Fada Ya Barke tsakanin Maharba da Fulani Makiyaya a Taraba, Lamarin Ya Munana

Fada Ya Barke tsakanin Maharba da Fulani Makiyaya a Taraba, Lamarin Ya Munana

  • Rikici ya barke tsakanin maharba da makiyaya a Angwan Kuwait, Bali, jihar Taraba, sakamakon gardama kan dibar ruwan rijiya
  • An ce makiyaya sun doki wata mata da ta hana su ruwa, inda ta kai kara wajen maharba, lamarin da ya haddasa jikkata mutane tara
  • Rahoto ya nuna cewa an garzaya da makiyaya tara zuwa asibiti yayin da 'yan sanda suka kama mataimakin shugaban maharban garin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Taraba - Akalla Fulani makiyaya tara sun samu raunuka iri daban-daban bayan rikici mai muni da ya barke tsakaninsu da kungiyar maharba a karamar hukumar Bali, jihar Taraba.

Rahoto ya nuna cewa rikicin ya faru da yammacin ranar Juma’a, 24 ga Mayu, a unguwar Angwan Kuwait, kusa da garin Bali, bayan husuma kan amfani da ruwan da dabbobi za su sha.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Matasa sun gamu da ajalinsu a wajen karbo bashi a Kano

Fada ya barke tsakanin makiyaya da maharba a Taraba, mutane 9 sun jikkata
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, IDP Kayode Egbetokun. Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Fada ya barke tsakanin makiyyaa da maharba

Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa rikicin ya fara ne bayan wasu makiyaya sun yi yunkurin dibar ruwa daga rijiyar garin, amma wata mata mai suna Nater Ayinaorga ta hana su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya una cewa makiyayan sun ce sun bukaci ruwa ne don su shayar da dabbobinsu, amma suka fahimci cewar matar ba za ta kyale su ba.

An ce hakan ne ya sa makiyayan suka lakadawa matar duka, inda ta garzaya ta kai kara wajen kungiyar maharba ta garin Bali.

Da maharban suka je su cafke makiyayan da ake zargi da cin zarafin matar, sai fada ya barke, inda aka yi amfani da adduna har wasu makiyaya tara suka ji munanan raunuka.

Wadanda suka jikkata sun hada da Adamu Kantu, Haruna Kantu, Abdul Kantu, Sani Kantu, Jibrin Kantu, Umar Kantu, Saidu Kantu, da Amadu Kantu.

Kara karanta wannan

An fara raba tallafin gwamnatin Tinubu, mutane miliyan 15 za su ci gajiyar shirin

'Yan sanda sun dauki mataki kan maharba

An bayyana cewa an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibitin Alura da asibitin gwamnati na Bali don ceto rayukansu.

Majiyoyin tsaro sun tabbatar da faruwar lamarin, inda aka sanar da hukumomi wanda ya kai ga rundunar 'yan sanda ta fara bincike kan rikicin.

Rundunar ta kama mataimakin shugaban kungiyar maharba ta Bali, Mista Aloysius Vaakaa, domin amsa tambayoyi, yayin da ake ci gaba da neman sauran maharban da ake zargi da hannu a lamarin.

Hotunan da mai sharhi kan lamuran tsaron ya samu sun nuna yadda wadanda suka jikkata ke da raunukan yankan adda a kai, hannu da bayansu, wanda ya nuna tsananin tashin hankalin da ya auku.

Ana so a yi sulhu tsakanin makiyaya da maharba bayan fada ya barke tsakaninsu a Taraba
Taswirar Najeriya da ke nuna jihar Taraba da ke Arewa maso Gabashin kasar. Hoto: Legit.ng
Source: Original

An nemi a yi sulhu tsakanin maharba da makiyaya

Majiyoyin tsaro sun ce yankin yanzu yana cikin kwanciyar hankali, sai dai halin tsaron na iya sauyawa a kowane lokaci, amma sojoji na cikin shiri domin hana karin tashin hankali.

An bukaci shugabannin al’umma da masu ruwa da tsaki su shiga tsakani domin tabbatar da adalci da kuma sasanta rikicin da ba a san makararsa ba.

Kara karanta wannan

A ƙarshe, an gano Hamdiyya a Zamfara, an faɗi halin da take ciki

An ce yin adalci da sasanci ne kawai zai sa a kauce wa sake barkewar rikicin, musamman ganin irin zaman dar-dar da ke yankin sakamakon rikicin manoma da makiyaya.

'Ana yi wa Fulani rashin adalci' - Abubakar

A zantawarmu da wani Abubakar Ahmed Tashi daga Karim Lamido da ke jihar Taraba, ya ce tsarin shugabanci na Najeriya ya mayar da Fulani makiyaya saniyar ware.

Abubakar Tashi ya ce:

"Idan an kai mana hari, muka rasa jama'armu, ba a saurarenmu. Babu mai taya mu kuka, babu mai shiga kafafen yada labarai ya yi Allah wadai.
"Amma idan muka mayar da martani, ko da ba da tashin hankali ba, ko ta hanyar kare kai ko yin zanga-zangar lumana, sai a far mana da suka da munanan kalamai."

Abubakar ya ce Fulani ba sa adawa da zaman lafiya, amma zaman lafiya ba tare da adalci ba, tamkar zalunci ne a wajensu.

Ya kara da cewa:

"Muna rokon duniya da ta saurare mu. Kada a yanke mana hukunci bisa kanun labarai da ba su bayyana cikakken labari ba. Kada a siffanta mu da laifin wasu 'yan kalilan. Ku zo, ku gan mu, ku yi magana da mu, ku karanci halaye da dabi'unmu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba za ta magance matsalar ruwa, an fitar da biliyoyi domin noman rani

"Muna son ilimi. Muna bukatar a rika ba mu dama. Muna neman zaman lafiya. Kuma muna bukatar adalci."

Fada ya barke tsakanin makiyaya da manoma

A wani labarin, mun ruwaito cewa, rikici ya kunno kai a karamar hukumar Nangere da ke jihar Yobe bayan wani makiyayi ya sanya dabbobinsa sun lalata amfanin wata gona.

Lamarin ya yi muni har ya kai ga harbin Babayo Maina da kibiya a goshinsa, yayin da aka kashe Usman Mohammed, dan shekara 35 daga kauyen Chikuriwa.

Jami’an tsaro sun kwato dabbobi da suka hada da shanu, awaki da raguna, tare da kira ga shugabannin manoma da makiyaya domin warware rikicin lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com