Satar amsa da kin karatu ya sa an kashe intanet a gaba dayan kasa guda har sai dalibai sun gama jarrabawa
- Aljazair ta kashe intanet baki dayan kasar ta har sai baba ta gani
- Kasar na uskantar masifaffiyar satar jarrabawa
- Rashin karatu ma wani dalili ne saboda chatting ya shiga jikin matasan
A arewacin Afirka, kasar larabawa mai makwabtaka da Nijar, watau Aljaza'ir, ta kashe hanyoyin kafafen sadarwar kasar baki dayanta na lokacin wucin gadi, dalilinsu, shine samari da 'yan mata sunki karatu sai chatting da aikin facebook.
Jarrabawar gama sakandare ce tazomusu, kuma an kula duk da basu yi karatu ba samarin kan makale su saci amsa ta hanyar wayarsu domin su haye.
Gwamnati ta ce hakan zata daina faruwa, muddin aka dakile hanyoyin satar amsa na zamani da yaran kasar suka naqalta kamar ja'irai.
DUBA WANNAN: An tafka asara a kasuwar hada-hadar hannayen jari
Ko a kasar nan ma, sadarwar intanet, tana baiwa dalibai damar su yi karatu, ko kuma su yi satar amsa kai-tsaye lokacin da suke zana tasu jarrabawar, bayan sun biya kudi.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng