Gobara ta kama gidan yarin Kuje da ke Abuja

Gobara ta kama gidan yarin Kuje da ke Abuja

- Gobara ta lullube gidan yarin kuje da ke Abuja da misalinn karfe 10:45 am na safe

Wata kungiyar da take fafutuka kwato ‘yancin fursunonin, (PAIN) ta dauki alhakin gobarar. PAIN ta bayyana haka ne ta hanyar rubuta wasikar ne da hanu ta lika wurin da ake lika sanarwa, amma kuma ma’aikatan ta cire wasikar.

PAIN ta ce “ta yi haka ne domin jawo hankalin al’umma su san irin zalunci da cin hancin da ke faruwa a gidan yarin”.

Kungiyar ta ce fursunoni da dama sun rasa rayukansu ne saboda rashin adalci, da cin amana, da cin hanci da kuma rashin kulawa da lafiyan fursunonin da aka tsare, a lokacin da ba su da lafiya da kuma tsabtace asbitin.

Samuel Mba ya rasu ne ranar talata 27-yuni, sanadiyar rashin magungunan da za a masa jinya da shi, an tsare shi ne shekara hudu da ta wuce da sunan yana jiran shari’a, haka ma sauran fursunoni suke ta mutuwa sanadiyar rashin kulawa, musamman daga fannin kula da lafiya na rashin isassun magunguna.

PAIN ta ce duk da dubban kudaden da ake ware wa don kula da lafiyar fursunoni, duk da haka sai sun fita nemo kudin da za su saya magani da kansu ga masu karfi, wadanda ba su da shi kuma sai abin da hali ya yi da su, ko kuma su nemi taimako daga wurin al’umman gari ko za su yi nasara.

Gobara ta kama gidan yarin Kuje da ke Abuja.
Gobara ta kama gidan yarin Kuje da ke Abuja.

PAIN ta bayyana halin da Asibitin gidan yari ke ciki, ta ce asibitin ya zama tamkar wani gidan ado, ko kuma na ajiyan kayaki, saboda rashin kayan aiki. Kungiyar ta ce ta kona gidan yarin ne saboda gwamnati ta sake yin ginin gidan yari na zamani saboda a samu wadatattun wurin ajiye masu laifi. An tara mutane da yawa wuri guda kamar dabbobi ai hakan bai dace ba.

Kungiyar ta kalubalanci alkalan kotun shari’a na ma su laifuka, “shin akwai bambanci tsakanin laifin talaka da mai kudi ne da ake bambbance hukuncisu? Ga azzalumai ‘yan siyasa da suke satar kudin al’umma amma ‘yan kwanaki kawai ake yanke musu a gidan yari, ko da an tsare su ana ba su kulawa na musamman tamkar ba a gidan yari suke ba. Ga wani talaka ya saci wayar selula an ajiye shi sama da shekara wai yana jiran shariya, kuma ba beli. Kungiyar PAIN ta kara da cewa “mafi yawa daga cikin alkalan suna saurin tura mutane gidan kaso ne saboda son zuciyako ra’ayi, amma ba wanda aka taba tsare shi a ciki ya ga yadda fursunoni ke wahala.

KU KARANTA: 'yan sanda sun kama dalibai uku ma su garkuwa da mutane a Enugu

Wuraren da suka kone sun hada dad akin magani na gidan yarin, da dakin masujiran shari’a mai lamba 2 yana daukan mutane 153, da dakin fursunoni mai lamba 3 wanda ke daukan mutane 322, da daki mai lamba 4 wanda ked a mutane 306, wadannan su ne wuraren da suka kone.

PAIN ta bayyana cewa adadin fursunoni 781 suka rasa matsuguni a gidan yarin Kuje da ke Abuja. Kuma suuna rokon alkalai da ta dubi halin da fursunonin ke ciki a yanzu musamman wadanda suke jiran shari’a da a yanke musu hukunci, domin rage yawan cunkoson da gidan yarin yake ciki.

Don samun labarai masu dadi da kayatarwa, ku ziyarci safin mu na

https://business.facebook.com/naijcomhausa/#

Don bamu shawara ko labarai, tuntubemu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng