Kasuwa ba Tabbas: Wasu Ƴan Najeriya Sun Yi Asarar Naira Tiriliyan 1.4 a Mako 4
- Kasuwar hannun jari ta NGX ta gamu da asarar Naira tiriliyan 1.4 cikin makonni hudu, yayin da jimillar jarin kamfanoni ya ragu zuwa N65.819tn
- Ma'aunin hannun jari na ASI ya ragu da kashi 2.7%, wanda ke nuna ci gaba da faduwar kasuwa duk da saukar farashin kayayyaki a Najeriya
- Yayin da 'yan kasuwa ke cike da fargabar lalacewar kudinu, masana sun ce wannan babbar dama ce ta sayen hannun jari a farashi mai sauki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Kasuwar hannun jari ta Najeriya (NGX) na ci gaba da fuskantar tsiyayewar kudi, inda ta 'yan kasuwarta suka tafka asarar Naira tiriliyan 1.4 a cikin makonni hudu a jere.
A ƙarshen ranar Juma’a, jimillar jarin kamfanonin da aka yi hada-hadarsu ya ragu daga Naira tiriliyan 67.193 zuwa Naira tiriliyan N65.819, daidai da ragin kashi 2.1.

Asali: Getty Images
All-Share Index (ASI), wanda ke auna darajar kasuwar hannun jari, ya ragu da makin 2,858.43 (kashi 2.7), inda ya rufe cinikin ranar a 104,962.96 daga 107,821.39, inji rahoton Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu zuba jari na asara a kasuwar NGX
Duk da saukar hauhawar farashin kayayyaki, an ce kasuwar hada-hadar ba ta wani daga sama ba, yayin da masu saka jari ke ci gaba da nuna fargaba kan saukar dukiyarsu.
Masu saka jari na ci gaba da nuna damuwa kan rashin tabbas a kasuwar hada-hadar kudi ta duniya, da canjin kudaden waje, da shirin gwamnati kan gyara kudin kasar.
Cinikin hannun jari ya ragu sosai, inda jimillar hannun jarin da aka sayar a mako ya sauka da kashi 11.5% zuwa Naira biliyan 2.90.
Jimillar kuɗin da aka samu a hada-hada ya ragu da kashi 24.3%, inda ya aka samu faduwar kudin da ake juyawa da Naira biliyan 8.06, sakamakon ƙauracewar masu zuba jari.
Masana sun bayyana cewa wannan koma bayan ya samo asali ne daga fargabar da masu saka jari ke yi kan ribar kamfanoni da matsin tattalin arziki.
Manyan bangarorin da suka yi asara
Daga cikin manyan bangarori shida da ake bin diddiginsu, biyar sun fuskanci hasara, yayin da bangaren kayan masarufi kadai ya samu ɗan ci gaba.
Rahoton This Day ya nuna NGX-CGI ya samu ƙaruwa da kashi 0.06%, sakamakon karuwar sha’awar mutane kan zuba jari a kamfanonin Neimeth, NNFM, NASCON da Dangote Sugar.
A gefe guda, bangaren masana’antu ya fi shan wahala, inda ya samu asarar kashi 3.39%, sakamakon sayar da hannun jarin kamfanin simintin BUA, UPDCREIT da Cutix Plc.
Bangaren hada-hadar kuɗi ma bai tsira ba, domin NGX-BI da ke auna hanun jarin bankuna ya ragu da kashi 2.5%, yayin da NGX-II da ke auna hannun jarin inshora ya ragu da kashi 2.8%.
An samu rububin sayar da hannun jarin kamfanonin hada-hadar kuɗi kamar Universal Insurance, Sovereign Trust Insurance, FCMB, FirstBank HoldCo da AccessCorp.

Kara karanta wannan
'Yan sanda sun kama matasa da bindigogi 10, harsasai 124 za su kai wa ƴan ta'adda
Haka nan, bangaren mai da iskar gas ma ya tafka asara, inda NGX-OGI da ke auna hannun jarin mai da gas ya ragu da kashi 1.08%, yayin da NGX-CI da ke auna hannun jarin kayayyaki ya faɗi da kashi 0.45%.
Masana na ba da shawarar sayen hannun jari

Asali: UGC
Duk da haka, masana a cibiyar Cowry Asset sun ce wannan babbar dama ce ga masu saka hannun jari na dogon lokaci domin sayen hannun jari a farashi mai sauki.
Sun ce kasuwar ta sauka kasa fiye da kima, wanda ke nuna cewa masu hikima a cikin masu saka jari na iya amfani da wannan dama don mallakar hannun jari mai yawa.
Masana sun shawarci masu saka jari da su yi nazari kan manyan kamfanonin hannayen jari da ke ba da riba, su sayi hannayen jarin su ajiye don samun riba mai yawa a gaba.
Sai dai har yanzu ba a bayyana lokacin da kasuwar za ta farfado ba, yayin da masu saka jari ke ci gaba da zaman jiran ganin sauyi a tattalin arzikin Najeriya.
Masu zuba jari za su gina matatun mai
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamnatin Tarayya ta ce wata gamayyar masu zuba jari daga Koriya ta Kudu za ta gina matatun mai hudu a sassa daban-daban na Najeriya.
Ministan albarkatun mai, Heineken Lokpobiri, ya ce matatun za su iya tace ganguna 100,000 na mai a kowace rana, wanda zai taimaka wajen bunkasa samar da mai a kasar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng