Kuma dai: Majalisa Ta Kawo Kudurin da Zai Hana Tinubu, Atiku, Obi Yin Takara

Kuma dai: Majalisa Ta Kawo Kudurin da Zai Hana Tinubu, Atiku, Obi Yin Takara

  • Majalisar wakilai ta tsallakar da kudirin da ke hana 'yan takarar shugaban kasa da gwamna da suka haura shekaru 60 a duniya shiga zabe
  • Baya ga dokar kayyade shekaru, majalisar ta amince da kudirin kirkirar Jami’ar Alvan Ikoku da sabuwar karamar hukumar Ideato ta Yamma
  • Majalisar ta kuma saurari kudirorin kirkirar sababbin jihohi biyu; Jihar Wan daga Arewa ta Tsakiya da Jihar Gobir daga Arewa maso Yamma

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A ranar Alhamis, majalisar wakilan Najeriya ta tsallakar da kudurin da ke neman hana Atiku Abubakar, Peter Obi, Bola Tinubu, da sauran su yin takara.

An rahoto cewa, kudirin dokar da ya tsallake karatu na biyu, zai hana wadanda suka kai shekaru fiye da 60 yin takarar kujerar shugaban kasa ko gwamnan jiha.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun cafke mataimakin shugaban ƙasa, sabon yaƙi na shirin ɓarkewa a Sudan

Majalisar wakilai ta kawo kudurin da zai hana Atiku, Obi, Tinubu takarar shugaban kasa.
Kudurin hana 'yan sama da shekaru 60 takara zai shafi Atiku, Tinubu, Obi da sauransu. Hoto: @officialABAT, @atiku, @PeterObi
Asali: Twitter

Rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa Hon. Ikeagwuonu Ugochinyere ne ya dauki nauyin kudurin, wanda ke neman sauya wasu sassa na kundin tsarin mulkin 1999.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce, idan har kudurin ya tsallake karatu na uku, kuma shugaban kasa ya amince da shi, zai sake fasalin sharuddan cancantar tsayawa takarar manyan kujerun siyasa.

Muhimman abubuwan da kudirin ya kunsa

Wasu muhimman abubuwa da wannan sabon kudurin doka ya kusan, sun hada da:

  • ‘Yan takarar shugabancin kasa da gwamna ba za su wuce shekaru 60 ba a lokacin da za su tsaya takara.
  • Dole ne ‘yan takarar su mallaki kwalin digiri na farko a fannin da suke da kwarewa a kai, a matsayin mafi karancin takardar karatu.
  • Kudirin ya nemi gyara sashe na 131 na kundin tsarin mulki domin shigar da bukatar kayyade shekaru ga 'yan takarar shugaban kasa, da kuma sashe na 177 domin gwamnonin jihohi.

Muhimman kudirori da majalisar ta amince da su

Kara karanta wannan

'Yara miliyan 1.5 za su mutu': Najeriya na fuskantar sabuwar barazana daga Amurka

Baya ga dokar kayyade shekaru ga 'yan takarar shugaban kasa da gwamna, majalisar ta kuma amince da wasu kudirori da suka hada da:

1. Kudirin kirkiro jami’ar Alvan Ikoku

Rahoto yanuna cewa Hon. Tajudeen Abbas, mataimakin shugaban majalisar da Ikenga Imo Ugochinyere ne suka dauki nauyin kudirin.

Wannan kuduri yana neman a mayar da kwalejin ilimi ta Alvan Ikoku da ke a jihar Imo zuwa jami’ar tarayya.

2. Kudirin kirkiro karamar hukumar Ideato ta Yamma

An gabatar da wannan kudurin ne domin kirkiro wata sabuwar karamar hukuma a jihar Imo domin bunkasa ayyukan mulki da ci gaba a jihar.

3. Raba mukaman siyasa ga matasa da nakasassu

An ce Hon. Ugochinyere ne ya dauki nauyin kudirin da ke neman tabbatar da cewa matasa da mutane masu fama da nakasa suna da kason su a nade-naden mukaman siyasa.

4. Kudirin canza harkokin kasuwanci

Majalisar wakilai ta karbi kudurorin da ke neman yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin Najeriya
Bayan kudurin kayyade shekaru 'yan takara, majalisa ta karbi muhimman kudurori. Hoto: @HouseNGR
Asali: Facebook

Wannan kudiri na neman bai wa gwamnatocin tarayya da jihohi ikon hada gwiwa wajen tafiyar da harkokin kasuwanci don bunkasa tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Za a share hawayen ƴan Najeriya, Majalisa ta ɗauki mataki kan tsadar datar MTN da Airtel

5. Kudirin kara yawan kujeru ga mata a majalisa

Hon. Kafilat Ogbara ta dauki nauyin kudirin da ke neman kara yawan mata a majalisar dokoki ta tarayya da ma majalisun dokoki na jihohi.

6. Kudirin sauya tsarin shari’a

Kudirin hanzarta shari’a wanda Hon. Benjamin Okezie Kalu ya dauki nauyi, da kudirin karin yawan alkalai a Kotun Koli da kotun daukaka kara wanda Hon. Bello Kaoje ya dauki nauyi sun tsallake karatu.

7. Kudirin kirkiro sababbin jihohi

Rahoton ya bayyana cewa, an gabatar da kuduri a gaban majalisar da ke neman kirkirar jihar Wan (Arewa ta Tsakiya) da jihar Gobir (Arewa maso Yamma).

Wadannan dokoki suna da daga cikin wadanda aka gabatar, a shirin sake fasalin tsarin mulkin Najeriya, da nufin kara damawa da matasa da mata a siyasa, da kuma inganta harkokin tattalin arziki da shari’a.

"Ka tsufa, ka hakura da takara" - George ga Atiku

Kara karanta wannan

Kariya ta kare: Majalisa ta amince da kudirin da zai tubewa ƴan siyasa zani a kasuwa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Olabode George ya dage kan cewa babu wani dalili da Atiku Abubakar zai sa sake neman tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Tsohon mataimakin shugaban PDP na kasar ya nanata cewa, yanzu Atiku ya yi tsufan da bai kamata a ce ya nemi takarar shugabancin Najeriya ba

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel