'Yan Kasuwa Sun Ƙara Kuɗin Gas Ɗin Girki, 5kg Ya Haura N8000 a Wasu Jihohin Najeriya

'Yan Kasuwa Sun Ƙara Kuɗin Gas Ɗin Girki, 5kg Ya Haura N8000 a Wasu Jihohin Najeriya

  • Hukumar NBS ta ce farashin kilo 5 na gas din girki ya tashi daga N7,885.60 zuwa N8,167.43 a watan Mayun 2025 a wasu jihohin Najeriya
  • Jihohin Abia, Ebonyi da Rivers sun fi tsadar kilo 5 na gas, yayin da aka fi samunsa da araha a Oyo, Niger da Plateau, inji rahoton hukumar NBS
  • Yayin da Legit Hausa ta ji ra'ayin wasu 'yan Najeriya, rahoton na NBS ya nuna cewa farashin kilo 12.5 ya fi tsada a Delta, Abia da Ebonyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta bayyana cewa farashin gas din girki mai nauyin kilo 5 ya karu daga N7,885.60 a watan Afrilu zuwa N8,167.43 a watan Mayun 2025.

Wannan na ƙunshe ne a cikin rahoton “farashin gas din girki” na watan Mayun 2025 da hukumar ta fitar a ranar Alhamis, 3 ga Yunin 2025, a birnin Abuja.

Kara karanta wannan

'Zuwansa alheri ne': Ribadu ya faɗi yadda Tinubu ya ceto Najeriya daga tarwatsewa

Hukumar NBS ta ce an fi samun tsadar gas din girki a Abia, inda kilo 5 ya haura N8000 a Mayun 2025.
Hukumar NBS ta fitar da rahoton farashin gas din girki na watan Mayun 2025. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

'Farashin gas ya karu a Mayun 2025' - NBS

Rahoton da aka wallafa a shafin NBS na intanet, ya nuna cewa wannan karin farashin da aka samu a watan Mayu ya kai kashi 3.57 idan aka kwatanta da farashin a watan Afrilu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NBS ta ce farashin kilo 5 na gas din ya karu ya karu da kashi 10.10 a shekara, daga N7,418.45 a watan Mayun 2024 zuwa N8,167.43 a Mayun 2025.

Ana tattara bayanan farashin gas din girkin daga ƙananan hukumomi 774 na Najeriya da babban birnin tarayya (FCT), ta hanyar rahotannin fiye da mutane 10,000, inji NBS.

Kiyasin farashin da aka tattara yana nuna ainihin nauyin kashe-kuɗin da mutane suke yi a kan gas da kuma ainihin farashin da mutane ke sayan kilo daban-daban na gas din girki a faɗin ƙasar.

Jihohin da aka fi tsadar gas a Najeriya

A rahoton jihohi, NBS ta bayyana cewa jihar Abia ce ta fi sauran jihohi tsada, inda farashin kilo 5 na gas din ya kai N9,181.20, sai Ebonyi a kan N9,177.32 da kuma Rivers a kan N9,174.40.

Kara karanta wannan

"Ba a kama shugaban ADC yana cusa daloli a aljihu ba," Dalung ya wanke ƴan APC tas

A gefe guda, jihar Oyo ce ta fi arahar gas din girki, inda ake sayar da kilo 5 a kan N7,116.49, sai jihohin Niger da Plateau da suke sayar da shi a kan N7,142.07 da N7,177.10.

Nazarin yanki-yanki ya nuna cewa yankin Kudu-Maso-Kudu ne ya fi tsada, inda kilo 5 na gas din girkin ya kai N8,760.51, sai Kudu-Maso-Gabas da suke sayar da shi a kan N8,724.70.

“A Yankin Arewa ta Tsakiya kuwa, ana sayar da kilo 5 na gas din girki a kan N7,759.38, wanda ya nuna cewa ya fi Kudu araha” in ji NBS.
Har wa yau, NBS ta ce farashin kilo 12.5 na gas din girki ya karu da kashi 2.18 daga N20,268.06 a watan Afrilu zuwa N20,709.11 a Mayun 2025.
Rahoton farashin gas da NBS ta fitar na watan Mayu, ya nuna cewa Yobe ta fi arahar 12.5kg na gas din girki. Hoto: @NBS_Nigeria
Source: Twitter

Farashin kilo 12.5 na gas din ya karu a jihohi

Har wa yau, NBS ta ce farashin kilo 12.5 na gas din girki ya karu da kashi 2.18 daga N20,268.06 a watan Afrilu zuwa N20,709.11 a Mayun 2025.

Ta ƙara da cewa a shekara guda, farashin kilo 12.5 ya karu da kashi 32.52 daga N15,627.40 a watan Mayun 2024 zuwa N20,709.11 a Mayun 2025.

Nazarin jihohi ya nuna cewa jihar Delta ce ke da farashi mafi tsada, inda kilo 12.5 ya kai N23,356.46, sai Abia da ake sayar da shi kan N22,953.01 da kuma Ebonyi a kan N22,943.30.

Kara karanta wannan

'Na raina albashin': Hadimin Sanata ya yi murabus daga muƙaminsa bayan shekaru tare

A gefe guda, jihar Yobe ce ta fi arahar gas din mai nauyin kilo 12.5, inda ake sayar da shi a kan N18,500, sai Lagos da Kebbi da suka biyo baya da N18,536.00 da N18,606.60.

'Yan Najeriya sun yi martani kan karin kudin gas

A zantawar Legit Hausa da Hauwa'u Mohammed, mazauniyar Minna, jihar Neja ta ce ta sayi gas din girki kan N1300 a wani sabon gidan sayar da gas da aka bude a kusa da inda take.

Hauwa ta ce:

"Na je da bututun gas dina mai cin 12.5kg, amma da na ji karin kudin, sai dai na hakura na sayi 10kg, duk da cewa dama 12kg nake sanya mata.
"Amma da yake sabon wuri ne, wai Karamah Ventures, to suna sayar a 1kg a kan N1400, haka na sayi na N13,000. Amma fa, watanni biyu da suka wuce, 11kg a kan N11,300 na saye shi.
"Ka ga an samu karin kudin sosai. Ko shi kanshi buhun gawayi yanzu ya koma N10,000, a baya har N8,000 an sayar da shi. Ina ga suma suna la'akari da kudin gas din wajen kara masa kudi."

Kara karanta wannan

David Mark: Takaitaccen tarihin jagoran hadakar ADC da ya yi gwamna tun a 1984

Shi kuwa ma'aikacin Legit Hausa, Mallam Muhammad Malumfashi, ya ce ya yi mamaki da aka ce har 5kg na gas din girki ya kai N8,000.

A cewar Malam Malumfashi:

"Mu a nan 1kg N1100 yake, Allah kyauta."

An koma girki da gawayi saboda tsadar gas

A wani rahoton, mun ruwaito cewa, mazauna garin Makurdi sun bayyana damuwa kan hauhawar farashin gas din girki da ya addabi al’umma a kwanakin nan.

Rahotanni sun bayyana cewa sakamakon tsadar gas din, mutane da dama sun koma amfani da icce da gawayi domin dafa abinci.

Har wa yau, rahoton ya nuna cewa jama’a na fuskantar ƙarin kashe kuɗi wajen cika tukunyar gas dinsu, tare da ƙorafi kan tsadar man kananzir shi ma.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com