, ya taimakawa al'umma ta hanya daban-daban a lokacin rayuwarsa.

Bola Tinubu ya yabawa Makinde

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci gwamnonin jihohin ƙasar nan su yi koyi da Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo.

Tinubu wanda mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya wakilta ya ce jikoki masu tasowa ba zasu manta da Gwamna Makinde ba

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel