Ana Zargin Wani Babban Ɗan Siyasar Najeriya Ya Ci Zarafin Ma'aikatan Jirgin Sama

Ana Zargin Wani Babban Ɗan Siyasar Najeriya Ya Ci Zarafin Ma'aikatan Jirgin Sama

  • Kamfanin Air Peace ya yi Allah-wadai da halin rashin da'a da tashin hankali da wani fitaccen ɗan siyasa ya nuna a filin jiragen Legas
  • Air Peace ya yi ikirarin cewa dan siyasar ya kawo cikas ga ayyukan filin jirgin da kuma cin zarafin ma'aikata bayan ya rasa dama shiga jirgi
  • Yayin da ya zayyana abubuwan da suka faru, kamfanin ya gargadi abokan huldarsa kan tayar da zaune tsaye kan abin da aka san doka ne

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kamfanin jirgin sama na Air Peace ya yi Allah-wadai da abin da ya kira "halin rashin da'a da tashin hankali" da wani "fitaccen dan siyasa a Najeriya" ya nuna.

Air Peace ya yi ikirarin cewa fitaccen dan siyasar ya kawo cikas ga ayyukan kamfanin a filin jirgin sama na Legas bayan jirgin da ya kamata ya shiga ya tashi.

Kara karanta wannan

Abin ya juya: An shiga firgici a Kano da ango ya hallaka amaryarsa da wuƙa

Kamfanin Air Peace ya zargi wani babban dan siyasa da kawo tsaiko da cin zarafin ma'aikatansa a Legas
Matafiya na hawa jirgin kamfanin Air Peace. Hoto: @flyairpeace
Source: UGC

'Dan siyasa ya rasa damar shiga jirgin sama

Air Peace ya bayyana abin da ya faru a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun hukumar gudanarwa da aka wallafa a shafinsa na X a safiyar Laraba.

Kamfanin jirgin ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:10 na safe a filin jiragen Murtala Muhammed, bangare na 1 (Zulu Hall) da ke Legas.

Sanarwar ta ce dan siyasar da ba a bayyana sunansa ba ya iso a makare don shiga jirgin Flight P47120, wanda aka shirya zai tashi zuwa Abuja da karfe 6:30 na safe.

Ta kara da cewa:

"Bisa ga tsauraran dokokin sufurin jiragen sama da kuma ka'idar kamfanin na tashi a kan lokaci, an rufe kofar shigar fasinjoji cikin jirgin kuma ya tashi kamar yadda aka tsara."

'Dan siyasa ya tayar da husuma a filin jirgi

Air Peace ya yi ikirarin cewa a lokacin da dan siyasar ya fahimci cewa ya rasa damar shiga jirgin, sai ya fara masifa, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba.

Kara karanta wannan

Bayan cacar baki, Elon Musk ya yi nadamar zafafa harshe ga Trump

Kamfanin ya kuma yi ikirarin cewa, dan siyasar ya fusata sosai, har ta kai, "ya na kai hari ga ma'aikatan jirgin sama tare da rufe babban kofar shiga tashar jirgin."

Sanarwar kamfanin jirgin saman ta kara da cewa:

"Bayan ya shiga tashar ta kafin tsiya, sai kuma ya hana sauran fasinjoji shiga, ya rufe kofa, wanda ya haifar da babban cikas ga ayyukan filin jirgin saman na yau da kullum."

Air Peace ya kara da cewa halin da babban dan siyasar ya nuna a gaban ma'aikata da fasinjoji ya haifar da jinkirin aiki da kuma matsaloli ga kamfanin.

Kamfanin Air Peace ya gargadi fasinjoji kan tayar da zaune tsaye don sun rasa jirgi bisa kuskurensu
Babban jirgin sama mallakin kamfanin jiragen Air Peace a Najeriya. Hoto: @flyairpeace
Source: Getty Images

Air Peace ya aika gargadi ga fasinjoji

Sanarwar ta kara da cewa:

"A matsayin martani, Air Peace ya dauki matakin gaggauta, inda ya canza wa fasinjoji hanya zuwa wata tashar daban don kwantar da tarzomar da kuma kiyaye jadawalin tafiye-tafiye.
"Mun yi matukar kaduwa da wannan halin tashin hankali da rashin bin ka'idojin jirgin sama da dan siyasar ya nuna.
Babu wani fasinja, komai matsayinsa ko mukaminsa, da ke da 'yancin kawo cikas ga ayyukan jirgi ko jefa lafiyar wasu cikin hadari."

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ci gyaran Tinubu, ya fadi hanyar da zai bi wajen cire tallafin man fetur

Kamfanin Air Peace ya sake nanata matsayarta na kin amincewa da tashin hankali, cin mutunci, ko kowane irin cin zarafi ga ma'aikatanta ko abokan huldarta.

Karanta sanarwar a kasa:

Jirgin Air Peace ya samu matsala a sama

A wani labarin, mun ruwaito cewa, kamfanin Air Peace ya sanar da cewa jirginsa da ke jigilar fasinjoji daga jihar Edo zuwa Abuja ya samu matsala yayin tafiya.

Mai magana da yawun kamfanin, Ejike Ndulue, ya tabbatar da cewa injiniyoyi na aiki tukuru don magance wannan matsalar.

Ejike Ndulue ya kuma nanata aniyar kamfanin na ci gaba da kiyaye ingantattun matakan tsaro don tabbatar da lafiyar matafiya a Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com