Jiran Shekara 3: Za a Fara Hukunta Daliban Najeriya da aka Kama da Satar Amsa
- Gwamnatin tarayya ta umurci hukumomin jarrabawa da su dauki mataki kan cibiyoyin da ake zargi da taimaka wa dalibai wajen satar amsa
- JAMB ta bayyana cewa za a dakatar da daliban da aka kama da laifin satar amsa na tsawon shekaru uku daga rubuta wata jarrabawar gama sakandare
- Sabon tsarin zai hada da hukunta cibiyoyin jarrabawa na CBT da makarantun sakandare da suka saba doka, kuma a bayyanawa duniya sunayensu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta dauki sabon mataki mai tsauri a yunkurinta na yaki da satar amsa.
Rahotanni sun nuna cewa matakan za su shafi dukkan harkokin ilimi musamman a fannin shirya jarrabawa ga daliban makarantu.

Source: Twitter
Jaridar Leadership ta ce a ranar Talata hukumar JAMB ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana cewa ministan ilimi, Dr Tunji Alausa ne ya tabbatar da hakan.
Dr Tunji Alausa ya umurci a rufe duk wasu cibiyoyi da aka gano suna taimakawa dalibai wajen satar amsa a Najeriya.
An dade ana zargin wasu makarantun sakandare da cibiyoyin CBT da shirya jarrabawa ta hanya mara kyau, wanda hakan ke haifar da gurbacewar tsarin ilimi a ƙasar nan.
Za a hukunta cibiyoyin da ake satar amsa
Jami'in hulɗa da jama’a na JAMB, Fabian Benjamin, ya bayyana cewa za a kwace lasisin gudanar da jarrabawa ga cibiyoyin da aka kama da taimakon satar amsa na tsawon shekaru.
Ya ce wannan hukunci zai shafi dukkanin hukumomin shirya jarrabawa irinsu WAEC, NECO da NABTEB, domin tabbatar da cewa babu wata cibiya da za ta tsira daga hukunci.
Jaridar the Cable ta wallafa cewa sanarwar ta ce:
“Hukuncin zai zama gargadi mai zafi ga masu gudanar da dukkan cibiyoyin satar amsa a Najeriya,”
Za a hukunta dalibai masu satar amsa
JAMB ta kara da cewa duk wani ɗalibi da aka kama da satar amsa za a hana shi shiga kowace irin jarrabawa ta ƙasa na tsawon shekaru uku.
Sanarwar ta bayyana cewa za a yi amfani da lambar shaidar zama dan kasa (NIN) wajen gano daliban da suka aikata laifin, domin dakile yunkurin canza suna ko karya doka.
Hukumar ta ce wannan mataki na kunshe ne a cikin Sashe na 16(2) na Dokar Satar Amsa, wanda ke baiwa hukumomin damar samun bayanai game da masu laifi.

Source: Twitter
JAMB ta yi kira ga iyaye da wakilan dalibai
JAMB ta jaddada cewa wannan sabon tsari zai fara aiki nan take, tare da bukatar iyaye da dalibai su dauki matakin da muhimmanci.
Hukumar ta ce manufar wannan tsarin ita ce dawo da mutuncin jarrabawa a matakin sakandare da kuma tabbatar da adalci a tsarin ilimi a Najeriya.
Majalisa ta yi magana kan faduwa a JAMB
A wani rahoton, kun ji cewa majalisar tarayya ta yi magana kan faduwar da aka samu sosai a jarrabawar JAMB ta bana.
Majalisar ta yi magana ne bayan hukumar JAMB ta tabbatar da cewa an samu tangarda wajen rubuta jarrabawar.
Bayan gano kuskuren da aka samu, Legit ta rahoto cewa JAMB ta bayyana wasu jihohi da za a sake rubuta jarrabawar a Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

