'Yan Bindiga Sun Ƙara Yi Wa 'Sojoji' Ɓarna bayan Sun Karɓi Naira Miliyan 10 a Kogi
- Tsohon Manjo a rundunar sojin Najeriya, Joe Ajayi ya mutu a hannun masu garkuwa da mutane bayan an biya kuɗin fansa Naira miliyan 10
- Tun farko ƴan bindiga sun yi garkuwa da Ajayi ne da suka kai farmaki gidansa a garin Odo-Ape, karamar hukumar Kabba-Bunu ta Jihar Kogi
- Majiyoyi sun ce tsohon Manjon ya shiga mawuyacin hali a hannun ƴan bindigar sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kogi - Wani tsohon jami’in sojin Najeriya, Manjo Joe Ajayi (Mai ritaya) ya mutu a hannun ƴan bindigar da suka yi garkuwa da shi a jihar Kogi.
Ƴan bindiga sun sace Ajayi ne a gidansa da ke garin Odo-Ape, karamar hukumar Kabba-Bunu ta Jihar Kogi.

Source: Original
Ƴan bindiga sun karɓi kuɗin fansa N10m

Kara karanta wannan
Guguwar Tinubu na kwasar 'yan adawa, karin Sanatoci, 'Yan majalisa 12 sun koma APC
Vanguard ta tattaro cewa tsohon Manjo a rundunar sojin Najeriya ya rasa rayuwarsu a hannun masu garkuwa da mutane duk da an biya Naira miliyan 10 don kuɓutar da shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An sace Manjo Ajayi ne da misalin karfe 11:30 na dare, ranar Laraba, 21 ga Mayu, 2025, lokacin masu garkuwan suka kai farmaki gidansa.
Majiyoyi sun ce masu garkuwan sun bukaci kudin fansa har Naira miliyan 50 a farko, sai dai rashin biyan waɗannan kudi ya jefa Ajayi cikin matsala saboda rashin lafiyar da yake fama da ita.
Me ya yi ajalin tsohon Manjo a Kogi?
Masu garkuwan sun sanar da iyalansa cewa za su karɓi karin kudi kafin su amince a kai masa magani, amma hakan ma bai yiwu ba saboda ƴan uwansa ba su da kuɗin.
A karshe, bayan sun fahimci cewa ba zai iya rayuwa ba, sai suka rage bukatar kudin fansa zuwa ₦10m, abin da iyalinsa suka gaggauta biya da fatan cewa yana raye.
Sai dai bayan biyan kudin, maimakon a tarar da shi a wurin da ƴan bindigar suka yi wa iyalansa kwatance, sai aka tarar da gawarsa.
A halin yanzun an kai gawar tsohon sojan ɗakin ajiyar gawarwaki na Asibitin Kabba a jihar Kogi.

Source: Twitter
Wane mataki ƴan sanda suka ɗauka?
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kogi ta tabbatar da rasuwar Manjo Joe Ajayi mai ritaya, a hannun masu garkuwa da shi duk da biyan kudin fansa N10m.
SP Williams Ovye-Aya, mai magana da yawun rundunar, ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a ranar Litinin a Lokoja, rahoton Punch.
Ya kuma ƙara da cewa rundunar ba za ta yi ƙasa a guiwa ba wajen ganowa da cafke waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki tare da gurfanar da su a kotu.
Ƴan bindiga sun kuma kai hari a Kogi
A wani labarin, kun ji cewa ƴan bindiga sun sake kai kazamin hari yankin ƙaramar hukumar Yagba ta Yamma a jihar Kogi.
Bayanai sun nuna cewa ƴan bindigan sun sace mutane huɗu a ranar Talata a garin Okoloke, da ke ƙaramar hukumar Yagba ta Yamma a jihar.
Rahotanni sun nuna cewa a safiyar ranar Laraba, mutane da dama sun fara barin garin sakamakon tsananin hare-haren da ake yawan kai musu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
