Gwamnan Benue Ya Fusata da Kisan Matafiya 'Yan Kano, Ya sha Alwashi
- Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Iormem Alia ya nuna takaicinsa kan kisan gollar da aka yiwa wasu matafiya ƴan asalin Kano a jiharsa
- Hyacinth Ali ya yi Allah wadai da kisan na mutane biyu wanda ya bayyana a matsayin rashin imanin da ba za a lamunta
- Gwamnan ya kuma miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga takwaransa na Kano, Abba Kabir Yusuf kan kisan mutanen da aka yi a daren ranar Litinin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Benue - Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya yi magana kan kisan da aka yi wa wasu ƴan asalin Kano a jiharsa.
Gwamna Hyacinth Alia ya yi Allah-wadai da kisan mutanen guda biyu da ake zargin wasu matasa ne suka kashe a ƙauyen Agan da ke Makurdi.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta ce hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan, Tersoo Kula, ya fitar.
An kashe ƴan Kano a jihar Benue
Wata majiya daga jami’an tsaro ta bayyana cewa mutanen biyu suna jigilar kaya ne zuwa gabashin ƙasar, lokacin da aka kai musu hari kuma aka kashe su da misalin ƙarfe 11:00 na dare a ranar Litinin.
An dai kashe su ne bayan da suka tsaya don siyan kati na waya.
"Sun tsaya a ƙauyen Agan don siyan kati na waya, sai wasu matasa suka kai musu hari suka kashe su."
- Wata majiya
Me Gwamna Alia ya ce kan kisan ƴan Kano
Gwamna Alia ya bayyana lamarin a matsayin ta’addanci da rashin imani wanda ba za a yarda da shi ba, tare da bayar da umarnin a gaggauta cafkewa da gurfanar da waɗanda suka aikata laifin.
"Ƴan sanda sun riga sun kama wasu mutum biyar da ake zargi a Makurdi bayan umarnin gwamnan."
- Tersoo Kula
Gwamna Alia ya nuna alhini kan faruwar lamarin, inda ya jaddada cewa mutanen Benue an sansu da zaman lafiya da kuma karɓar baƙi hannu bibbiyu, rahoton tashar Channels tv ta fitar ya tabbatar.

Source: Facebook
"Ba za mu lamunci ƴan ta’adda su lalata mana suna ba. Dole ne a gano su, a kamo su, sannan a hukunta su bisa doka."
- Tersoo Kula
Gwamnan ya kuma aika da saƙon ta’aziyya ga takwaransa na jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, tare da tabbatar wa al’ummar Kano cewa za a yi adalci.
Gwamnan Benue ya dakatar da hadiminsa
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya dakatar da ɗaya daga cikin hadimansa daga kan muƙaminsa.
Gwamna Alia ya dakatar da Mista Mkor Aondona daga muƙaninsa na mai ba shi shawara na musamman kan shirye-shirye, bincike da tsara tsare-tsare.
Dakatarwar da gwamnan ya yi ta biyo cafke Mkor Aondona da jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC suka yi masa bisa zargin tilastawa mata yin lalata da shi da barazanar yaɗa sirrinsu ta kafar intanet.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

