Ana Jimamin Kisan Kyaftin Ɗin Soja, Ƴan Bindiga Sun Hallaka Sufetan Ɗan Sanda
- Wasu da ake zargin makiyaya ne sun kashe wani jami’in ‘yan sanda da wani mutum a kauyen Ikyac-Gev da ke Makurdi, jihar Benue
- Jami’in, Igba Terwase, yana dawowa daga jinya ne lokacin da aka kai masa hari, an ajiye gawarsa da wani mutumin da ba a san shi ba
- Rundunar ‘yan sanda ta tura 'Operation Zenda' wurin, inda aka cafke wani yaro dan shekara 12 da ake zargin yana tare da maharan
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Makurdi, Benue - Wani abin bakin ciki ya faru a jihar Benue bayan yan bindiga sun kuma kai mummunan hari.
Yayin harin, yan bindiga sun hallaka wani babban jami'in ɗan sanda da ke dawowa cikin gari daga jinya a kauyensu.

Source: Facebook
Yan bindiga sun kashe babban ɗan sanda
Rahoton Zagazola Makama ya ce maharan sun kashe jami’in ‘yan sanda mai mukamin 'Inspector' da wani farar hula.
Lamarin ya faru ne a kauyen Ikyac-Gev da ke yankin 'North Bank' a Makurdi, babban birnin jihar Benue.
Rundunar yan sanda ta tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata 7 ga watan Mayun 2025.
Wata majiya ta shaida cewa lamarin ya afku lokacin da Igba Terwase Timothy ke dawowa gari daga jinya a kauyensu.
Majiyar ta ce kaninsa, Igba Aondogu ne ya kai rahoton kisan ga ‘yan sanda a ofishinsu na ‘C’ Division.

Source: Original
Benue: Matakin da yan sanda suka ɗauka
Hakan ya sa aka hanzarta aika jami’ai zuwa wurin da lamarin ya faru, an gano gawarsa da wata guda da ba a san ko ta wanene ba.
A martaninsa, Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Benue ya umarci tura jami’an 'Operation Zenda' zuwa yankin.
Jami’an sun bi sawun maharan zuwa wani dajin da ake zargin mafakar makiyaya ce.
Da suka hango jami’an na karatowa, wasu da ke dauke da bindiga sun bude musu wuta daga nesa, amma an yi artabu mai karfi har suka tsere.
Sun bar wani yaro dan shekara 12 mai suna Dahiru Eti da ake zargin yana daga cikinsu.
Yan sanda sun cafke matashi a Benue
Wani jami’in ‘yan sanda ya ce an kama yaron, kuma yana hannunsu yanzu yana taimaka wa wajen bin sawun wadanda suka tsere daga wurin harin.
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Benue ta ce za ta tabbatar da kamo wadanda suka aikata kisan, tare da tabbatar wa da jama’a kariya ta tsaro.
Borno: Boko Haram sun kashe babban soja
Kun ji cewa wasu majiyoyi sun ce al'umma sun shiga jimami a jihar Borno sakamakon wani sabon harin ta'addanci da ƴan ta'addan Boko Haram suka kai.
Ƴan ta'addan ƙungiyar Boko Haram sun farmaki wani ƙauye dake ƙaramar hukumar Gwoza a daren ranar Laraba 7 ga watan Mayun 2025.
An ce harin da ƴan ta'addan suka kai ya jawo asarar rayukan jami'an tsaro, yayin da dakarun sojoji suka kashe wasu daga cikin masu tayar da ƙayar baya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

