Wani Abin Fashewa Ya Tarwatse a Gidan Yarin Maiduguri? NCoS Ta Fadi Abin da Ya Faru
- Hukumar NCoS ta karyata jita-jitar fashewar bam a gidan yarin Maiduguri, tana mai cewa wani fursuna ne ya cinna wa katifarsa wuta
- Jami’an tsaro sun dakile gobarar da Charles Okah ya haddasa, inda suka samu ashana a ɗakinsa, kuma aka garzaya da shi asibitin gidan
- Hukumar ta ce babu wata fashewar bam ko hari daga waje, sannan ta bayyana Charles Okah matsayin fursuna mai yawan haddasa fitina
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Borno - Hukumar NCoS ta karyata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa wani abin fashewa ya tarwatse a gidan yarin Maiduguri (MaSCC) da ke Borno.
A cewar hukumar, abin da ya faru ba fashewar bam ba ne, wani ɗan gidan yarin ne mai suna Charles Okah, ya cinna wa katifarsa wuta da gangan tare da ƙaryar cewa gobara ta tashi.

Kara karanta wannan
"Ba mu buƙatar albarkar shi kafin fatattakar Tinubu," Tsohon Sakataren gwamnatin Buhari

Source: Twitter
Fursuna ya cinna wa katifarsa wuta a Maiduguri
Wani jami’in hukumar NCoS ya bayyana cewa Charles ya cinna wa katifarsa wuta, sannan ya fara ihu ta taga yana cewa gobara ta tashi, inji rahoton Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce jami’an tsaro da ke bakin aiki a lokacin sun hanzarta zuwa inda lamarin ya faru, suka tarar da katifar tana ci da wuta kuma suka kashe wutar nan take.
Wannan matakin gaggawa ya hana yaduwar wutar ko ƙarin lahani ga ɗakin gidan yarin ko wurin gaba ɗaya.
Binciken da aka yi a ɗakin Charles ya sa an gano kwankon ashana ɗaya, wanda ya yi amfani da shi wajen banka wa katifar wuta.
An karyata tashin bam a gidan yarin Maiduguri
An garzaya da Charles zuwa asibitin gidan yari domin duba lafiyarsa, kuma yana samun sauƙi a halin yanzu yayin da aka canza masa wata katifar
Jami'in hukumar gidan yarin da ba a bayyana sunansa ba ya shaida cewa, “babu wata alamar fashewar bam, babu kuma wani hari daga waje da aka kai kan wannan gin."
Channels TV ta rahoto jami'in hulda da jama'a na hukumar NCoS, Umar Abubakar yana cewa:
“In har da gaske an samu fashewar bam a ɗakin Charles Okah, ta yaya ba zai ji rauni ba? Shi da kansa ne ya ke ihu yana cewa gobara ce ta tashi.
"Rahotannin da ake yadawa kan tashin bam din ba gaskiya ba ne, yanzu komai ya koma dai-dai a gidan yarin. Fursunoni na ci gaba da samun kulawa ba tare da tasgaro ba. A yi watsi da wannan rahoton karyar."
Hukumar ta kuma ƙaryata jita-jitar cewa babu jami’ai a bakin aiki a lokacin da abin ya faru, inda ta tabbatar da cewa jami’an tsaro sun amsa kiran gaggawa kuma sun tabbatar da tsaron sauran fursunoni.

Source: Getty Images
An ji yadda fursuna ke haddasa fitina
Dangane da yadda Charles ya samu ashana, hukumomin sun bayyana cewa an ba shi damar halartar taron coci na bikin Easter, wanda ake zaton ya yi amfani da damar wajen sace wa tare da boye ashanar da ya yi amfani da ita.
A kan dalilinsa na aikata hakan, jami’ai sun bayyana Charles a matsayin “fursuna mai son tayar da zaune tsaye wanda ya saba haddasa matsaloli akai-akai.”
Charles Okah yana tsare a gidan gyaran halin Maiduguri tun ranar 16 ga Maris, 2025, bayan hukuncin da aka yanke masa kan harin bam da ya afku a Eagle Square Abuja.
An ce harin bam din ya faru ne a ranar bikin ‘yancin kan Najeriya, lokacin mulkin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan.
Fursunoni sun tsere daga gidan yari a Maiduguri
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Hukumar gidajen gyaran hali ta Najeriya (NCoS) ta bayyana cewa fursunoni 274 sun tsere aga gidan yarin Maiduguri.
Ta ce fursunonin sun tsere ne yayin da ake kokarin kwashe su daga cibiyar da katangarta ta rushe sakamakon ambaliyar ruwa mai karfi.
Sai dai hukumar ta tabbatar da cewa tana da cikakkun bayanan fursunonin da suka hada da shaidar shacin yatsunsu, kuma za a kama su nan ba da jimawa ba.
Asali: Legit.ng

