Jirgi Majalisar Dinkin Duniya ya yi hatsari dauke da albashin ma'aikata a Sudan ta Kudu

Jirgi Majalisar Dinkin Duniya ya yi hatsari dauke da albashin ma'aikata a Sudan ta Kudu

- Jirgin kwasan kaya na Majalisar Dinkin Duniya ya yi hatsari bayan ya dauko albashin ma'aikatan hukumar samar da abinci ta Majalisar

- Mutane tara ne ke a cikin jirgin lokacin afkuwar lamarin, takwas daga ciki sun mutu

- Har ila yau albashin ma'aikatan kimanin dalar Amurka 35,000, sama da miliyan 16 kenan a kudin Najeriya ya kone kurmus

Rahotanni da muke samu ya nuna cewa wani jirgin kwasan kaya na Majalisar Dinkin Duniya ya yi hatsari bayan ya dauko albashin ma'aikatan hukumar samar da abinci ta Majalisar, sashin Hausa na BBC ta ruwaito.

An tattaro cewa irgin ya yi hatsari ne a kusa da Juba, babban birnin Sudan ta Kudu. Kuma mutane tara ne ke a cikin jirgin lokacin afkuwar lamarin, takwas daga ciki sun mutu.

Hatsarin ya afku ne a ranar Asabar, 22 ga watan Agusta.

Mutum hudu daga cikin mutanen da suka mutu a hatsarin 'yan kasar Sudan ne, biyu kuma daga Tajikistan, yayinda dayan kuma ya kasance daga kasar Ukraine.

Shugaban kasar Sudan ta Kudu, Salva Kiir ne ya bayyana hakan a cikin wani sakon ta'aziyya da ya fitar.

Mutumin da ya rayu na asibiti ana duba lafiyarsa.

An tattaro cewa Bankin Opportunity Bank ne ya yi hayar jirgin domin kai albashin ma'aikatan hukumar WFP da ke a birnin Wau a Sudan ta Kudu.

Jirgi Majalisar Dinkin Duniya ya yi hatsari dauke da albashin ma'aikata a Sudan ta Kudu
Jirgi Majalisar Dinkin Duniya ya yi hatsari dauke da albashin ma'aikata a Sudan ta Kudu Hoto: Bdnews24
Asali: UGC

Ministan sufuri na kasar ya bayyana cewa kudin da jirgin ya dauko sun kone kurmus inda aka yi asarar kusan dalar Amurka 35,000, sama da miliyan 16 kenan a kudin Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Daga dawowa: ‘Yan Najeriya sun chaa a kan Aisha Buhari saboda ta yi kira ga inganta asibitoci

A wani labari na daban, uwargidan shugaban kasar Najeriya, AIsha Muhammadu Buhari, ta bayyana abinda ta fuskanta yayin da take cikin jirgin dakarun sojin saman Najeriya (NAF), yayin da take dawowa daga UAE bayan duba lafiyarta da ta je yi.

A yayin sanar da dawowarta, matar shugaban kasan a wata takarda da ta fitar a ranar Asabar, ta bayyana yadda wata iska mai karfi a sararin samaniya ta kusa ragargaza jirgin da take ciki.

Ta bayyana kwarewa da dagewar matukin jirgin da zama daya daga cikin abinda ya tseratar da su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel