Tsoro Ya Kare: 'Yan Banga 300 Sun Shiga Daji Sun Kashe 'Yan Bindiga 80
- Wasu 'yan bindiga da masu sa kai sun fafata a wani artabu da ya barke a dajin Dutsen Zaki da ke karamar hukumar Wase, Jihar Filato
- Rahotanni sun tabbatar da cewa sama da 'yan sa kai 16 sun jikkata yayin da su kuma suka hallaka 'yan bindiga sama da 80 yayin artabun
- Wannan rikici ya faru ne makonni biyu bayan jami'an tsaro da 'yan sa kai sun kashe 'yan bindiga biyar a kauyen Kadil Masudu na jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Filato - Mutane da dama sun rasa rayukansu a wani fada mai tsanani da ya barke tsakanin 'yan sa kai da 'yan bindiga a dajin Dutsen Zaki da ke cikin karamar hukumar Wase a jihar Filato.
Wani jagoran 'yan sa kai a yankin, Abdullahi Hussaini, ya bayyana cewa rikicin ya faro ne tun ranar Asabar, kuma ya ci gaba har zuwa ranar Laraba.

Source: Original
Rahoton Daily Trust ya ce fiye da 'yan sa kai 300 ne suka shiga dajin domin fatattakar 'yan bindigar, inda suka kashe akalla 80 daga cikinsu, ciki har da matansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kai farmaki maboyar 'yan bindiga a Filato
A cewar Abdullahi Hussaini, 'yan sa kai sun kai farmaki maboyar 'yan bindigar da ke cikin dajin Dutsen Zaki da ke kewaye da kauyukan Zurak, Aduwa, Kinashe da Odare a gundumar Bashar.
Ya ce:
“Mutane a yankin Bashar ba su da kwanciyar hankali saboda hare-haren da ke kara yawaita.
"Hakan ya sa muka yanke shawarar kai farmaki. An dade cikin damuwa kan wannan daji saboda sun dade suna fakewa a nan.”
Ya kara da cewa a baya sun gwabza da su amma ba su ci nasara ba, a wannan karon sun yi nasara ta hanyar kashe da dama daga cikin su, yayin da sauran suka tsere.
'Yan sa kai sun rasu yayin artabu da 'yan bindiga
Wani shugaban matasa a yankin, Shafi’i Sambo, ya tabbatar da faruwar al’amarin, yana mai cewa daga cikin ‘yan sa kai hudu da suka rasa rayukansu har da kwamandan su.
Ya ce an riga an nada sabon kwamanda domin ci gaba da gudanar da farmakin har sai sun kora dukkan 'yan bindigar daga yankin.
Rahotanni sun ce akalla 'yan sa kai 16 ne suka jikkata kuma ana basu kulawar gaggawa a cibiyoyin lafiya biyu daban-daban da ke Wase da Bauchi.

Source: Getty Images
Halin da ake ciki bayan kashe 'yan bindiga
Wani mazaunin yankin, Abdullahi Bin Umar, ya bayyana cewa mazauna kauyukan da ke zagaye da dajin sun fara barin gidajensu saboda fargabar abin da ka iya faruwa.
Ya ce:
“Mutane sun cika da tsoro saboda yawan 'yan bindigar da aka kashe da kuma yadda wasu suka gudu. Ba a san ko za su dawo su rama ba.”
A halin da ake ciki, kakakin rundunar Operation Safe Haven, Manjo Samson Zhakom, bai ce uffan ba kan wannan lamari har zuwa lokacin da aka kammala rahoton.
Sojoji sun kama makamai a jihar Filato
A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojin Najeriya sun kama wani waje da ake boye makamai da ake zargi 'yan ta'adda na amfani da su a jihar Filato.
Rahotanni sun nuna cewa mutanen da suke zaune a wajen sun tsere zuwa wani waje yayin da sojojin suka musu dirar mikiya.
Sai dai rahoton da rundunar soji ta fitar ya nuna cewa sun samu nasarar tattara makaman da aka ajiye a wajen da babur din 'yan ta'addan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


