Mutane Za Su More, Gwamnatin Tinubu Ta Ware Sama da N750bn na Wasu Muhimman Ayyuka
- Gwamnatin tarayya ta ware sama da Naira biliyan 750 domin gudanar da wasu ayyuka da suka ƙunshi gina tituna, kiwon lafiya, makamashi da ruwa
- Majalisar Zartarwa ta Tarayya watau FEC ce ta amince da ware kuɗin a taron da ya gudana karƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ranar Litinin
- Daga cikin ayyukan da za a yi da kuɗin harda sake gina titin Sakkwato-Zamfara-Katsina-Kaduna wanda aka fara a kan kudi Naira biliyan 105
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da wasu sababbin ayyuka da gyaran hanyoyi a jihohi da za su laƙume kudi fiye da Naira biliyan 750.
Ministan Ayyuka, Dave Umahi, ne ya bayyana hakan a Fadar Shugaban Ƙasa bayan taron FEC da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta a ranar Litinin.

Source: Facebook
Umahi ya ce majalisar ta amince da sake nazari kan wasu manyan ayyuka da gwamnatin Tinubu ta gada domin duba yiwuwar ƙarasa su, Daily Trust ta rahoto.
Yadda Gwamnatin Tinubu za ta kashe N750bn
Muhimman ayyukan da gwamnatin Tinubu ta amince a aiwatar sun haɗa da sake tsara titin Akure-Eta-Ogbese-Ekiti zuwa Ikere-Ado-Ekiti wanda ya ratsa jihohin Ondo da Ekiti.
Wannan titin dai ya kai tsawon kilomita 18.4 amma yanzu za a rage shi ya dawo kilomita 15, da kuɗi Naira biliyan 19.4.
Haka zalika, gwamnati za ta ci gaba da aikin hanyar Sokoto-Zamfara-Katsina-Kaduna da aka fara kan kimanin Naira biliyan 105.
Duk da cewa an fara aikin na tsawon kilomita 375, yanzu an daidaita aikin zuwa kilomita 82.4 da gada shida, ba tare da ƙarin kuɗi ba.
A jihar Borno kuwa, gwamnatin tarayya ya amince da aikin titin Maiduguri-Monguno da aka fara a 2018 mai tsawon kilomita 105, wanda aka raba shi zuwa matakai biyu.
Mataki na farko, an amince da aikin gina titi mai tsawon kilomita 30 kan kuɗi Naira biliyan 21, yayin da za a gabatar da na biyu bayan an kammala na farko.
A jihar Gombe, gwamnati ta ware Naira biliyan 9.25 domin aikin sashen Cham-Numan na titin Gombe-Yola da ke Adamawa, kamar yadda Channels tv ta kawo.
Gwamnatin Tinubu za ta gina FMC a Makurɗi
A ɓangaren kiwon lafiya. Ministan Lafiya, Farfesa Ali Pate, ya bayyana cewa FEC ta tattauna batutuwa guda biyu masu muhimmanci ga bangaren lafiya.
"Na farko shi ne karɓar rahoton kwamitin majalisa kan yaki da barkewar cutar amai da gudawa a 2023.
"Na biyu kuma shi ne amincewa da gina sabon asibitin tarayya (F. M. C), Makurdi, a sabon wuri da ke Apir, a jihar Benuwai," in ji shi.

Source: Twitter
A bangaren wutar lantarki, Ministan Makamashi, Adebayo Adelabu, ya ce majalisar ta amince da dokar ƙasa ta farko a tarihi kan harkokin wutar lantarki a Najeriya.
Bugu da ƙari, Ma’aikatar Ruwa ta Tarayya ta samu amincewar majalisa domin gyaran gaggawa ga Dam ɗin Alau da ke Maiduguri a Jihar Borno.
Gwamnatin Najeriya ta amince da jami'o'i 11
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Bola Tinubu ta amince da kafa sababbin jami'o'in kudi 11 domin bunkasa harkokin ilimi a Najeriya.
Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) ta miƙa lasisin gudanarwa ga sababbin jami’o’in a wani taro da aka shirya a Abuja.
Shugaban NUC, Farfesa Abdullahi Ribadu ya ce tun bayan bude damar kafa jami’o’i masu zaman kansu a 1999, an samu gagarumar ci gaba a fagen ilimi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


