'Yan Ta'addan ISWAP Sun Farmaki Sansanin Sojoji, an Samu Asarar Rayuka

'Yan Ta'addan ISWAP Sun Farmaki Sansanin Sojoji, an Samu Asarar Rayuka

  • Ƴan ta'addan ƙungiyar ISWAP sun kai wani hari a sansanin sojoji da ke jihar Yobe a yankin Arewa maso Gabas
  • Dakarun sojoji sun yi artabu da ƴann ta'addan na tsawon awanni bayan harin da suka kai musu a cikin tsakar dare
  • Wata majiya ta tabbatar da samun asarar rayuka daga ɓangaren dakarun sojoji da ƴan ta'addan na ISWAP

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ƴobe - Ƴan ta’addan kungiyar Islamic State West Africa Province (ISWAP) sun kai hari garin Buni Gari da ke ƙaramar hukumar Gujba a jihar Yobe.

Ƴan ta'addan na ISWAP sun kai harin ne da da misalin ƙarfe 2:00 na dare a ranar Juma’a, 2 ga watan Mayun 2025.

'Yan ISWAP sun farmaki sojoji a Yobe
'Yan ta'addan ISWAP sun hallaka sojoji 4 a Yobe Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta ce wata majiyar tsaro ta tabbatar da faruwar lamarin.

Ƴan ISWAP sun kai hari a Yobe

Kara karanta wannan

Mele Kyari: Tsohon shugaban kamfanin NNPCL ya fada komar hukumar EFCC

Majiyar ta bayyana cewa ƴan ta’addan sun kai hari a wani ɓangare na hedkwatar dakarun rundunar 27 Brigade da ke Buni Gari.

Buni Gari yana ƙasa da kilomita bakwai daga Buni Yadi, inda makarantar dakaru na musamman ta sojojin Najeriya take.

Harin ya faru ne kwana biyu bayan taron gwamnonin Arewa maso Gabas da aka gudanar a Damaturu, inda suka tattauna batutuwa da suka shafi tsaro, talauci da kuma rashin kyawun hanyoyi a yankin

Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa ƴan ta’addan sun fara harbi ba kakkautawa kafin su bankawa wasu gine-gine mallakin jama'a da kuma wani gini na sojoji wuta.

Dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai sun yi arangama mai tsanani da ƴan ta’addan bayan harin da suka kai a Buni Gari.

Yobe: An hallaka dakarun sojoji

Jaridar Daily Tust ta ce wata majiya ta tabbatar mata da cewa an kashe sojoji guda huɗu yayin harin.

An shammace mu sai dai muka ji fashewar bama-bamai da kuma harbe-harbe masu ƙarfi, amma mun tsaya tsayin daka. An lalata yawancin kayan yaƙinmu a yayin fafatawar."

Kara karanta wannan

"Ƴan bindiga sun shiga uku": Abin da Tinubu ya ce kan matsalar tsaro a Katsina

"Eh, mun rasa wasu sojoji huɗu, kamar yadda su ma suka yi asarar mutane a lokacin artabun mai zafi da ya ɗauki awanni da dama."

- Wata majiya

'Yan ISWAP sun kai hari a Yobe
'Yan ta'addan ISWAP sun kashe sojoji a Yobe Hoto: Legit.ng
Source: Original

Me rundunar sojoji ta ce kan harin?

Rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da faruwar lamarin ta hanyar wata taƙaitacciyar sanarwa da ta wallafa a shafinta na X a ranar Asabar, 3 ga watan Mayun 2025.

“Dakarun rundunar Operation Hadin Kai na cikin fafatawa da ƴan ta’addan ISWAP a harin da suka kai Buni Gari, jihar Yobe."

- Rundunar sojojin Najeriya

ISWAP ta ɗauki alhakin kai hari a Borno

A wani labarin kuma, kun ji ƙungiyar ƴan ta'addan ISWAP ta ɗauki alhakin kai harin bam a jihar Borno.

Fashewar bam ɗin da ta yi sanadiyyar rasa ran mutum 26 ta auku ne a kusa da garin Rann, a ƙaramar hukumar Kala-Balge da ke jihar Borno.

Wani jami’in tsaro da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa wasu daga cikin gawarwakin mutanen da fashewar ta ritsa da su sun ƙone sosai, ta yadda ba za a iya gane su ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng