Zulum Ya Fadi Matsayar Gwamnati a kan Boko Haram, ISWAP bayan Ganawa da Tinubu
- Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum ya ziyarci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yayin da matsalar tsaro ke kara kamari a jiharsa
- Ya bayyanawa manema labarai bayan taron cewa ya shaidawa shugaban kasar irin matsalar da suka fuskanta, musamman ta rashin tsaro
- Babagana Zulum ya bayyana matsayar da suka cimma da gwamnatin tarayya, yayin da ake sa ran raguwar harin 'yan ta'adda a Arewa maso Gabas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa ba zai taɓa bari 'yan ta'adda da masu tayar da ƙayar baya su mamaye kowace ƙaramar hukuma a jiharsa ba.
Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan wata ganawa da suka yi da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, inda suka tattauna kan ƙalubalen tsaro.

Kara karanta wannan
"Tinubu ya dage sai an magance matsalar tsaro a 2025," Badaru ya faɗi halin da ake ciki

Source: Facebook
Jaridar This Day ta ruwaito cewa Gwamna Zulum ya shaida wa shugaban ƙasa halin da yankin Arewa maso Gabas, musamman jihar Borno ke ciki dangane da matsalolin tsaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan Borno ya gana da Bola Tinubu
Channels Television ta ruwaito cewa Zulum da Shugaba Tinubu sun tattauna yadda gwamnatin tarayya da ta jiha za su haɗa kai domin shawo kan matsalar tsaro da ke addabar yankin.
Zulum ya ce:
"Na zo ne musamman domin na ba shi bayani kan halin da ake ciki a Arewa maso Gabas, musamman jihar Borno. Wannan ne babban dalilin da ya sa na zo. Domin kun ji yadda abubuwa ke ƙara tsananta a wasu sassan Arewacin Najeriya, musamman Arewa maso Gabas.
"Na kwashe kusan sati guda ina zagayen wasu ƙananan hukumomin da lamarin ya shafa. Muna ƙoƙarin ganin yadda za mu rage hare-haren da ake kai wa sansanonin soja da sauran wurare.
"Saboda haka, na zo na ba shugaban ƙasa bayani kan yadda gwamnati ta jiha da ta tarayya za su iya aiki tare domin rage matsalolin da muke fuskanta."
Za a hada gwiwa domin kawo tsaro a Borno
Gwamna Zulum ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu ya tabbatar masa da cewa gwamnati za ta ɗauki matakan da suka wuce waɗanda aka riga aka ɗauka tun da fari kan rashin tsaro.

Source: Facebook
Ya ce:
"A gaskiya mun roƙi gwamnatin tarayya da ta ɗauki mataki, kuma ina ganin cikin 'yan kwanakin nan rundunar sojojin Najeriya ta ɗauki wasu muhimman matakai da za su rage barazanar ta'addanci.
"Ina da tabbacin cewa gwamnatin tarayya na aiki a kan wannan tsari. Amma dai Shugaban Ƙasa ya tabbatar min da cewa za su yi duk abin da ya kamata domin shawo kan lamarin, kuma na yi imani cewa za a ɗauki mataki."
'Har da yan siyasa cikin Boko Haram,' Zulum
A baya, mun ruwaito cewa gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce wasu 'yan siyasa da jami'an rundunar soji na bai wa 'yan ta'addan Boko Haram bayanan sirri don kai hari.
Zulum ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a ranar Laraba, 21 ga watan Mayu, 2025, inda ya ce taimakon da 'yan ta'addan ke samu ya kara karfafa ayyukan Boko Haram.
Gwamnan ya ce akwai 'yan leƙen asiri a cikin sojoji, 'yan siyasa da wasu daga cikin al'umma waɗanda ke taimaka wa 'yan ta'adda da bayanan sirri a sassa daban daban dake jihar.
Asali: Legit.ng

