Akpabio Ya sake Kwabo Zance, Ya Shawarci 'Yan Najeriya Su Rungumi Talauci Hannu Bibbiyu

Akpabio Ya sake Kwabo Zance, Ya Shawarci 'Yan Najeriya Su Rungumi Talauci Hannu Bibbiyu

  • Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya bayyana cewa bai kamata 'yan Najeriya su rika duba talauci a matsayin mugun abu ba
  • Ya bayyana cewa ya kamata jama'ar kasar nan su dauki darasi daga rayuwar Fafaroma Francis na tawakkali da rashin tara abin duniya
  • Sanatan ya bukaci ‘yan Najeriya da su rungumi juna da haɗa kai, tare da raba abin hannunsu domin rage wa juna matsalar da ake ciki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya ce talauci ba laifi ba ne kuma wani lokaci ana kallonsa a matsayin falala ga dan adam.

Akpabio ya fadi hakan ne yayin da yake magana daga birnin Rome bayan halartar jana'izar Fafaroma Francis wanda aka birne a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

El-Rufa'i ya gano wanda ya fi dacewa ya mulki Najeriya a 2027

Akpabio
Sanata Akpabio ya shawarci yan Najeriya Hoto: Godswill Obot Akpabio
Source: Facebook

Arise News ta ruwaito cewa Akpabio ya shawarci ‘yan Najeriya da su yi riƙo da saƙon ƙaunar juna da haɗin kai, yana mai jaddada cewa talauci bai kamata a duba shi a matsayin mugun abu ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akpabio ya gano darasi daga rayuwar Fafaroma

Linda Ikeji ta wallafa cewa Akpabio ya yi nazari kan rayuwar marigayi Fafaroma Francis, wanda ya rasu yana da shekaru 88.

Shugaban majalisar dattawan ya bayyana halin Fafaroma a matsayin wani babban darasi da ‘yan Najeriya ya kamata su yi koyi da shi.

Ya ce:

"Idan ka duba cocin Katolika, ba kawai coci ba ne. Vatican ana kallonta a matsayin ƙasa ce. Don haka, shugaban ƙasa ne ya rasu kuma aka birne shi yau."

Ya jaddada cewa Fafaroma Francis, wanda ya jagoranci mabiya fiye da biliyan 1.5 a duniya, ya rasu ba tare da dukiya ba, inda ya ce:

"Mutum ne ya mutu yau a matsayin mutum – Fafaroma – wanda darajarsa ta kudi ba ta wuce $100 ba, yana nuni da cewa ba lallai ne mu bauta wa Allah cikin alfarma ba. Mafi kyau shi ne mu bauta masa ta hanyar sadaukar da kanmu saboda wasu."

Kara karanta wannan

Ba daidai bane: Peter Obi ya tausayawa dalibai kan wahalar rubuta JAMB

Shawarar Akpabio ga 'yan Najeriya

Sanata Akpabio ya ce ya kamata rayuwar Fafaroma ta zama abin koyi ga ‘yan Najeriya, yana mai karfafa musu gwiwa da su rika taimakon juna musamman a lokacin da ake fuskantar ƙalubale.

Sanata
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio Hoto: Godswill Obot Akpabio
Source: Facebook

Ya ce:

“Ya kamata ‘yan Najeriya su ƙaunaci juna, kuma cewa talauci ba laifi ba ne. Wani lokaci, talauci falala ce daga Ubangiji."
"Kuma duk abin da kake da shi, ya kamata ka iya raba shi da ‘yan uwanka, musamman a wannan lokaci na bukukuwan Easter.”

Akpabio ya magantu kan shirin hallaka Sanata

A baya, kun samu labarin cewa Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya shigar da ƙara gaban Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, kan zargin kisan kitsa kisa da aka yi masa.

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta shaidawa mabiyanta cewa Akpabio ya hada baki da gwamnan Kogi na yanzu, Ahmed Ododo da tsohon gwamna, Yahaya Bello domin a kashe ta.

A wata takarda da aka rubuta a ranar 3 ga Afrilu, Akpabio ya yi watsi da zargin Natasha, yana mai cewa hakan ƙarya ce da ake ƙoƙarin yaɗawa don ɓata masa suna da mutunci a Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng