'Sun Canja Salo': EFCC Ta Bankado Yadda Manyan 'Yan Siyasa Ke Satar Kudin Jama'a
- EFCC ta bayyana cewa manyan 'yan siyasa na amfani da 'yan 'Yahoo-Yahoo' wajen safarar biliyoyin kuɗin sata zuwa ƙasashen waje
- Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya ce an gano yadda 'yan Yahoo ke bude asusun crypto tare da tura kuɗaɗen ciki don sayen kadarori
- Olukoyede ya kuma nuna damuwar cewa 'yan damfara sun koma fashi, garkuwa da mutane, da kisan kai don tsafi idan damfara ta gaza
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC) ta bayyana cewa wasu manyan 'yan siyasa a Najeriya sun canja salon karkatar da kudaden sata.
EFCC ta shaida cewa yanzu 'yan siyasar sun koma amfani da 'yan damfara na yanar gizo da ake kira 'yan Yahoo-Yahoo safarar kudaden da suka sata zuwa kasashen waje.

Source: UGC
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ne ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai a hedikwatar hukumar da ke Abuja a ranar Litinin, inji rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan siyasa sun canja salon satar kudin jama'a
Olukoyede, ya jaddada cewa hadin gwiwa tsakanin 'yan siyasa da 'yan damfara na nuna irin zurfin cin hanci da rashawa da ya mamaye tsarin mulki da shugabanci a kasar.
Ya bayyana cewa binciken EFCC ya gano yadda manyan 'yan siyasa ke hada kai da 'yan Yahoo wajen bude asusu na cryptocurrency domin tura kudin sata zuwa kasashen waje don sayen motoci da gidajen alfarma.
A cewarsa:
“Lokacin da suka sace biliyoyin Naira, sai su ba wadannan 'yan Yahoo kudin; su kuma su bude asusu na crypto, daga nan sai a tura kudin zuwa kasashen waje.
“Yawancin manyan 'yan siyasa na tuntubar wadannan matasan, suna kama masu daki a otel, sannan su bude musu asusun banki domin aikewa da kudin zuwa kasashen waje.”
Ƴan Yahoo sun koma fashi da garkuwa
Shugaban EFCC ya nuna damuwa kan yadda 'yan damfarar suka sauya daga damfarar yanar gizo, zuwa fashi da makami, garkuwa da mutane da ma kisan kai don tsafi.
Jaridar Daily Trust ta rahoto Ola Olukoyede yana cewa:
“Abin da ya fi hadari shi ne, ba wai Yahoo-Yahoo kadai suke yi ba; wasu daga cikinsu sun koma fashi, garkuwa da mutane. Idan sun gaza damfara, sai su koma wadannan munanan dabi’u.”
Olukoyede ya koka kan yadda wadannan ayyuka ke bata sunan Najeriya a duniya, inda ya bayyana cewa 'yan Najeriya na fuskantar tsangwama daga jami'an shige da fice idan suna tafiya kasashen waje.

Source: Facebook
EFCC ta cafke wanda ya yi safarar N5bn
A cewar shugaban hukumar ta EFCC:
“Idan kun je kasashen waje da fasfo din Najeriya, sai ku ga ana kallonku da wutsiyar ido tattare da alamar rashin yarda. Hakan abin kunya ne da wasu matasanmu suka jawo mana.”
Daga karshe, ya ce rashin yarda da yin aiki tukuru da sha’awar samun dukiya cikin gaggawa ne ke jefa matasa cikin wadannan mummunan halaye.
Ya bayyana cewa EFCC ta kama wani dan Yahoo 'dan shekara 22 da ya yi safarar fiye da Naira biliyan 5 a cikin wata 18, duk da cewa bai taba yin wani aiki na halal a baya ba.
'Masu daukar nauyin ta'addanci na amfani da crypto'
A wani labarin, mun ruwaito cewa, EFCC ta bayyana cewa ana amfani da wasu matasa a ke hada-hadar kuɗaɗen intanet (crypto) wajen ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci a Najeriya.
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana cewa 'yan ta'addan na amfani da manyan manhajoji irin su Binance wajen yin hada-hadar kuɗaɗen ayyukan ta’addanci.
Olukoyoyede ya jaddada cewa akwai buƙatar gaggawa ta yin amfani da fasaha mai zurfi wajen bin diddigin kuɗaɗen da ake amfani da su wajen aikata laifuffuka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


