Fitattun 'Yan Najeriya 5 da EFCC Ta Cafke a Watanni 12 da Laifin da Suka Aikata

Fitattun 'Yan Najeriya 5 da EFCC Ta Cafke a Watanni 12 da Laifin da Suka Aikata

Abuja - Jami’an hukumar EFCC sun kama fitattun 'yan Najeriya biyar, ciki har da Emeka Okonkwo (E-Money) da Aisha Sulaiman Achimugu, bisa laifuffukan kuɗi daban-daban.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

An kama E-Money, sanannen mai harkar kiɗa da nishaɗi a jihar Legas, a gidansa da ke unguwar Omole, Legas da tsakar dare.

EFCC ta cafke fitattun 'yan Najeriya 5, ciki har da Aisha Achimugu da E-Money
Hagu zuwa Dama: Aisha Achimugu, jami'an hukumar EFCC, Emeka Okonkwo (E-Money). Hoto: @aisha_achimugu, @officialEFCC, @iam_emoney01
Source: Twitter

A gefe guda, EFCC ta kama Aisha Achimugu, wata shahararriyar ‘yar kasuwa, jim kaɗan bayan dawowarta daga London, kamar yadda NTA ta rahoto.

Lauyoyin Aisha Achimugu sun bayyana cewa jami'an EFCC sun kama fitacciyar 'yar kasuwar kasa da kasar ne da misalin ƙarfe 5 na safe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mashahuran 'yan Najeriya 5 da EFCC ta kama

A cikin watanni 12 (daga Afrilun 2024 zuwa Afrilun 2025), hukumar EFCC ta cafke wasu fitattun 'yan Najeriya bisa laifuffukan kuɗi daban-daban, inji rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Abin fashewa da ake zargin bam ne ya tarwatse a Borno, sama da mutane 25 sun mutu

1. Bobrisky (Idris Okuneye)

Hukumar EFCC ta cafke shahararren ɗan daudu, wanda ya yi shuhura a intanet, Idris Okuneye, da aka fi sani da Bobrisky, a watan Afrilu 2024, kamar yadda muka ruwaito.

Hukumar da ke yaki da rashawa da masu yi wa dukiyar al'umma zagon kasa, ta ce ta kama Bobrisky bisa zargin cin zarafin kuɗin Najeriya ta hanyar watsa Naira a wajen biki.

Bobrisky ya amsa laifinsa kuma kotu ta yanke masa hukuncin wata shida a kurkuku ba tare da zabin tara ba. An sako shi a watan Agusta 2024 bayan karewar wa'adinsa.

2. Ajayi Oluwabukola Temitope

‘Yar kasuwa daga Ibadan, Temitope Ajayi, ta shiga hannun EFCC a cikin watan Agusta, 2024 bisa zargin zambar da ta kai Naira miliyan 25.

An ce Temitope ta karɓi kuɗi daga mutane da dama da sunan za ta sayar musu da lemun kwalba amma ba ta cika wannan alkawari ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kebbi da gwamnoni 4 za su bar APC, su shiga hadakar Atiku? An ji gaskiya

Hukumar EFCC ta cafke 'yar kasuwar ne bayan da ta gudanar da bincike sakamakon karbar korafe-korafe daga waɗanda ta 'damfara.'

3. Cubana Chief Priest (Pascal Okechukwu)

Hukumar EFCC ta cafke mashahurin mai otal da gidan kwankwadar barasa, Cubana Chief Priest, a Afrilun 2024 bisa zargin watsa takardun Naira 'yan ₦500 a wajen wani taro.

Duk da cewa Cubana ya ce bai aikata laifin ba, amma daga bisani ya amince da sulhu da hukumar EFCC ta hanyar bayar da Naira miliyan 10 kuma wayar jama'a game da illar cin zarafin Naira.

4. Aisha Achimugu

Jami'an hukumar EFCC sun kama fitacciyar 'yar kasuwar kasa da kasa, Aisha Achimugu a ranar 29 Afrilu 2025 bayan ta dawo daga London.

An ce EFCC ta cafke ta ne kasa da awanni 24 da wata kotun tarayya mai zamanta a Abuja ta bayar da umarnin ta bayyana gabanta bisa zargin laifuffukan kuɗi da ba ta bayyana ba.

Lauyoyinta sun ce bai kamata hukumar EFCC su kama ta ba domin ta dawo kasar ne da kanta, kuma yanzu haka ta fara yajin cin abinci.

Kara karanta wannan

Jerin manyan 'yan siyasar da sauya sheka zuwa APC ya kare su daga binciken EFCC

Hukumar EFCC ta cafke E-Money a gidansa da ke Legas kan zargin cin zarafin Naira
Sanannen mai harkar kiɗa da nishaɗi a jihar Legasm Emeka Okonkwo (E-Money). Hoto: @iam_emoney01
Source: Twitter

5. Emeka Okonkwo (E-Money)

BBC ta rahoto cewa EFCC ta kama Emeka Okonkwo (E-Money) a Afrilun 2025 bisa zargin watsa dalar Amurka a bainar jama’a da kuma karya dokar musayar kuɗi.

An kama shi a gidansa da ke Omole, da ke jihar Legas. EFCC ta shaida cewa rana ci gaba da bincike kan zargin da ake masa kuma za ta aika sa kotu da ta kammala.

E-Money ya sha wahalar rayuwa kafin arziki

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Emeka Okonkwo, wanda aka fi sani da E-Money ya kasance talaka futuk, kafin daga bisani Allah ya sa ya zamo mai tarin dukiya.

Rahotanni sun bayyana cewa E-Money ya sha gwagwarmayar rayuwa kafin ya tara biliyoyin Naira da ya ke da su yanzu, tare da mallakar kamfanin Five Star Music.

Attajirin wanda aka haifa a ranar 18 ga watan Fabrairun 1981, a yankin Ajegunle da ke jihar Legas, ya kasance kani ga mashahurin mawaki, Kcee.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com