Yadda biloniyan Najeriya, E-Money ya sha wahalar rayuwa kafin ya tara dukiya

Yadda biloniyan Najeriya, E-Money ya sha wahalar rayuwa kafin ya tara dukiya

- Masu iya magana su kan ce, Tabaraka mai mayar da dan talaka sarki, kuma a bishi ana ta fadanci

- Mashahurin dan kasuwan nan mai suna Emeka Okonkwo wanda aka fi sani da E-Money ya tara dukiya

- Mutumin mai shekaru 39, ya mallaki makeken gida da motoci na shiga tsara, duk da dan talaka ne shi tilis

Wani dan Najeriya, mai suna Emeka Okonkwo, wanda aka fi sani da E-money, mashahurin dan kasuwa ne mai dukiya, yanzu haka shine mai kamfanin Five Star Music.

Biloniyan wanda aka haifa a ranar 18 ga watan Fabrairun 1981, a wuraren Ajegunle da ke jihar Legas, kuma kanin wannan mashahurin mawakin ne, wanda akafi sani da Kcee.

An san mutumin mai shekaru 39 da rayuwa cikin wadata, jaridar Legit.ng ta duba makeken gidansa wanda yake a Banana Island, wanda kimarsa ta kai naira biliyan 1.

Mutum ne mai matukar son jin dadi da more rayuwarsa, sannan gidansa yana da matukar kyau.

Yana da motoci na shiga tsara, wadanda ya ajiye a harabar gidansa.

Yadda biloniyan Najeriya, E-Money ya sha wahalar rayuwa kafin ya tara dukiya
Yadda biloniyan Najeriya, E-Money ya sha wahalar rayuwa kafin ya tara dukiya. Hoto daga gistoftheday.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Ku bani lambarsa, ya gamsar da ni matuka - Budurwa da aka yi wa fyade ta roki kotu

Mutumin dan asalin jihar Anambra ya fito daga gidan talauci amma zuciyarsa bata mutu ba, inda ya dage wurin neman na kansa.

Da a ce wani zai ce masa zai samu wannan wadatar a shekaru 20 da suka wuce, tabbas zai karyata.

KU KARANTA: Dakarun soji sun cafke wani da ake zargi da hada kai da 'yan bindiga

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya jinjina wa kotun Dubai, a kan yanke wa mutane 6 masu daukar nauyin 'yan Boko Haram hukunci, Daily Trust ta wallafa.

Ya yi farin cikin yadda cikin shekaru 11, aka samu hanyar gano masu daukar nauyin 'yan Boko Haram, wanda kungiyar ta yi ajalin dubbannin mutane da kuma rasa gidajen miliyoyin mutane, har da ma'aikatan gwamnatin wadanda suka kai kimar dala biliyan 9 a jihar Borno da sauran wuraren arewa maso gabas da Najeriya gabadaya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel