Portable: Bayan Zayyano Laifuffukansa, Kotu Ta Tura Fitaccen Mawaki Gidan Kaso
- Wata kotun Majistare a jihar Ogun ta yanke wa mawaki Habeeb Okikiola hukuncin daurin wata uku a gidan yari bisa laifin cin zarafin dan sanda
- An kama mawakin da aka fi sani da Portable tun watan Maris 2023 bayan da ya buge wani babban ɗan sanda kuma ya hana jami’an tsaro kama shi
- Lauyan gwamnati ya bayyana cewa Portable ya aikata laifin a ranar 18 ga Nuwamba, 2022 a Okeosa, Ilogbo, yankin karamar hukumar Ifo
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abeokuta, Ogun - Wata kotun Majistare a jihar Ogun da ke zamanta a karamar hukumar Ifo a Ogun, ta daure mawaki a gidan kaso.
Kotu ta yanke wa mawaki Habeeb Okikiola da aka fi sani da Portable hukuncin daurin wata uku, tare da zabin biyan tarar N30,000.

Source: Instagram
An same Portable da laifin cin zarafin jami’in ‘yan sanda da kuma hana kama shi yayin da aka kai masa takardar kamu a baya, cewar The Nation.
Martanin Portable a kotu kan zarge-zargen
Hukuncin na zuwa bayan gurfanar da mawakin, Habeeb Okikiola Olalomi a gaban kotun Abeokuta da yan sanda suka yi.
Sai dai yayin zaman kotu, Portable ya musanta laifuffuka biyar da mai gabatar da karar ke tuhumarsa da su, ciki har da cin zarafi da amfani da makamai.
An tsare Portable bisa tuhumar hadin baki da kai wa jami'an gwamnatin Ogun hari kan yunkurin rufe wata babbar mashayarsa da ke garin.

Source: Instagram
Hukuncin da kotu ta yankewa Portable
An kama mawakin ne a watan Maris 2023 bayan da ya kai wa wani jami'in dan sanda hari kuma ya hana jami’ai aiwatar da umarnin kama shi.
Lauyan ‘yan sanda, Insfekta Olumide Awoleke, ya shaida wa kotu cewa Okikiola ya aikata laifin ne a 18 ga Nuwamba, 2022 da misalin karfe 11:00 na safe a Okeosa, Ilogbo.

Kara karanta wannan
Bayan shafe wata 2 a hannunsu, ƴan bindiga sun hallaka limami da danginsa a Zamfara
Takardar tuhumar ta ce:
“Kai Badmus Habeeb Okikiola, wanda aka fi sani da Portable, da wasu da ba a kama ba, kun hada baki domin aikata laifi wato cin zarafi, wanda hakan ya saba da sashi na 517 na dokar manyan laifuka ta jihar Ogun ta 2006.
“Ka kuma kai farmaki ga Osimosu Emmanuel Oluwafemi, ta hanyar dukan jikinsa a wannan rana, wanda ya sabawa sashi na 351 na dokar manyan laifuka.
"Haka kuma, a shekarar 2022, ka sace kayan waka a Okeosa, Ilogbo, ciki har da Yamaha H55, AKG P420 da sauran kayan 'studio'.”
A hukuncinsa, Alkalin babbar kotun, Babajide Ilo, ya same shi da laifi a tuhume-tuhume biyu, ya yanke masa wata daya da zabin biyan N10,000, da kuma wata biyu da zabin N20,000, Vanguard ta ruwaito.
'Yan sanda na neman Portable ruwa a jallo
A baya, kun ji cewa Rundunar ‘yan sanda a Ogun ta ayyana fitaccen mawaki Habeeb Okikiola a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo.

Kara karanta wannan
Abin fashewa da ake zargin bam ne ya tarwatse a Borno, sama da mutane 25 sun mutu
Hukumar na neman mawaki Portable ne bisa zargin kai hari ga jami’an gwamnati yayin da suke aikinsu a jihar.
An ce Portable da ‘yan daba tara sun kai farmaki da makamai, sun ji wa jami’an rauni, amma suka tsere suka kai rahoto wurin ‘yan sanda.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
