Jirgi Ya Sauke wa Ƴan Bindiga Makamai da Abinci a Kwara? Ƴan Sanda Sun Yi Bayani

Jirgi Ya Sauke wa Ƴan Bindiga Makamai da Abinci a Kwara? Ƴan Sanda Sun Yi Bayani

  • Rundunar ƴan sanda ta karyata cewa jirginta mai saukar ungulu ya kai wa ƴan bindiga abinci ko makamai a Kogi, bidiyon da ya yadu ba gaskiya ba ne
  • Adejobi ya bayyana cewa jirgin na ƴan sanda ne kuma yana aikin tsaro na halal a yankin Obajana, tare da haɗin gwiwar ƴan banga da maharba
  • Rundunar ta yi Allah wadai da yaɗa labaran ƙarya, tana mai gargadin cewa hakan na iya lalata amincewar jama'a ga jami'an tsaro da sadaukarwarsu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Rundunar ƴan sanda ta karyata rahoton da ke yawo cewa wani jirgi mai saukar ungulu ya sauke wa ƴan bindiga abinci ko makamai a jihar Kogi.

Wani bidiyo da ya yadu a intanet da ke nuna wani farin jirgin ƴan sanda yana sauka da kuma tashi a cikin daji, kewaye da 'yan bindiga, ya haifar da ce-ce-ku-ce.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun magantu kan bidiyon jirgi da ake zargi ya saukewa yan bindiga makamai

Rundunar 'yan sanda ta karyata cewa jirginta ya kai wa 'yan bindiga makamai a Kwara, ta ce aiki ta yi
Shugaban 'yan sandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun. Hoto: @Princemoye1
Source: Twitter

'Yan sanda sun magantu kan jirgin da aka gani

Bidiyon, tare da cewar makamai yake sauke wa, ya tayar da hankalin jama'a game da yiwuwar haɗin baki tsakanin jami'an tsaro da ƴan ta'adda, inji rahoton The Cable.

Sai dai, a cikin wata sanarwa da kakakin 'yan sanda, ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar a ranar Talata, 13 ga Mayu, 2025, rundunar ta warware rudanin da aka samu.

CP Olumuyiwa ya shaida cewa cewa an ga jirgin saman yana sauka da tashi ne a wani ɓangare na wani aikin tsaro da aka gudanar a ranar Asabar, a yankin Obajana na jihar Kogi.

Kakakin 'yan sandan ya ce:

"Jirgin da aka gani a bidiyo na daga cikin wani bangare na aikin tsaro da aka gudanar a hukumace, sabanin labarin yaudara da ƙarya da ke nuna cewa an yi amfani da jirgin wajen kai kayan abinci ga ƴan fashi"

Dalilin ganin jirgin 'yan sanda a dajin Kwara

Kara karanta wannan

'Ba a saba gani ba': Ɗan shekara 18 ya dirka wa 'yan mata 10 ciki a wata 5

An ce aikin haɗin gwiwar jami'an tsaro ne, da ya kunshi ƴan sanda, ƴan banga da maharba, da nufin yaƙi da fashi da makami, garkuwa da mutane, da sauran laifuffuka a yankin.

Rundunar ta ce an tura jirgin 'yan sanda, mai lamba 412EP (5N-GEJ), don samar da karin sa ido daga sama da kuma tallafa wa jami'an tsaron a lokacin atisayen.

Adejobi ya yi Allah wadai da yadda aka rika yada rahotanni karya kan lamarin, yana mai gargadin cewa irin wannan yaɗa ƙarya na iya lalata amincewar jama'a ga hukumomin tsaro.

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta sake jaddada ƙudurinta na kare rayuka da dukiyoyi, tare da alƙawarin ci gaba da haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki don inganta tsaron jama'a.

Rundunar 'yan sanda ta sha alwashin ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya
Shugaban 'yan sandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun. Hoto: @Princemoye1
Source: Twitter

An taba samun makamancin haka a 2021

Wannan lamari ba shi ne karo na farko da bidiyoyi da suka yadu suka haifar da cece-kuce game da zargin haɗin baki tsakanin jami'an tsaro da ƴan fashi ba.

Ko a shekarar 2021, an ga wani bidiyo makamancin wannan, wanda aka yi zargin cewa jirgin sama mai saukar angulu ya kai wa ƴan fashi kayan abinci da makamai.

Kara karanta wannan

"So suke a yafe masu zunubai," Jigon PDP ya tona asirin wasu gwamnoni da jiga jigai

Sai dai, shi ma rundunar ta fito ta karyata rahoton, inda ta ce bidiyon jirgin ya fito ne daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, kuma jirgin ba shi da alaƙa da Najeriya, inji rahoton Premium Times.

Boko Haram ta koma kai hari da jirgi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Hon. Ahmed Jaha ya bayyana cewa Boko Haram na amfani da jirage marasa matuƙi don kai hare-hare a Borno.

Ya kuma bayyana cewa an kashe manoma goma a mazabarsa, kuma Boko Haram na ƙara samun ƙarfi a Borno fiye da yadda suke a baya.

A nasa ɓangaren, Hon. Yusuf Gagdi ya yi iƙirarin cewa 'yan ta'adda sun ƙwace tankokin soji guda 40, wanda ya ce lamari ne da ke buƙatar agaji daga Shugaba Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com