Majalisa Na Duba Buƙatun Ƙirƙirar Sababbin Jihohi 46 da Ƙananan Hukumomi 117
- Majalisar Wakilai na nazarin buƙatu 46 na sababbin jihohi da 117 na ƙananan hukumomi, da kuma 86 na gyaran tsarin mulki
- Arewa ta Tsakiya ce ke kan gaba wajen neman jihohi, yayin da Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu suka yi zarra a neman ƙananan hukumomi
- Shugaban kwamitin, Benjamin Kalu, ya buƙaci 'yan Najeriya su ba da gudunmawa don inganta tsarin mulki, yana mai jaddada muhimmancin hakan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Majalisar wakilai na duba buƙatu kusan 46 na ƙirƙirar sababbin jihohi da buƙatu 117 na ƙananan hukumomi a faɗin jihohin tarayya 36.
Majalisar na kuma duba buƙatu biyu na daidaita iyakokin jihohi da kuma kusan kudurori 86 na sauya kundin tsarin mulki da majalisar ta riga ta amince da su.

Source: Twitter
Bukatu 46 na kirkirar jihohi na gaban majalisa

Kara karanta wannan
Jama'atul Nasril Islam ta yi magana kan karuwar kashe kashe da farfadowar Boko Haram
Duk wadannan bukatu, suna karkashin kwamitin majalisar wakilan da ke duba sauye-sauyen kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, inji rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yankin Arewa ta Tsakiya ke kan gaba da buƙatu 12 na ƙirƙirar sababbin jihohi, sai Kudu maso Yamma da buƙatu takwas, Arewa maso Yamma da Kudu maso Kudu na da bakwai kowanne, sannan Arewa maso Gabas da Kudu maso Gabas na da buƙatu shida kowanne.
A ɓangaren ƙananan hukumomi, Arewa maso Gabas na da buƙatu 22, Arewa maso Yamma na da 14, Arewa ta Tsakiya na da 21, Kudu maso Gabas na da 24, Kudu maso Yamma na da 12, yayin da Kudu maso Kudu ke da buƙatu 24.
Shugaban kwamitin kuma mataimakin shugaban majalisar, Benjamin Kalu, ya ce ya raba dukkanin ƙudurori da buƙatun da aka shigar zuwa rukuni-rukuni domin sauƙaƙa fahimtarsu.
Wasu kudurori na sauya kundin mulkin Najeriya
Kalu ya bayyana cewa ƙudurorin da ake dubawa sun haɗa da: Sauye-sauyen tsarin zaɓe, gyaran bangaren shari’a da majalisa, mulkin haɗin gwiwa.
Sauran sun hada da inganta tsaro da kafa ‘yan sandan jihohi, rage ikon gwamnatin tarayya, ƙarfafa hukumomi, sarautun gargajiya da gyaran kasafin kuɗi.
Hakazalika akwai kudurori da suka shafi 'yan ƙasa, hakkokin dan Adam, gyaran ƙananan hukumomi da kuma ƙirƙirar sababin jihohi da ƙananan hukumomi.

Source: Twitter
Majalisa ta aika sako ga 'yan Najeriya
Benjamin Kalu ya bukaci ‘yan Najeriya da su ba da gudunmawarsu a aikin duba tsarin mulki domin ya dace da muradun jama'a, yana mai cewa waɗanda suka ki ba da gudunmawa yanzu, ba za su yi korafi daga baya ba.
Ya ce ci gaba da duba kundin tsarin mulki yana da matuƙar muhimmanci domin cigaban dimokuraɗiyyar ƙasa, saboda kusan koyaushe ana samun wuraren da ya kamata a gyara.
Kalu ya ce kwamitin majalisar ya himmatu wajen tabbatar da shigar duka ‘yan ƙasa da masu ruwa da tsaki wajen sauya tsarin mulki, a cewar rahoton Tribune.
Majalisa za ta ji ra'ayoyi kan kirkirar jihohi 31
Tun da fari, mun ruwaito cewa, majalisar Dattawa ta shirya gudanar da zaman sauraron ra’ayoyin jama’a kan ƙudurori 31 da suka shafi buƙatar ƙirƙirar sababbin jihohi.
Zaman zai kuma tattauna muhimman batutuwa kamar bayar da 'yancin kai ga ƙananan hukumomi, kafa 'yan sandan jihohi, da sauye-sauye a bangaren shari'a da tsarin mulki.
Kwamitin na neman ra’ayoyin al’umma domin inganta wakilcin mata a harkokin siyasa da kuma bada damar tsayawa takara ba sai da jam’iyya ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
