'Duk Musulmin da Bai Son Nasarar Iran kan Isra'ila Munafiki ne': Shehi Ya Yi Tankaɗe

'Duk Musulmin da Bai Son Nasarar Iran kan Isra'ila Munafiki ne': Shehi Ya Yi Tankaɗe

  • Musa Yusuf Assadus Sunnah ya goyi bayan Iran kan rikicin da ke tsakaninta da Isra'ila, yana mai cewa nasararta za ta taimaki Musulunci
  • Sheikh Assadus Sunnah ya ce duk Musulmin da ke fata Isra'ila ta doke Iran to akwai munafurci a zuciyarsa, yana kuma ganin hakan rashin kishi ne
  • Malamin ya bukaci Musulmai su tallafa da addu'a ko da ba da wani abu ba, yana mai jan hankalin su guji sabani saboda ra'ayi ko kungiyanci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah ya yi magana kan rigimar ƙasashen Isra'ila da Iran da ke faruwa a yanzu haka.

Sheikh Assadus Sunnah ya nuna damuwa kan yadda ake samun rarrabuwar kawuna game rikicin tsakanin Musulmi saboda sabani.

Sheikh ya fadi matsayarsa kan rikicin Iran da Isra'ila
Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah ya goyi bayan Iran. Hoto: Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah.
Source: Facebook

Matsayar Assadus Sunnah kan fadan Iran - Isra'ila

Kara karanta wannan

Macron: 'Amurka ta mika tayin tsagaita wuta ga kasashen Isra'ila da Iran'

Malamin ya yi magana ne a cikin wani faifan bidiyo da shafin Karatuttukan Malaman Musulunci ya wallafa Facebook a jiya Litinin 16 ga watan Yunin 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin faifan bidiyon, Assadus Sunnah ya nuna goyon bayansa ga kasar Iran madadin Isra'ila.

Malamin ya ce ya kamata kowane Musulmi ya yi fatan Iran ta samu nasara kan Isra'ila a halin da ake ciki.

A cewarsa:

"Waɗanda suke sauraronmu su sani ba mu rokon Allah ya nuna mana ranar da za a ce ga Isra'ila ta yi nasara kan Iran.
"Domin a samu wannan abin ya tabbata wani abin kasanci ne ga Musulunci da Musulmi.
"Amma a ce a wayi gari Iran ta yi nasara kan Isra'ila kasan wannan daukaka ce ga Musulunci."
Sheikh Assadus Sunnah ya soki masu goyon bayan Isra'ila
Sheikh Assadus Sunnah ya ce munafukai ne ba su son nasarar Iran kan Isra'ila. Hoto: Getty Images.
Source: Getty Images

Assadus Sunnah ya soki masu goyon bayan Isra'ila

Sheikh Assadus Sunnah ya ce duk wanda bai goyon bayan Iran ta yi nasara kan Isra'ila tabbas akwai munafurci a zuciyarsa.

"Shiyasa muke da 'maslaha' idan Allah ya taimaki Iran a kan Isra'ila ta rusa ta, amma ba Isra'ila ta yi nasara kan Iran ba.

Kara karanta wannan

Iran ta sake yin luguden wuta kan birnin Tel Aviv, Isra'ilawa 8 sun bakunci lahira

"Duk wanda aka wayi gari a zuciyarsa yana burin Allah ya sa Isra'ila ta murkushe Iran, na rantse da Allah munafiki ne.
"Saboda haka duk wanda bai son Iran da murkushe Isra'ila ba wallahi akwai munafurci a zuciyarsa."

- Cewar Sheikh Assadus Sunnah

Shawarar Sheikh Assadus Sunnah ga al'ummar Musulmi

Sheikh Assadus Sunnah ya bukaci kowane Musulmi ya ba da gudunmawa kan abin da ke faruwa a yankin.

Ya ce a matsayinka na Musulmi mafi karancin abin da za ka iya yi shi ne addu'a da kuma goyon baya domin samun nasarar Iran.

Sheikh ya fadi matsayarsa kan rikicin Iran da Isra'ila

Kun ji cewa fitaccen matashin malamin Musulunci, Sheikh Abdallah Mahmud Adam ya goyi bayan Iran kan Isra'ila a fadan da ake ci gaba da yi a yanzu haka.

Malamin ya ce abin takaici ne yadda ake kawo rarrabuwar kawuna tsakanin Musulmi saboda kungiyanci da akida da kuma mashabanci.

Sheikh Abdallah ya bayyana irin gatan da Iran ta yi wa Musulunci da kuma Musulmi a duniya baki daya musamman a wannan hali da ake ciki a yanzu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.