Kano: Iyalan Ganduje Sun Nuna Goyon Baya ga Sanusi II bayan Nada Sabon Dagaci

Kano: Iyalan Ganduje Sun Nuna Goyon Baya ga Sanusi II bayan Nada Sabon Dagaci

  • Mai martaba Sarki Muhammad Sanusi II, ya naɗa Alhaji Jamilu Sani Umar, ɗan uwan tsohon gwamnan Kano, a matsayin sabon Dagacin Ganduje
  • Nadin ya zo bayan mayar da Sanusi II kan kujerar sarauta, abin da ke nuna sauyin salo a siyasar Kano, inda aka ce iyalan Ganduje sun nuna goyon baya
  • Masu sharhi na ganin naɗin wani mataki ne da zai iya daidaita yanayin siyasa da ake ciki a Kano, musamman tsakanin Abdullahi Ganduje da Sanusi II

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - A wani lamari da ya girgiza saraura da siyasar Kano, Khalifa Muhammad Sanusi II ya naɗa Alhaji Jamilu Sani Umar a matsayin sabon Dagacin Ganduje.

Rahotanni sun nuna cewa nadin ya gudana ne a fadar mai martaba Sanusi II, ranar Talata, 13 ga watan Mayu, 2025.

Kara karanta wannan

Bayan dawowar Sanusi II daga Tunisia, Aminu Ado Bayero ya dura a Lagos

Sanusi II
Sarautar Kano: Sanusi II ya nada sabon dagaci a Ganduje
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan yadda aka yi nadin sarautar ne a wani sako da fadar mai martaba Sanusi II ta wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin lura, Alhaji Jamilu ɗan uwan tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ne, wanda masarautar Kano karkashin Sanusi II ta tuɓewa rawani a baya.

Rahoton Kano Focus ya bayyana cewa 'yan uwan Ganduje sun amince da wannan nadin, inda wasu suka halarci taron naɗin kai tsaye, abin da ke nuna goyon baya ga bangaren Sanusi II.

Iyalan Ganduje sun amince da sabon dagaci

Bayan da aka mayar da Sanusi II kan kujerarsa, al’amuran siyasa da na sarautar gargajiya suka fara sauyawa a Kano.

A cikin haka ne aka samu wani rahoto da ke nuna cewa Ganduje ya nuna goyon baya ga naɗin ɗan uwansa da Sanusi II ya yi.

Wani na kusa da iyalan Ganduje ya shaida cewa tsohon gwamnan ya shirya taro da manyan dangi inda ya bukaci su goyi bayan sabon dagacin.

Kara karanta wannan

"So ya zama ajali": Matashi ya 'mutu' a gidan budurwarsa daga zuwa taɗi a Kano

Wannan na nuni da sauyin ra’ayi daga tsohon gwamnan wanda a baya ya taka rawa wajen tube Sanusi II.

Masana na ganin sauyin siyasa a Kano

Masana siyasa sun bayyana cewa wannan naɗin ya nuna cewa akwai ƙoƙarin daidaita yanayin siyasar jihar Kano

Ana ganin goyon bayan da iyalan Ganduje suka nuna yana da ma’ana ta siyasa da harkokin sarautar gargajiya.

Hakan na iya zama wata dabara domin tsamo kai daga rikicin baya da kuma samun sabuwar mafita a tsakaninsu da masarautar Kano bayan mayar da Sanusi II.

Sanusi II
Iayalan Ganduje sun nuna goyon baya ga nadin da Sanusi II ya yi. Hoto: Masarautar Kano
Source: Twitter

Alamu sun nuna cewa nadin zai iya cusa sabon dangantaka da za ta iya tasiri a gaba, musamman a siyasa da sarauta.

Tsakanin Ganduje da Sarki Sanusi II

Tun daga lokacin da Abdullahi Ganduje ya zama gwamnan Kano, dangantakarsa da Mai martaba Sarki Muhammad Sanusi II ta kasance mai cike da abin ban takaici.

Ganduje an ce ya taka rawa wajen kawo karshen mulkin Sanusi II a matsayin sarkin Kano, inda aka kori Sanusi daga kan kujerarsa a watan Maris 2020 bisa wasu dalilai na siyasa da na masarauta.

Kara karanta wannan

Duk da ɓatan dabo da Turji ya yi, hadiminsa ya sauya salon hare hare a Sokoto

Rikicin ya ta’azzara tsakanin Ganduje da Sanusi II, inda aka samu fuskantar juna tsakanin gwamna da sarki, har ya kai ga wasu manyan batutuwa na siyasa da na masarauta suka rikice.

A wannan lokaci, iyalan Ganduje sun kasance masu nuna rashin amincewa da Sanusi II, wanda hakan ya janyo cikas ga zaman lafiya da hadin kai a jihar.

Sai dai, bayan dawo da Sanusi II kan sarautarsa a watan Mayu 2025, an fara ganin wasu alamu na sassauci da canji a tsakanin bangarorin biyu.

Wannan sabon nadin Alhaji Jamilu Sani Umar, dan uwan Ganduje, a matsayin Dagaci daga Sanusi II, na nuna wani yunkuri na daidaita al’amura da kuma kyautata dangantakar siyasa da sarautar gargajiya a Kano.

Masana na ganin wannan mataki zai iya kawo zaman lafiya da hadin kai tsakanin tsohon gwamnan da sarkin Kano.

Sarki Sanusi II ya je taro a kasar Tunusia

A wani rahoton, kun ji cewa mai martaba Muhammadu Sanusi ya je kasar Tunusia wani taron tattalin arziki.

Manyan mutane daga Najeriya da suka hada da gwamnan Bauchi Sanata Bala Mohammed sun halarci taron.

Sarkin ya tattauna da masu zuba jari daga kasashen duniya domin duba yadda zai jawo hankalinsu zuwa jihar Kano.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng