Shugaba Tinubu da Wike Sun Kinkimo Gagarumin Aiki a INEC ana Shirin Zaben 2025

Shugaba Tinubu da Wike Sun Kinkimo Gagarumin Aiki a INEC ana Shirin Zaben 2025

  • Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na shirin kaddamar da fara aikin gina sabuwar hediwatar hukumar zaɓe ta kasa watau INEC a Abuja
  • Hukumar gudanarwa ta Abuja (FCTA) karkashin jagorancin Nyesom Wike ce ta shirya aikin domin bikin cikar Tinubu shekara biyu a kan mulki
  • Sai dai wannan lamari ya fara tayar da jijiyoyin wuya, inda ra'ayoyin lauyoyi ya banbanta kan wannan aiki na gina ofishin INEC

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ana sa ran Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai kaddamar da fara aikin gina sabuwar hedikwatar Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da ke Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa wannan aikin ya shiga jerin ayyukan da Hukumar Gudanarwa ta Abuja (FCTA) ta shirya domin cikar Tinubu shekaru biyu a kan mulki.

FCTA za ta gina babban ofishin INEC.
Shugaba Tinubu zai kaddamar da aikin gina sabuwar hedikwatar INEC a Abuja Hoto: @OfficialFCTA
Source: Twitter

Rahoton da Daily Trust ta tattaro ya bayyana cewa an shirya gudanar da bikin kaddamar da fara ginin sabuwar hedikwatar INEC a ranar Talata a unguwar Maitama.

Kara karanta wannan

Da gaske sojoji sun hamɓarar da shugaban ƙasa a Kamaru? Bincike ya bankaɗo gaskiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi daga Hukumar Raya Birnin Tarayya (FCDA) sun ce FCTA ce za ta aiwatar da aikin, wanda za a kashe biliyoyin naira akansa, ko da yake cikakken bayani game da aikin bai fito fili ba tukuna.

Dalilin da ya sa FCTA za ta gina hedikwatar INEC

Daya daga cikin manyan jami’an FCDA ya ce duk da INEC hukuma ce mai zaman kanta, FCTA na da alhakin gina da gyaran gine-ginen gwamnati da ke Abuja, ciki har da Fadar Shugaban Ƙasa da Majalisar Ƙasa.

“Amma saboda INEC hukuma ce mai matuƙar muhimmanci, mutane, musamman 'yan siyasa, za su iya fara sukar aikin, sai dai ban ga wata manufa mara kyau a ciki ba,” in ji majiyar.

Shin aikin yana cikin kasafin kuɗin 2025?

Wani darakta da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa duk da Majalisa ta amince da kasafin kuɗin Abuja, har yanzu mai girma shugaban ƙasa bai rattaɓa hannu ba.

Kara karanta wannan

"Arewa ta fi kowacce shiyya morewa," Dankabo ya fadi yadda ake amfana da Tinubu

Haka kuma, ya ce a halin yanzu babu cikakken bayani kan ko aikin gina hedikwatar INEC na cikin kasafin da kuma nawa aka ware wa aikin.

A baya-bayan nan, Ministan FCT, Nyesom Wike, ya sha suka kan gina masaukan alkalai a yankin Mabushi na Abuja, inda wasu suka ce yana neman saye bangaren shari'a, zargin da ya musanta.

Martanin Hadimin Wike

Lere Olayinka, mai taimaka wa Wike kan hulɗa da jama’a da kafofin sada zumunta, ya tabbatar cewa gina ofisoshin INEC aikin hukumar FCTA ne.

“Dukkanin gine-ginen gwamnati da ke birnin tarayya mallakin FCTA ne, ciki har da Majalisar Ƙasa,” in ji shi.

Game da adadin biliyoyin kuɗin da aikin gina sabuwar hedkwatar INEC zai laƙume, Olayinka ya ce a jira zuwa ranar bikin kaddamarwa.

Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Gina sabuwar hedikwatar INEC ta fara jan hankalin masana doka Hoto: Nyesom Wike
Source: Facebook

Ra’ayoyin lauyoyi sun bambanta

Wani lauya, Obioma Ezenwobodo ya ce duk da cewa INEC tana da 'yancin kanta a tsarin mulki, ta na ƙarƙashin bangaren zartaswa, don haka babu laifi idan an gina mata ofis.

Amma Hameed Ajibola Jimoh ya ce wannan aiki ba dole ba ne kuma salwantar da dukiyar al'umma ce a kan abin da bai zama tilas ba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tafka kuskure a jawabin ranar dimokuradiyya, gwamnati ta ba da hakuri

“Bana ganin akwai bukatar FCTA ta ɗauki nauyin gina ofishin INEC. Kodayake suna da ‘yancin kashe kuɗinsu yadda suka tsara, ya kamata su yi komai a kan gaskiya."

INEC ta sanya ranakun zaɓen Osun, Ekiti

A wani labarin, kun ji cewa hukumar INEC ta zaɓi ranakun da za a gudanar da zabukan gwamnoni a jihohin Ekiti da Osun.

INEC ta ce zaɓen gwamna a jihar Ekiti zai gudana ranar Asabar, 20 ga Yuli, 2026, yayin da na Osun zai gudana ranar Asabar, 8 ga Agusta, 2026.

Haka zalika hukumar ta kammala shirin gudanar da zaɓukan cike gurbi a majalisun dokokin ƙasa da na jihohi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262