Sojoji Sun Kutsa Maboyar 'Yan Ta'adda cikin Dazuka, an Kashe Miyagu

Sojoji Sun Kutsa Maboyar 'Yan Ta'adda cikin Dazuka, an Kashe Miyagu

  • Dakarun sojojin Najeriya sun ƙara azama a yunƙurin da suke yi na kakaɓe ƴan ta'adda masu tayar da ƙayar baya a jihohin Sokoto da Zamfara
  • Sojojin sun kutsa cikin dazuka idan suka yi artabu da ƴan ta'adda a sassa daban-daban na jihohin na yankin Arewa maso Yamma na Najeriya
  • Jami'an tsaron sun samu nasarar a sansanonin ƴan ta'adda masu yawa tare da hallaka wasu daga cikinsu a farmakin da suka kai

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Dakarun sojoji na rundunar Operation Fansan Yamma, sun kutsa cikin daji zuwa mafakar ƴan ta'adda a jihohin Zamfara da Sokoto.

Dakarun sojojin sun samu nasarar lalata sansanonin ta’addanci da dama tare da ƙwato makamai a sassa daban-daban na jihohin guda biyu.

Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda
Sojoji sun farmaki 'yan ta'adda a Zamfara, Sokoto Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun sake farmakar sansanin sojiji, an yi barna

Sojoji sun kai hare-hare a cikin dazuka

Dakarun sojoji sun kutsa wurare masu hatsari da suka haɗa da Gidan Madi, ƙauyen Tsamiya, Tudun Ruwa, Alela, da wasu dazuka da aka fi sani da zama mafakar ƙungiyoyin ƴan ta’adda.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa dakarun sun fuskanci harin kwantan ɓauna da dama daga mayaƙan ƙungiyar ƴan ta’adda ta Lakurawa.

Duk da ƙoƙarin hana su shiga, dakarun sun ci gaba da kai farmaki, inda suka share wuraren ɓoyo na ƴan ta’adda da ke bayan ƙauyen Alela, ciki har da yankin Areo, Damoria, Tumuna, da dajin Goboro.

“Waɗannan wurare an daɗe ana amfani da su a matsayin wuraren ajiya da shirya kai kai hari kan ƙauyuka da kuma rundunonin tsaro."

- Wata majiyar sojoji

Sai dai, dakarun sojoji sun samu asara a yayin harin. Wani soja ya jikkata a lokacin artabun, yayin da wani ɗan sa-kai da ke taimakawa a aikin ya rasa ransa.

Kara karanta wannan

Duk da ɓatan dabo da Turji ya yi, hadiminsa ya sauya salon hare hare a Sokoto

An gaggauta kai sojan da aka jikkata zuwa asibitin sojoji na runduna ta 8 da ke jihar Sokoto domin samun cikakkiyar kulawa.

Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda
Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda a Sokoto, Zamfara Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Dakarun sojoji sun kashe ƴan ta'adda

Dakarun sun kuma kashe ƴan ta’adda guda shida da ke da alaƙa da ƙungiyar Lakurawa yayin farmakin.

Hakazalika wasu da dama sun tsere cikin dazuka tare da raunukan harbin bindiga iri-iri.

Daga cikin makaman da aka ƙwato daga sansanonin da aka rusa sun haɗa da bindigogi daban-daban, gidan harsashi, rediyo guda biyu da babura, waɗanda ake zargin ana amfani da su wajen aikata ta'addanci.

Ƴan ta'addan ISWAP sun farmaki sojoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan ta'addan ƙungiyar ISWAP sun kai harin ta'addanci a wani sansanin sojojin Najeriya da ke jihar Borno.

Ƴan ta'addan sun kai farmakin ne a sansanin sojojin wands yake a ƙaramar hukumar Kala Balge ta jihar Borno.

Miyagun ƴan ta'addan sun hallaka aƙalla sojojin Najeriya guda biyar yayin da wasu kuma suka samu munanan raunuka a yayin harin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng