Rikici Ya Tsananta: Tinubu Ya ba da Umarnin Kwashe Ƴan Najeriya daga Isra'ila da Iran

Rikici Ya Tsananta: Tinubu Ya ba da Umarnin Kwashe Ƴan Najeriya daga Isra'ila da Iran

  • Gwamnati za ta kwashe 'yan Najeriya daga Isra'ila da Iran, saboda tsanantar rikicin da ke faruwa, a cewar ma'aikatar harkokin waje
  • Ofisoshin jakadancin Najeriya a Tel Aviv (Isra'ila) da Tehran (Iran) na ci gaba da tuntuɓar 'yan ƙasa don tabbatar da dawowar su gida
  • Gwamnatin tarayya ta yi kira ga Isra'ila da Iran da su tsagaita wuta, tare da jaddada goyon bayanta ga warware rikicin ta hanyar sulhu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za ta kwashe 'yan Najeriya da suka makale a Isra'ila da Iran, sakamakon ƙaruwar rikicin da ke faruwa tsakanin ƙasashen biyu.

A daren ranar Talata, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin waje, Kimiebi Ebienfa, ya fitar da sanarwa da ta yi bayani kan shirye-shiryen da ake yi yanzu haka.

Kara karanta wannan

Gaza: Tankokin yakin Isra'ila sun bude wuta kan Falasdinawa, mutane da dama sun rasu

Gwamnatin tarayya za ta kwaso 'yan Najeriya daga Isra'ila da Iran saboda tsanantar rikici
Barin wuta tsakanin Iran da Isra'ila ya sa Tinubu ya ba da umarnin kwaso 'yan Najeriya. Hoto: Getty Images, @officialABAT/X
Source: UGC

Za a kwaso 'yan Najeriya daga Iran da Isra'ila

Kimiebi ya ce ofisoshin jakadancin Najeriya da ke Tel Aviv (Isra'ila) da Tehran (Iran) suna ci gaba da tuntuɓar 'yan Najeriya da abin ya shafa domin tabbatar da dawowar su gida lafiya, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An shawarci 'yan Najeriya da ke yankunan da abin ya shafa da su bi ƙa'idojin tsaro na gida sosai, kuma su tuntubi ofishin jakadancin Najeriya don yin rajista.

Ma'aikatar ta yaba da jajircewar jami'an diflomasiyya a ƙasashen biyu, kuma ta tabbatar wa jama'a aniyar gwamnati na kare lafiya da jin daɗin 'yan ƙasarta a waje.

Ta kuma yaba da irin haɗin gwiwar da take samu daga abokan hulɗarta na ƙasa da ƙasa da kuma hukumomin yankin don tabbatar da tsarin kwashe 'yan Najeriya cikin gaggawa.

Sakon gwamnati ga mazauna Iran da Isra'ila

Sanarwar ta ce:

"Biyo bayan ƙaruwar rikicin tsakanin Isra'ila da Iran, gwamnatin tarayya ta yanke shawarar kwashe 'yan Najeriya da suka makale a ƙasashen biyu cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

"Komai ya tsaya," Iran ta samu gagarumar nasara da ta harba rokoki kan matatar man Isra'ila

"Don haka ana ba duk 'yan Najeriya da abin ya shafa shawara mai ƙarfi da su bi ƙa'idojin tsaro da suka dace kuma su tuntubi ofishin jakadancin Najeriya ko wani ofishin jakadanci mafi kusa don yin rajista tare da jiran ƙarin umarni.
"Ma'aikatar ta yaba da ƙoƙarin da ofisoshin jakadancin mu na Tel Aviv, Isra'ila da Tehran, Iran suke yi wajen tuntuɓar al'ummar Najeriya a cikin wannan mawuyacin lokaci."
Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta yi kira ga Isra'ila da Iran da su tsagaita wuta, su sasanta kansu
Ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar
Source: Twitter

Najeriya na so Iran da Isra'ila su sulhunta kansu

Bugu da ƙari, gwamnatin tarayya ta sake yin kira ga Iran da Isra'ila da su tsagaita wuta tare da yin zama a kan teburin sasanci don kawo karshen rikicin.

Jaridar The Guardian ta rahtoo ma'aikatar wajen Najeriya ta sake jaddada aniyar kasar na ba da gudunmawa wajen warware rikicin Isra'ila da Iran ta hanyar lalama.

"Muna kira ga dukkan bangarorin da abin ya shafa da su rungumi tattaunawa, su mutunta dokokin jin kai na ƙasa da ƙasa, kuma su ba da fifiko ga kare fararen hula."

- A cewar sanarwar Kimiebi Ebienfa.

Za a samar da ƙarin bayani game da aikin kwaso 'yan Najeriya daga Isra'ila da Iran ta kafofin sadarwar gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da za su iya faruwa a yakin Isra'ila da Iran da yadda zai shafi duniya

China ta zargi Trump kan yakin Iran da Isra'ila

A wani labarin, mun ruwaito cewa, China ta zargi shugaban Amurka, Donald Trump, da "rura wutar" rikicin da ke tsakanin Iran da Isra'ila.

Wannan zargin ya biyo bayan gargadin da Trump ya yi wa mazauna Tehran da su kwashe kayansu su fice daga babban birnin nan take.

China ta kuma bukaci 'yan ƙasarta da su gaggauta barin Isra'ila yayin da ta ce rikicin yana haifar da lalacewar ababen more rayuwa da kuma ƙaruwar asarar rayuka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com