EFCC Ta Fadi Sunayen Jami'an NNPCL da Suka 'Sace' Kudin Matatun Mai bayan Kama Su

EFCC Ta Fadi Sunayen Jami'an NNPCL da Suka 'Sace' Kudin Matatun Mai bayan Kama Su

  • Hukumar EFCC ta kama tsohon jami’in kudi na kamfanin NNPCL bisa zargin hannu a badakalar dala biliyan 7.2 da ta shafi gyaran matatun mai
  • Rahotanni sun ce an cafke wasu tsofaffin shugabanni na matatun Warri da Fatakwal bisa zargin almubazzaranci, karɓar na goro da karkatar da kuɗi
  • Rahotanni sun bayyana cewa an dade ana jiran kammala aikin gyaran matatun, inda wasu daga ciki suka fara aiki, yayin da wasu ba su fara ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumar hana almundahana ta EFCC ta cafke tsohon shugaban sashen kudi na kamfanin NNPCL, Umar Isa.

Rahoto ya nuna cewa an kama shi ne bisa zarginsa da hannu a cikin badakalar dala biliyan 7.2 da ke da nasaba da aikin gyaran matatun Kaduna, Warri da Fatakwal.

Kara karanta wannan

An kashe Hausawa suna shirin tafiya daurin aure a Filato, sojoji sun kai dauki

EFCC ta kama jami'an NNPCL kan zargin sace kudin gyaran matatu
EFCC ta kama jami'an NNPCL kan zargin sace kudin gyaran matatu. Hoto: EFCC Nigeria
Source: Facebook

Majiyoyi daga hukumar EFCC sun bayyanawa The Cable cewa Umar Isa ne wanda ya jagoranci sakin kudi domin aikin gyaran matatun lokacin da yake ofis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A halin yanzu yana fuskantar bincike tare da wasu jami’an NNPCL da suka hada da shugabannin matatun mai daban-daban.

An zargi waɗannan jami’ai da aikata laifuffukan cin hanci, amfani da ofis ba bisa ka’ida ba, karkatar da kuɗi da kuma karɓar na goro daga hannun 'yan kwangila.

Jami'an NNPCL da hukumar EFCC ta kama

Binciken ya shafi tsohon babban daraktan matatar Warri, Jimoh Olasunkanmi, wanda ke tsare a hannun EFCC a halin yanzu, bisa zargin rawar da ya taka a cikin badakalar.

Business Day ta wallafa cewa sauran da ake gudanar da bincike a kansu sun hada da Tunde Bakare, wanda shi ne shugaban matatar Warri a yanzu.

Sauran sun hada da tsohon shugaban matatar Fatakwal Ahmed Adamu Dikko da Ibrahim Monday Onoja wanda shi ma ya taba shugabantar matatar Fatakwal.

Kara karanta wannan

2027: An fara ruguza hotunan Tinubu a Kano, 'yan sanda sun yi gargadi

Wani jami’i daga EFCC ya bayyana cewa:

“Bincike yana cigaba da zurfafa, kuma akwai yiwuwar kara kama wasu da ake zargin sun amfana daga wannan kudi na gyaran matatun.”

Matatun da EFCC ta kama mutane a kansu

A baya, an gano cewa kamfanin NNPCL na fama da jinkiri wajen kammala gyaran matatar Fatakwal, duk da cewa wasu sassa na tsohuwar matatar sun fara aiki a karshen 2024.

A ranar 26 ga Nuwamba, 2024, an fara tace danyen mai a tsohuwar matatar Fatakwal, wacce ke da ƙarfin tace ganga 60,000 a kullum.

Wata sanarwa daga NNPCL ta musanta cewa an sake rufe matatar, bayan wata guda da fara aiki, lamarin da ya jefa shakku a zukatan jama’a.

Halin da matatun Najeriya ke ciki

A ranar 19 ga Mayu, kungiyar masu gidajen sayar da man fetur (PETROAN) ta bukaci gwamnati ta gaggauta kammala aikin gyaran sabuwar matatar Fatakwal da kuma matatun Warri da Kaduna.

Kwana biyar bayan haka, kamfanin PHRC ya sanar da rufe matatar domin gudanar da aikin gyaran gaggawa, matakin da ya sake haifar da cece-kuce a Najeriya.

Kara karanta wannan

Lakurawa sun fara kafa sharudan noma, sun hana aiki da injuna a Kebbi

Ana cigaba da bincike kan gyaran matatun mai a Najeriya
Ana cigaba da bincike kan gyaran matatun mai a Najeriya. Hoto: Getty Images
Source: UGC

Kamfanin NNPCL ya kara kudin man fetur

A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin man Najeriya na NNPCL ya kara kudin man fetur a wasu sassa na kasar nan.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an kara kudin man fetur din ne kwanaki kadan bayan matatar Dangote ta yi karin kudi.

Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da fuskantar matsalolin game da man fetur sakamakon yakin da aka yi tsakanin Iran da Isra'ila.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng