Dubu ta Cika: Jami'an DSS Sun Cafke Rikakkun 'Yan Bindiga bayan Dawowa daga Saudiyya
- Dubun wasu riƙaƙƙun ƴan bindiga ta cika bayan sun dawo daga aikin Hajji a ƙasa nai tsarki watau Saudiyya
- Jami'an tsaron DSS da wasu hukumomin tsaro ne suka ƙaddamar da wani samame a filin jirgin sama na Kaduna
- Samamen ya jawo cafke mutane shida da ake zargin ƴan bindiga ne ciki har da wasu mata gudu uku
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Wani babban samamen tsaro da aka gudanar a filin jirgin sama na ƙasa da Ƙasa da ke Kaduna ya haifar da kama mutane shida da ake zargi da zama ƴan bindiga.
Daga cikin mutanen da jami'an tsaron suka cafke har da mata uku, jim kaɗan bayan dawowarsu daga aikin Hajji a ƙasa mai tsarki watau Saudiyya.

Source: Twitter
Tashar AIT ta rahoto cewa wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatar mata da cafke riƙaƙƙun ƴan bindigan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami'an DSS sun cafke ƴan bindiga
Majiyar ta ce jami’an hukumar tsaro ta farin ƙaya (DSS) tare da haɗin gwiwar wasu hukumomin tsaro ne suka kai samamen da asuba ta ranar Talata, 24 ga watan Yunin 2025.
Jami'an tsaron sun cafke waɗanda ake zargin ne da misalin ƙarfe 3:40 na safe, a daidai lokacin da suka sauka daga jirgin da ke dawo da alhazan Najeriya daga Saudiyya.
Majiyar ta bayyana cewa rahotannin leƙen asiri sun danganta mutanen da aka kama da ayyukan ƴan bindiga a yankin Arewacin Najeriya.
Su wanene ƴan bindigan da aka cafke
Daga cikin waɗanda aka kama akwai, Hajara Halidu, daga ƙaramar hukumar Giwa, Haruna Aliyu, daga ƙaramar hukumar Giwa da Idris Suleiman, wanda ake zargin riƙaƙƙen ɗan bindiga ne.
Sauran sun haɗa da Hadiza Iliyasu, da aka bayyana a matsayin mahaifiyar marigayi Buharin Daji, sanannen shugaban ƴan bindiga, Safiya Iliyasu, tsohuwar matar Buharin Daji da Abdullahi Iliyasu, da ake zargin ɗan uwan Buharin Daji ne.
Dukkan waɗanda ake zargin an tafi da su nan take zuwa inda ake tsare da su domin ci gaba da bincike.

Source: Original
Wannan gagarumin samame ya zo ne bayan kama wani mutum da ake zargi da zama jagoran masu garkuwa da mutane, Sani Galadi, a filin jirgin sama na Sokoto a ranar 19 ga watan Mayu, a lokacin da yake ƙoƙarin tafiya aikin Hajji na shekarar 2025.
Masu sharhi kan harkokin tsaro sun bayyana cewa kama wadannan mutane na nuna irin yadda wasu miyagun mutane ke ƙoƙarin amfani da aikin Hajji a matsayin hanyar samun mafaka ko ɓoye ayyukansu.
DSS ta bayyana cewa ana ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala.
Ƴan sanda sun daƙile harin ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sandan jihar Katsina sun samu gagarumar nasara kan ƴan bindiga.
Ƴan sandan sun yi nasarar daƙile wani hari da ƴan bindiga ɗauke da makamai suka kai a ƙaramar hukumar Sabuwa.
Jami'an sun kuma yi nasarar ceto manoma shida da ƴan bindigan suka sace bayan sun farmake su a gona.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

