Siyasar Najeriya: Kwankwaso Ya Hadu da Shugaban Gwamnonin Arewa a Kano

Siyasar Najeriya: Kwankwaso Ya Hadu da Shugaban Gwamnonin Arewa a Kano

  • Rahotanni sun nuna cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamna Inuwa Yahaya sun gana a filin jirgin sama a Kano
  • Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe shi ne shugaban kungiyar gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya
  • Haduwar jagororin ta ya janyo abin magana kafafen sada zumunta, wasu na ganin hanya ce kawai ta hada shugabannin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Tsohon gwamnan Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya gana da gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya.

Rahotanni sun bayyana cewa sun hadu ne a safiyar Litinin a filin jirgin saman Malam Aminu Kano da ke Kano.

KWankwaso
Kwankwaso hadu da gwamna Inuwa Yahaya. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Haduwar Rabiu Kwankwaso da Gwamna Inuwa

Hadimin Kwankwaso ya wallafa a X cewa ganawar ta faru ne a wajen masaukin manyan baki, inda aka ga shugabannin biyu na musabaha da gaisuwa cikin nitsuwa.

Kara karanta wannan

Kolmani: Gwamnatin Tinubu za ta cigaba da aikin hako man fetur a Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Inuwa Yahaya, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin Arewa, ya kasance a cikin sahun shugabannin da ke da tasiri a yankin.

Kwankwaso kuwa na ci gaba da taka rawa a siyasar Najeriya, musamman a Arewacin ƙasar, inda ya ke jagorantar jam’iyyar NNPP.

Ganawar ta haifar da abin magana a kafafen sada zumunta, inda masu sharhi ke bayyana ra’ayoyinsu kan abin da ganawar ke iya nufi a siyasar kasa da yankin Arewa.

An ce hanya ce ta hada Inuwa da Kwankwaso

Yayin da wasu ke ganin ganawar wani yunkuri ne na sabuwar fahimta tsakanin shugabannin biyu, wasu kuwa na kallon hakan a matsayin haduwar da ta faru ba zato ba tsammani.

Wasu da suka yi sharhi a karkashin rubutun hadimin Kwankwaso sun ce, “Hanya ce kawai mai sa zumuntar dole,” kamar yadda Hausawa ke cewa idan mutane sun hadu ba tare da shiri ba.

Kara karanta wannan

Duk da ɓatan dabo da Turji ya yi, hadiminsa ya sauya salon hare hare a Sokoto

A wani bangare kuwa, ana ci gaba da tunanin ko ganawar na iya haifar da wani sabon salo a siyasar Arewa, duba da matsayin shugabannin biyu a harkar siyasa.

Kwankwaso ya je Kano domin halartar bikin yaye daliban jami'ar Aliko Dangote a Wudil, a nan kuma aka karamma shi da digirin Dakta.

Kwankwaso ya kai ziyarar duba aiki a Kano

Kafin haduwa a filin jirgin, hadimin Kwankwaso ya bayyana cewa jagoran NNPP ya kai ziyarar gani da ido a wurin da ake kera kayan dakin karatu a Kano.

An bayyana cewa kayan da ake kera wa na cikin shirye-shiryen gwamnatin jihar Kano ne na inganta yanayin ilimi, musamman a makarantun gwamnati.

Kwankwas
Kwankwaso yayin ziyarar duba aiki a Kano. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Wannan ya nuna irin yadda Kwankwaso ke ci gaba da goyon bayan gwamnatocin da ke bin sahun manufofinsa.

A yanzu dai, jama’a na ci gaba da saka idanu kan alaka tsakanin Kwankwaso da Gwamna Inuwa, ganin yadda siyasar Najeriya ke da cike da sauye-sauye tun kafin 2027.

Kwankwaso ya yi magana kan sauya sheka

A wani rahoton, kun ji cewa Madugun Kwankwasiyya ya ce butulci ne a zabi mutum a wata jam'iyya amma daga baya ya sauya sheka.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa sun yi magana da murya 1 kan rashin tsaro bayan taro a Kaduna

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana ne bayan wasu 'yan majalisa a jihar Kano sun sauya sheka daga NNPP zuwa APC.

Bayanin da Kwankwaso ya yi wata alama ce da ke nuna rashin tabbas kan rade radin da aka yi na cewa zai koma APC mai mulki a Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng