Bashin Naira Tiriliyan 4: Gwamnatin Najeriya Ta Fara Hararo Karin Kudin Wuta
- Ministan makamashi, Adebayo Adelabu, ya ce tattalin arzikin Najeriya ba zai iya ci gaba da daukar nauyin tallafin lantarki ba
- Ya bukaci a rungumi tsarin karin kudin wuta da ya dace da yadda ake amfani da lantarki domin farfado da bangaren samar da wuta
- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta biya kaso mai yawa daga cikin bashin N4tn da ake binta don hana rugujewar lantarki
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ministan makamashi, Adebayo Adelabu, ya bukaci 'yan Najeriya da su rungumi sabon tsarin farashin lantarki da zai yi daidai da amfani da wuta da kowanne mutum ke yi.
Adebayo Adelabu ya bayyana haka ne a yayin wata ganawa da shugaban kamfanonin samar da wuta a Najeriya (GenCos), Dr Joy Ogaji, da aka gudanar a Abuja.

Source: Twitter
The Nation ta wallafa cewa hadimin ministan, Bolaji Tunji ya bayyana cewa Adelabu ya jaddada bukatar sake nazari kan harkokin lantarki a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Tallafin lantarki ba zai dore ba” — Adelabu
Ministan ya bukaci ‘yan Najeriya su fahimci cewa dole ne a canja salon biyan kudin wuta zuwa wanda zai yi daidai da amfani da ita da ake domin kasar ba za ta iya saka tallafi ba.
Rahoton Channels TV ya nuna cewa Adelabu ya ce:
“Dole ne ‘yan kasa su fara biyan kudin da ya dace da wutar da suke amfani da ita.
"Gwamnatin tarayya za ta ci gaba da bayar da tallafi na musamman ga marasa galihu, amma ba za a iya cigaba da saka tallafin wuta gaba daya ba.”
Ya ce rashin wannan canjin na iya kara jawo tabarbarewar harkar wuta a kasar, wanda zai shafi rayuwar jama'a da ci gaban tattalin arziki gaba daya.
Gwamnati za ta biya bashin N4tn ga GenCos
A cewar ministan, gwamnati ta himmatu wajen warware matsalar bashin Naira tiriliyan 4 da ake binta, wanda ke zama barazana ga rugujewar sashen samar da wuta a Najeriya.
Ya bayyana cewa gwamnati za ta fara biyan kaso mai yawa daga cikin bashin, sannan sauran za a biya a hankali.
Adelabu ya ce akwai bukatar warware wannan lamari cikin gaggawa don kada a fada cikin matsalar rashin wuta a kasa baki daya.
Tinubu zai gana da shugabannin GenCos
Ministan ya bayyana cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gana da shugabannin GenCos nan gaba kadan domin hanzarta aiwatar da tsarin biyan bashin da suke bin gwamnati.
Ya ce matakin na daga cikin kokarin gwamnati na farfado da fannin wuta tare da tabbatar da dorewar samar da lantarki mai inganci ga ‘yan Najeriya.

Source: Getty Images
Adelabu ya jaddada cewa gwamnati ba za ta tsaya ba sai an samu gyara a bangaren lantarki wanda zai amfani dukkan al’umma.
Gwamnati ta kare shirin saka sola a Villa
A wani rahoton, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta bayyana cewa ba a Najeriya aka fara kafa sola a ma'aikatun gwamnati ba.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce ko a Amurka an taba sanya sola a fadar White House a Amurka.
Bayo Onanuga ya yi magana ne yayin da aka rika caccakar gwamnatin Bola Tinubu da ta ware Naira biliyan 10 don saka sola a Aso Villa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


