Jerin ɗakuna 9 na gidan kurkuku mafi alfarma a duniya

Jerin ɗakuna 9 na gidan kurkuku mafi alfarma a duniya

Tunanin zaman gidan kurkuku yana jefa mutane cikin firgici, kuma fargabar bai wa duga-dugai hutu a gidan gyara halin yana sa mutane su rika kiyaye doka.

Legit.ng ta kawo muku jerin gidajen kurkuku guda tara na alfarma wanda da yiwuwar baku san da kasancewar su ba a doron kasa.

Kamar yadda muka yakito daga shafin swoopwhoop.com, ga jerin gidajen gyara hali guda tara da aka ƙawata su da kayayyaki na alfarma.

1. Bastoy Prison- Kasar Norway

Bastoy Prison
Bastoy Prison
Asali: UGC

Bastoy Prison
Bastoy Prison
Asali: UGC

Bastoy Prison
Bastoy Prison
Asali: UGC

Bastoy Prison is located in Oslofjord and it houses a little over 100 inmates. These inmates enjoy luxuries like tennis, horseback-riding, fishing and sunbathing.

Kurkukun Bastoy yana cikin garin Oslofjord da ke Kudu maso Gabashin kasar Norway. Yana kuma dauke da fursunoni da suka haura 100 kadan.

Wadannan fursunonin suna samun jin daɗi kamar wasan tennis, hawa-dawakai, kamun kifi da kuma shan hasken rana.

2. HMP Addiewell - Kasar Scotland

HMP Addiewell
HMP Addiewell
Asali: UGC

HMP Addiewell
HMP Addiewell
Asali: UGC

Gidan Yarin Addiewell wanda ake yi kirari da 'Dan Sarauniya', yana Kudancin kasar Scotland, inda ake horas da fursunoni a kan harkokin sana'a ta tsawon awanni 40 a kowane mako.

Wannan gidan gyaran yana maida hankali ne kan taimaka wa fursunoni su koma irin rayuwar masu 'yanci cikin tsari mai ma'ana gamsarwa.

3. Otago Corrections Facility - Kasar New Zealand

Otago
Otago
Asali: UGC

Otago
Otago
Asali: UGC

Kurkukun Otago ta tanadar wa fursunoni dakuna masu kyau da za su samu damar jin dadi da walwala. Kurkukun ya na maida hankali wajen horas da fursunoni a kan sana'o'in hannu.

4. Justice Center Leoben - Kasar Austria

Justice Center Leoben
Justice Center Leoben
Asali: UGC

Gidan kurkukun The Justice Center, yana ba kowane fursuna daki daya nasa shi kadai, kuma yana dauke da dakin girki, bandakin wanka da akwatin talbijin.

Kurkuku yana dauke da wuraren atisaye da motsa jiki, filin wasan kwallon kwando da filin shakatawa.

5. Aranjuez Prison - Kasar Spain

Aranjuez
Aranjuez
Asali: UGC

Aranjuez
Aranjuez
Asali: UGC

Gidan yarin Aranjuez yana ba da damar 'yan kananan yara su zauna tare da iyayensu masu laifi. Wannan gidan gayra hali yana wuraren wasan da zai debewa 'yan kananan yara kewa.

A wannan kurkuku, iyayen da aka daure ana basu damar yin rayuwa da 'yan kananan 'ya'yansu da ba su da suka dan haura mataki na shayarwa.

6. Champ-Dollon Prison - Kasar Switzerland

Champ-Dollon
Champ-Dollon
Asali: UGC

Champ-Dollon
Champ-Dollon
Asali: UGC

Wannan gidan kaso yana ba fursunoni dama su ji tamkar su na dakunan kwana ne a makarantu na jami'a. An kawata wannan gidan gyara hali yana alfahari da faffadan wurin shakatawa da na wanka.

7. JVA Fuhlsbuettel Prison - Kasar Jamus

JVA Fuhlsbuettel
JVA Fuhlsbuettel
Asali: UGC

KARANTA KUMA: Zaftare kasafin kudin Ma'aikatar Lafiya da ta Ilimi: SERAP ta kai karar Buhari Majalisar Dinkin Duniya

JVA Fuhlsbuettel
JVA Fuhlsbuettel
Asali: UGC

Wannan gidan yari ya zama tamkar gida ga fursunoni da za su shafe tsawon lokaci su na cin sarka. Yana da wadatattun dakuna masu dauke da gado, kujera da bandakin wanka.

Ana bai wa fursunoni injunan wankin sannan kuma suna da damar shiga dakin taro da dakin shakatawa.

8. Sollentuna Prison - Kasar Sweden

Sollentuna
Sollentuna
Asali: UGC

Wannan gidan yari yana ba kowane fursuna daki daya mai dauke da wadataccen gado da bandakin wanka.

An tanadarwa fursunonin dakin motsa jiki, dakin dafa abinci, da kuma filin shakatawa mai fadi cike da talabijin da kujeru.

9. Halden Prison, Norway

Halden
Halden
Asali: UGC

Halden
Halden
Asali: UGC

Ana ganin cewa babu wani gidan yari daka walwala a duk duniya tamkar gidan kurkukun Halden. Kowane fursuna yana iya tsare sirrinsa cikin jin dadi da kwanciyar hankali.

Ana koyawa fursunoni sana'o'i tare da ba su damar yin wasanni. Su na kuma da wuraren motsa jiki, da dakin buga waka.

Irin wannan gidan cin sarka masu laifin da za su shafe lokaci mai tsawo suke fatan a kai su.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel