Neja: Alaƙa Ta Yi Tsami tsakanin Gwamna da Mataimakinsa? Umaru Bago Ya Yi Bayani

Neja: Alaƙa Ta Yi Tsami tsakanin Gwamna da Mataimakinsa? Umaru Bago Ya Yi Bayani

  • Gwamna Umaru Bago ya musanta raɗe-raɗin da ke yawo cewa alaƙa ta yi tsami tsakaninsa da mataimakinsa, Yakubu Garba
  • Bago ya ce shi da Kwamred Yakubu Garba tawagarsu ɗaya kuma manufarsu ɗaya ta kawo ci gaba da gina sabuwar jihar Neja
  • Ya bayyana cewa dangantakarsa da mataimakin gwamnan tana kyau da armashi, inda ya buƙaci jama'a su yi watsi da jita-jita

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Niger - Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya karyata rade-radin da ke cewa akwai sabani tsakaninsa da mataimakinsa, Yakubu Garba.

Gwamna Umaru Bago ya bayyana cewa yana da kyakkyawar dangantaka da mataimakin gwamna, babu wata tsama a tsakaninsu.

Gwamna Bago.
Gwamnan Neja ya musanta jita-jitar cewa alakarsa da mataimakinsa ta yi tsami Hoto: Mohammed Umaru Bago
Source: Facebook

Bago ya faɗi haka da yake hira da manema labarai bayan karɓar lambar yabo ta "Gwarzon Ma’aikata" daga ƙungiyoyin kwadago a bikin ranar ma’aikata a Minna, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

"Ɗan Arewa kaɗai," Dele Momodu ya faɗi wanda zai iya kayar da Shugaba Tinubu a 2027

Alaƙa ta yi tsami tsakanin Bago da mataimakinsa?

Ya bayyana dangantakar da ke tsakaninsa da mataimakin gwamnan Neja, Yakubu Garba a matsayin mai armashi.

A rahoton Tribune, Gwamna Bago ya ce:

“Jita-jita ce kawai, mu daina bata lokaci kan jita-jita. Dangantakarmu tana da kyau ƙwarai, babu wata matsala.
"Tawagarmu ɗaya kuma babu abin da zai raba mu. Burinmu ɗaya ne, kuma za mu cimma shi da ikon Allah, za mu gina sabuwar jihar Neja.”

Gwamna Bago ya halarci taron ranar ma'aikata

Gwamna Bago ya samu rakiyar Sanata Mohammed Sani Musa, mai wakiltar yankin Neja ta Gabas a Majalisar Dattawa, a wajen taron.

Ya bayyana cewa mataimakinsa bai samu damar halartar taron ranar ma'aikata na 2025 ba ne sabowa wasu muhimman ayyukan da suka sha ƙarfinsa.

Tun farko wani rahoto ya nuna cewa alaƙa tsakanin gwamnan da mataimakinsa ta yi tsami a ranar Litinin da aka fara yaɗa jita-jitar cewa Yakubu Garba na shirin yin murabus.

Kara karanta wannan

"Mun zama jihohi 3," Gwamna Otu ya hango abubuwan da ke janye gwamnoni zuwa APC

Yadda jita-jitar ta samo asali a Neja

Ko da yake babu wata sanarwa a hukumance kan batun, ganin Yakubu Garba ya fara tattara kayansa daga gidan da yake ciki ya ƙara rura wutar jita-jitar.

Majiyoyi sun bayyana cewa rashin jituwa ya fara shiga tsakanin Gwamna Bago da mataimakinsa ne tun bayan hawansu mulki a watan Mayu 2023.

Wasu na danganta matsalar da wani faifan sauti da aka ce an ji Yakubu Garba na sukar gwamnan tare da wasu jami'an gwamnati.

An ce Gwamna Bago ya nuna rashin jin daɗinsa da ya saurari faifan sautin kuma daga nan alaƙarsu ta soma rawa.

Mataimakin gwamnan Delta.
Zargin saɓani tsakanin Umaru Bago da Yakubu Garba ba gaskiya ba ne Hoto: Yakubu Garba
Source: Twitter

Gwamna Umaru Bago ya ƙaryata raɗe-raɗin

Rikicin ya ƙaru ne bayan sakin jerin sunayen 'yan takarar APC na zaɓen ƙananan hukumomin Neja da za a yi watan Nuwamba 2025, inda aka cire Babangida Wasa Kudo, ɗan takarar da Yakubu Garba ke marawa baya.

Sai dai a yanzu, Gwamna Bago ya musanta dukkan rahotanni da ke yawo, yana mai cewa babu wani saɓani tsakaninsa da mataimakinsa.

Kara karanta wannan

El-Rufa'i ya gano wanda ya fi dacewa ya mulki Najeriya a 2027

Mataimakin gwamnan Neja ya yi murabus?

A baya, kun ji cewa mataimakin gwamnan jihar Neja, Yakubu Garba ya ƙaryata jita-jitar da ake yaɗawa cewa ya yi murabus daga kan kujerarsa.

Babbar jami'ar hulɗa da jama'a ta mataimakin gwamnan, Ummikhultume Abdullahi, ta tabbatar da hakan a wata hira da aka yi da uta ta wayar tarho.

Mataimakin gwamnan ya ce bai yi murabus ba saɓanin raɗe-raɗin da mutane ke yaɗawa musamman a kafafen sada zumunta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262