Kuma dai: Yawan alkalan kotun koli ya sake ragu wa zuwa 13

Kuma dai: Yawan alkalan kotun koli ya sake ragu wa zuwa 13

Yawan alkalan kotun koli ya ragu daga 14 zuwa 13 bayan mai shari'a Amiru Sanusi yayi murabus a yau Litinin. Wannan cigaban ya biyo bayan koken da alkalin alkalai Jastis Tanko Muhammad yake yi na cewa shi da abokan aikinsa sunyi kadan a kotun kolin.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, kundin tsarin mulkin kasar nan ya aminta da alkalai 21 ne a matsayin cikakkun alkalan kotun kolin, abinda ba a taba yi ba a kasar nan.

Yawan alkalan kotun kolin ya kai 17 a ranar 18 ga watan Janairu, 2019 lokacin da tsohon alkalin alkalai Walter Onnoghen ya rantsar da Jastis Uwani Abba-Aji a matsayin alkaliyar kotun.

Amma kuma bayan barin Jastis Onnoghen a watan Afirilu 2019 da kuma murabus din Jastis Kumai Akaahs da Sidi Bage a shekarar da ta gabata, jimillar alkalan kotun kolin sun koma 14.

A watan Yuni 2019, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rubuta wasikar bukatar alkalin alkalai Jastis Tanko Muhammad da ya gaggauta zaben karin alkalai biyar don cike gibin yawan alkalan kotun kolin kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Kuma dai: Yawan alkalan kotun koli ya sake ragu wa zuwa 13
Kuma dai: Yawan alkalan kotun koli ya sake ragu wa zuwa 13
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Abubuwa 5 da ke fitar da soyayyar namiji daga zuciyar mace

Amma kuma har yanzu shugaban kasar bai yi komai ba a kan sunayen alkalan kotun daukaka kara da aka zaba don cike gibin tun a watan Oktoba na 2019.

A ranar Juma'a da ta gabata ne daraktan yada labarai na kotun kolin, Dr Festus Akande ya sanar da murabus din Jastis Amiru Sanusi, wanda ya fara aiki a kotun kolin a watan Mayu na 2015.

Da wannan murabus din nashi ne alkalan kotun kolin suka koma 13 wanda hakan ke bayyana gibin alkalai 8 kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar.

A lokacin da aka tuntubi daraktan yada labarai na kotun kolin, ya ce ba shi da masaniya a kan dalilin tsaikon da aka samu wajen tabbatar da alkalan da aka mika sunyensu don cike gibin kotun kolin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel