Zamfara: Bello Turji Ya Kawo Sabon Salo, Ya Gindaya Sharuɗan Yin Noma a Bana
- Hatsabibin dan bindiga, Bello Turji na bukatar N50m daga mazauna Tsallaken Gulbi da ke karamar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara
- Wadanda abin ya shafa sun hada da mutanen kauyen Fakai har zuwa Qaya da ke kusa da iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar
- An tabbatar da cewa Turji ya bukaci kudin ne domin ya bar su su ci gaba da noma a wannan kakar ba tare da sun samu matsala ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Rikakken dan ta'adda, Bello Turji ya sake dawowa inda yake addabar al'umma da ke Arewa maso Yamma a Najeriya.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa dan ta'addan ya dawo ne da wani irin salo wanda ya jefa mutane cikin tsoro.

Source: Original
Rahoton Bakatsine a shafin X ya ce Bello Turji ya bukaci makudan kudi na miliyoyi daga jama'a a jihar Zamfara a matsayin barinsu su yi noma.
Yadda Bello Turji ya addabi al'ummar yankin Arewa
Jihohin Arewa maso Yamma na fama da matsalolin tsaro musamman sanadin hare-hare daga yan bindiga da ke dauke da makamai.
Hatsabibin dan bindiga, Bello Turji na daga cikin manyan yan ta'adda da ke cin karensu babu babbaka a yankin da wasu yaransa.
Neman makudan kudi ko kuma kafa sharudan ga yan kauye domin fara noma ko biyan haraji ba sabon abu ba ne a Arewa maso Yamma.
Sojojin Najeriya na ci gaba da neman Bello Turji ruwa a jallo a kokarin kawo karshen ta'addanci da ya daidaita al'ummomi.
Duk da hatsabibancin Turji, ana ci gaba da samun galaba kansa musamman yadda ake hallaka yaransa ko wasu na hannun damansa.

Source: Twitter
Nasarar da Sojoji ke samu kan Bello Turji
Ko a kwanakin nan, sojoji sun yi nasarar kashe daya daga cikin manyan abokan kasurgumin ɗan ta’addan wanda ya rasa ransa a wani farmakin sojojin sama a jihar Sokoto.
Sojojin sama na Operation Fansan Yamma ne suka kai farmakin a maboyar 'yan ta’adda kusa da makarantar Tunfa a ƙaramar hukumar Isa, cewar Daily Post.
Rundunar soji ta ce dan ta'addan da aka kashe, Shaudo Alku na da alaƙar samar da makamai da shigo da kayan yaƙi daga Nijar zuwa Najeriya.
Yadda Turji ke cin karensa babu babbaka
An ce Turji ya bukaci N50m daga mazauna Tsallaken Gulbi a kauyen Fakai da ke karamar hukumar Shinkafi a Zamfara.
Wannan bukata ta shafi mazauna yankin daga Fakai har zuwa Qaya, kusa da iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar, domin su samu damar yin noma.
Cewar wata majiya:
"Ya ce sai an biya N50m kafin mu fara noma, Idan ba haka ba, za mu fuskanci matsala a gonaki.”
Yadda 'yan bindiga ke addabar mutanen Arewa
A Arewa maso Yammacin Najeriya, musamman a jihohin Zamfara, Katsina, Sokoto da Kebbi, matsalar yan bindiga ta zama tamkar ruwan dare.
Daya daga cikin munanan hanyoyin da ‘yan ta’addan ke amfani da su wajen cin zarafin al’umma shi ne kakabawa manoma da mazauna kauyuka haraji ko kudin kariya kafin su sami damar yin noma ko zaman lafiya a gidajensu.
A wasu lokuta, wadannan kudade da ake kira “harajin noma” na kai miliyoyin naira, kuma idan ba a biya ba, ‘yan bindigar na kai farmaki, su sace mutane ko su kona gonaki.
Wannan hali ya jefa dubban manoma cikin tsoro da fargaba, inda da yawa daga cikinsu ke barin gonakinsu ko su koma birane don tsira da rayuka.
Hakan ya janyo babban koma baya a harkar noma da samar da abinci, wanda ke barazana ga tattalin arzikin yankin da ma kasa baki daya.
Babu wani tsari na hukuma da ke tabbatar da tsaron da zai ba wa manoma damar aiki cikin kwanciyar hankali.
Duk da kokarin sojoji da jami’an tsaro, har yanzu ‘yan bindiga irin su Bello Turji na cin karensu babu babbaka, suna kakabawa jama’a haraji cikin karfin hali da rashin tausayi.
Yaran Turji sun yi barazanar korar al'ummar Sokoto
A wani labarin mai kama da wannan, wasu yaran Bello Turji sun ba wa mazauna kauyuka wa’adin ficewa daga garuruwansu ko kuma su fuskanci hare-hare.
Barazanar da sababbin hare-haren da Turji da yaransa ke kai wa mazauna kauyukan Zamfara da Sokoto ya jefa jama'a a mawuyacin hali.
Mazauna Bafarawa da wasu kauyuka sun tsere sakamakon barazanar da ‘yan bindiga ke yi, lamarin da ke kara tayar da hankali.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


