Kamfanoni 47 sun biya masu hannayen jari N1.1trn a 2019

Kamfanoni 47 sun biya masu hannayen jari N1.1trn a 2019

Kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya, NSE, ta jera wasu kamfanonni 47 da za su biya naira tiriliyan 1.11 ga masu hannayen jarinsu na ribar da suka samu a bara.

Wannan yana kunshe cikin rahoton shekara-shekara da kasuwar hada-hadar hannayen jarin kasar ta fitar kamar yadda lissafin da kamfanonin suka fitar ya nuna.

NSE ta bukaci a fara lissafi a kan kamfanonin 47 tun a watan Maris gabanin dokar kulle da aka shimfida saboda annobar korona ta tsayar da al'amura.

Sai dai hakan ya tilastawa NSE tsawaita wa'adin gabatar mata da bayanan lissafin kudin wanda ya bai wa kamfanonin damar samun karin kwanaki 60 har zuwa ranar 29 ga watan Mayu.

An yi wa kamfanonin rangwami domin samun damar miko bayanin lissafin kudinsu na shekara-shekara da ta kare a ranar 31 ga watan Dasumban 2019.

Kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya
Kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya
Asali: UGC

Kididdiga ta nuna cewa, kamfanin sadarwa na MTN, zai fi kowane kamfani biyan masu hannayen jari inda adadin kudin suka kai naira biliyan 281.5 cikin ribar da ya samu a bara kadai.

Kamfanin Siminti na Dangote ya biyo baya da naira biliyan 272.6.

Masu hannayen jari a kamfanonin biyu za su mallaki naira biliyan 558 cikin jimillar kudin masu hannayen jarin da zaa raba.

Kamfanin Siminti na Dangote da na MTN, za su biya masu hannayen jari kashi 55.8 cikin 100 daga cikin gaba daya jimillar kasafin masu hannayen jarin da za a rarraba da aka samu bara.

KARANTA KUMA: Bayyana kadarori: SERAP ta maka Buhari da Osinbajo a Kotun daukaka kara

Masu hannun jari na sauran kamfanoni 45 za su samu naira biliyan 442 wanda ya kasance kashi 44.2 cikin dari.

Kamfanin MTN ya samu karin kudin shiga da naira biliyan 122, inda hakan ya sa kamfanin ya samu ribar naira biliyan 60 a bara.

Shi kuwa kamfanin siminti na Dangote, ya samu nakasu wajen samun kudin shiga da naira biliyan 8, wanda ya janyo masa asarar riba idan an kwatanta da ribar da ya samu a shekarar 2018.

Ga dai adadin kudin hannayen jari da sauran manyan kamfanonin za su raba bayan fitar da lissafin kudinsu na bara:

Bankin Zenith - N87bn

Bankin Guarantee Trust - N82.4bn

Kamfanin Siminti na BUA - N59bn

Nestle - N55bn

Bankin UBA - N34bn

Stanbic IBTC - N31bn

Bankin Access - N23bn

Lafarge - N16bn

DUBA WANNAN: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka ana wallafawa

FBNH - N13.6bn

Nigerian Brewery - N12bn

Bankin Union - N7bn

Bankin Fidelity - N5.7bn

Transcorp - N5bn

Julius Berger - N4.3bn

Transcorp Plc - N4bn

United Capitals - N3bn

11plc - N2.9bn

Total Nigeria - N2.7bn

FCMB - N2.1bn

Presco - N2bn

Okomu oil - N1.9bn

WEMA - N1.5bn

Infinite Trust Mortgage bank - N1.4bn

African prudential - N1.4bn

May & Baker - N1.3bn

NASCON - 1bn

Daga cikin kamfanoni 47, kamfanoni 31 sun biya sama da Naira biliyan 1 ga masu rike da hannayen jarinsu.

Kwazon da kamfanin manja na Okomu Oil Palm Plc da Presco Plc suka yi, ya nuna cewa sun kasance bajimai a fannin hada-hadar amfanin gona da ya zamto abin lura.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel