Ana Shirin Sake Hana Muhammadu Sanusi II Hawan Sallah, Kwankwaso Ya Dura Kano
- Tsohon ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya isa jihar Kano domin sallar idin layya a gida
- Jagoran NNPP na kasa kuma tsohon gwamnan Kano ya koma gida ne a ranar Laraba, 4 ga watan Yuni, 2025, kwanaki biyu kafin babbar sallah
- Wannan dai na zuwa ne yayin da ake ta surutu kan batun hawan Sallah da Muhammadu Sanusi II ke shirin yi amma ƴan sanda sun hana
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Jagoran jam'iyyar NNPP na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso ya isa birnin Kano domin yin shagulgulan babbar sallah a gida.
Dr. Rabiu Kwankwaso, tsohon ɗan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar NNPP ya shiga Kano ne a jiya Laraba, 4 ga watan Yuni, 2024.

Source: Twitter
Mai taimaka wa Kwankwaso a kafofin sadarwa, Saifullahi Hasssan ne ya tabbatar da hakan a wani gajeren sako da ya wallafa a shafinsa na X.
Alhaji Saifullahi ya ce Madugun Kwankwasiyya ya dawo Kano ne domin ya yi sallar idin layya a gida kamar yadda ya saba.
Yadda aka hana hawan sallah a Kano
Wannan dai na zuwa ne yayin da aka fara ka-ce-na-ce kan batun hawan sallah da mai martaba sarki na 16, Muhammadu Sanusi II yake shirin yi.
Masarautar Kano ta fitar da sanarwar kan batun hawan sallah, inda ta gayyaci hakimai da sarakuna domin fara shirye-shiryen wannan al'ada.
Sanarwar da Damakwayon Kano ya fitar ta bukaci hakimai da su hallara da dawakansu ranar Laraba a cikin birnin Kano kafin babbar sallah.
Jim kaɗan bayan haka ne rundunar ƴan sandan Kano ta sake jaddada cewa haramcin hawan sallah da ta sanya tun karamar sallah yana nan daram.
Rundunar ta bayyana cewa bayan samun sahihan bayanan leƙen asiri da kuma nazarin tsaro na baya-bayan nan, ta gano cewa akwai barazanar tsaro a Kano.

Kara karanta wannan
Bola Tinubu ya karɓi bakuncin fitaccen malami, Tunde Bakare, an ji abin da suka tattauna

Source: Facebook
Rabiu Kwankwaso ya koma gida a Kano
Ana cikin wannan taƙaddama ne, jagoran NNPP na kasa kuma tsohon gwamnan kano, wanda ake kyautata zaton zai halarci hawan sallah idan za a yi, ya koma Kano.
Hadimin tsohon gwamnan, Saifullahi Hassan ya ce:
"Jagoran jam’iyyar NNPP, Mai Girma Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, PhD, FNSE, ya isa garin Kano a ranar 4 ga Yuni, 2025, domin shirye-shiryen bikin Eid al-Adha (Babbar Sallah).
"Allah Ya kai mu, ya sanya mu yi idi lafiya, cikin salama da albarka. Ameen.
Sallah: Gwamnatin Abba ta gargaɗi musulmi
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Kano ta gargaɗi musulmi da su yi taka tsan-tsan kana su tabbatar da lafiyar dabbobin da za su yi ibadar layya da su.
Kwamishinan Lafiya, Abubakar Labaran ya ce hakan zai taimaka wajen kare lafiyar jama’a da kuma dakile yaduwar cututtukan da mutane ke iya ɗauka daga dabbobi.
Ya tabbatar da cewa gwamnatin Kano na da isassun magunguna da kayan agaji a cibiyoyin lafiya domin ba da kulawa cikin gaggawa idan an samu matsala.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
