Jami'an Tsaro Sun Cafke Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sabon Yaƙi na Shirin Ɓarkewa a Sudan

Jami'an Tsaro Sun Cafke Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sabon Yaƙi na Shirin Ɓarkewa a Sudan

  • Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir, ya ba da umarnin kama mataimakinsa, Riek Machar, abin da ka iya haddasa wani sabon rikici a ƙasar
  • Manyan kasashen duniya sun fara janye jakadunsu da ma’aikatansu daga Sudan ta Kudu bayan harbe-harbe sun karade Juba, babban birni
  • Masana na gargadin wannan rikici na iya jefa Sudan ta Kudu cikin sabon yakin basasa wanda zai yi sanadiyyar asarar dubban rayuka

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sudan ta Kudu - Shugaban ƙasar Sudan ta Kudu ya kama mataimakinsa, a cewar wata sanarwa da jam’iyyar mataimakin shugaban ta fitar a ranar Alhamis.

Rahoton ya bayyana cewa wannan matakin na iya jefa ƙasar da ke da arzikin mai, amma mai fama da fatara, a cikin sabon yakin basasa.

Masana sun yi magana da aka kama mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu
Shugaban kasar Sudan ta Kudu ya sa jami'an tsaro sun kama mataimakinsa. Hoto: Majak Kuanymajak Kuany/AFP/Getty Images
Asali: Getty Images

Kama mataimakin shugaban kasa a Sudan ta Kudu

Kara karanta wannan

Rigimar sarauta: Kalu ya hadu da Aminu Bayero a taro, ya ƙi kiransa da 'sarkin Kano'

Rahoton Washington Post ya nuna cewa Shugaba Salva Kiir ya ba da umarnin kama mataimakin shugaban Sudan ta Kudu na farko, Riek Machar, a daren Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka nan, an kwace makaman masu tsaron mataimakin shugaban kasar tare da kame su, a cewar sanarwar da jam'iyyar Machar ta fitar.

Nicholas Haysom, wakili na musamman na ofishin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya kuma shugaban ofishin MDD a Sudan ta Kudu, ya ce:

"A daren yau, shugabannin ƙasar suna kan wata babbar gaba; ko dai su jefa ƙasar cikin rikici, ko kuma su ja ta zuwa ga zaman lafiya, farfado da tattalin arziki da dimokuraɗiyya."

Jakadun kasashen waje, ciki har da Amurka, Jamus da Birtaniya, sun fara rufe ofisoshinsu ko kuma janye ma'aikatansu, tare da kira ga 'yan kasashensu da su bar ƙasar yayin da jirgin sama ke ci gaba da tashi.

Amurka ta tsoma baki kan rigimar Sudan ta Kudu

Kara karanta wannan

2027: 'Yar takarar gwamnan APC, Aishatu Binani ta gana da shugaban SDP

A safiyar Laraba, kafin a kama Machar, an ji harbe-harbe a wurare da dama a babban birnin ƙasar, Juba, kamar yadda rahoton Reuters ya nuna.

Ofishin harkokin Afirka na ma’aikatar harkokin wajen Amurka ya wallafa a shafinsa na X cewa:

"Mun shiga damuwa kan rahoton da ke nuna cewa an kama tare da tsare mataimakin shugaban Sudan ta Kudu, Machar, a gidansa.
Mu na kira ga Shugaba Kiir da ya janye wannan mataki don guje wa ƙara dagula lamarin."

Babu wata sanarwa daga Shugaba Kiir ko wani jami'in gwamnati ko soji kan batun.

Barazanar yakin Basasa a Sudan ta Kudu

Kama mataimakin shugaban Sudan ta Kudu na barazanar barkewar yaki a kasar
Mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu na farko, Riek Machar. Hoto: @Drriekmachar
Asali: Twitter

Masana sun yi gargadin barkewar yakin basasa a kasar Sudan ta Kudu, tare da tuno yadda yakin na baya ya gurguntar da kasar, saboda yana cike da fyade, tilasta yara shiga aikin soja, yunwa da kisan kiyashi kan ƙabilanci.

Yakin basasar na baya, ya ƙare ne da aka cimma yarjejeniyar zaman lafiya a 2018, wacce ta samar da gwamnatin haɗin gwiwa da Kiir da Machar ke jagoranta tare.

Kara karanta wannan

Dawowar Fubara: Ana rade radin yin sulhu a Rivers, Wike ya yi magana

Alan Boswell, daraktan shirin kungiyar rikice-rikice ta kasa da kasa (ICG) a yankin Afirka, ya ce:

"Alamu na nuna Shugaba Kiir ke ƙara rura wutar wannan rikici. Wasu a Juba na fargabar cewa yana ƙoƙarin tayar da yaki saboda ƙabilanci."

Kiir da Machar sun fito ne daga ƙabilu daban-daban da ke yawan rikici kan ƙasa, siyasa da kiwo. Kiir na daga ƙabilar Dinka, yayin da Machar ke daga ƙabilar Nuer.

Najeriya ta tura sojoji zuwa Sudan ta Kudu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Najeriya ta tura sojoji 171 zuwa Abyei, iyakar Sudan da Sudan ta Kudu, domin aikin wanzar da zaman lafiya a ƙarƙashin shirin UNISFA.

Manjo-Janar Boniface Sinjen ya yi kira ga sojojin da su kasance masu kwarewa da da’a, tare da nisantar duk wani abu da ka iya bata martabar Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng