'Da Yamma Suka Tare Mu,' Yan Daba Sun Dawo Kwace Ido na Ganin Ido a Kano
Rahotannin ayyukan 'yan daba, wadanda suka hada da kwacen waya da babura, har da kisan kai na neman ya zama ruwan dare a wasu sassan jihar Kano.
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – A ranar Lahadi, 11 ga watan Afrilu, 2025, wasu gungun yan daba suka fito 'aiki' a Kofar Nasarawa gabanin sallar magrib.
Wadanda lamarin ya rutsa da su sun bayyanawa Legit yadda mamaki da fargaba ya kama su, ganin cewa ido na ganin ido aka fito gudanar da mummunan aikin da zai iya jawo rasa rai.

Source: Facebook
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da masu kwacen waya suka kashe wasu matasa har biyu kwanaki kadan da suka gaba, kamar yadda Aliyu Samba ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda yan daba suka kare mazauna Kano
Fatima Koguna ta shaida wa Legit cewa ta sha da kyar a hannun masu kwace yayin da ta ke wucewa kusa da Kofar Nassarawa jim kadan bayan ta tashi daga aiki a ranar Lahadi.
Ta ce:
“Muna sauka daga wannan wannan gadar ta titin gidan gwamnati, kafin mu karasa Kofar Nassarawa, kawa sai na ga yan daba ta ko ina, sun fito wasu da kananan wukake suna bi mota mota suna karbar waya da abin da ya samu."
Fatima ta ce lamarin na faruwa a kusa da ofishin yan sandan da ke Gidan Murtala, amma hakan bai hana masu laifi shigowa cikin cunkosun motoci ba.
'Yan daba sun kwace baburin bakano
Mustapha Muhammad Kankarofi kuwa ya tabbatarwa Legit cewa shi da kansa ya ga yadda wani mutum ya rasa babur dinsa.
Ya ce:
“Wani matashi na tsaye yana kokarin hawa babur dinsa, kawai wasu suka zo suka kwace masa shi. Ya rude, ya kasa yin komai, ni ma dake gefe ina wucewa rudewa na yi, na shiga fargaba sosai."
Kankarofi ya kara da cewa har yan daban suka wuce da baburin, ba a samu wanda ya kawo dauki ba, sai dai an ci sa'a wannan karon, ba su burmawa matashin wuka ba.
Yan daba sun kashe mazauna Kano 2
Wani dan jarida, kuma hadimi a ofishin Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Aliyu Samba, ya wallafa wani rubutu mai tayar da hankali a shafinsa na Facebook inda ya bayyana cewa:
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Jiya aka kawo wani tsohon dalibina, yaron kirki mai suna Ilyasu, cikin jini da rauni mai tsanani a cikin adaidaita sahu. Yara masu kwace ne suka tare shi a hanya suka yanke shi a wuya da agararsa. Safiyar nan na samu labarin an yi jana’izarsa.”
Aliyu ya kara da cewa wannan ba shi ne karon farko ba, domin wasu ‘yan kwanaki da suka wuce, kanin abokinsa mai suna Yasir, shi ma ya rasa ransa a wannan hanyar.
Wurin da ake samun wadannan hare-hare, a cewarsa, yana tsakanin Gidan Mai Tangaran da gidan A.A Mudallabi, har zuwa makabartar Sallari, hanyar da ta dade tana zama barazana ga masu wucewa da daddare.
Mazauna Kano sun roki jami'an tsaro
Mutanen sun bayyana fargabar cewa yan daba suna kara karfi, duk da cewa suna jin labarin gwamnati ta na daukar matakan dakile ayyukan yan daba.
Aliyu Samba ya ce:
“Ina kira da girmamawa ga hukumomin tsaro su kafa ofishin ‘yan sanda, NSCDC ko Bijilanti a hanyar, ko da na wucin gadi ne. Kuma a kara yawan sintiri da daddare.”
Matakin da 'yan sandan Kano ke dauka
A baya, an sha jin kakakin rundunar yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya na bayyana irin kokarin da suke yi domin dakile ayyukan bata garin matasa.

Source: Facebook
Sai dai rundunar ta na zargin cewa rashin ishashshen hadin kai, musamman daga iyayen matasan da ake gani suna kwace babbar barazana ce ga tabbatar da tsaron rayuka.
SP Kiyawa ya nanata bukatar jama'ar gari su rika bayar da bayanan sirri, tare da fito da masu laifi a maimakon ba su kariya.
Kano: An hallaka hatsabibin 'dan daba

Kara karanta wannan
An kama masu garkuwa kan sace yar shekara 1, aka wurga ta rijiya a Kano, Abba ya magantu
A baya, mun wallafa cewa jami’an ‘yan sanda a Kano sun kashe wani fitaccen ɗan daba da ake zargi da aikata fashi da makami, wanda aka fi sani da Baba Beru bayan an sha artabu.
Rahotanni sun tabbatar da cewa hatsabibin ɗan daban ya rasa ransa ne a daidai lokacin da ya yi yunƙurin kai hari kan jami’an tsaro a unguwar Gwammaja da ke cikin birnin Kano.
Wannan lamari ya ja hankalin jama’a, inda aka ruwaito cewa Baba Beru ya fito da wuka yana kokarin kai farmaki ga jami’an da ke bakin aiki, wanda hakan ya tilasta masu kare kansu.
Asali: Legit.ng


