Hannun jari: An rasa N222bn a cikin farkon makon nan a Najeriya
A lokacin da cutar COVID-19 ta ke cigaba da jefa tattalin arzikin kasashen Duniya a cikin mawuyacin hali, an shiga kasuwar hannun jarin wannan mako a Najeriya da kafar hagu.
Kasuwar hannun jarin Najeriya ta rasa fiye da Naira biliyan 200 a cikin farkon makon nan kawai. An bude kasuwar ta NSE na makon nan ne ne a jiya Ranar Litinin, 6 ga Watan Afrilu.
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa kasuwar ta shiga sabon mako ne da Naira tiriliyan 10.771. Hakan na nufin kasuwar ta yi asarar Naira biliyan 222 a daidai wannan lokaci.
A makon da ya gabata, an rufe kasuwar hada-hadar hannun jarin ne da Naira tiriliyan 10.993. An yi asarar 2.02% na hannun jarin da ke cikin kasuwar NSE a wannan makon da aka shiga.
Manyan kamfanonin kasar da hannun jarinsu ya yi kasa sun hada da irinsu: Seplat, kamfanin simintin Dangote, kamfanin simintin BUA, BOC Gases Nig. da kamfanin nan na NAHCO.
KU KARANTA: Yunwa ta fi cutar Coronavirus illa a Najeriya - Fasyose

Asali: Depositphotos
Hannayen jarin Cutix, da Learn Africa da kuma kamfanin NAHCO ya yi kasa da 10%. Yanzu darajar kamfanonin ya tashi a kan N1.26, N0.9k da kuma N2.34 na kowane hannun jari.
A wani bangare kuma, gaba ta kai bankin Access wanda su ka saye Diamond Bank a bara. Haka zalika hannun jarin kamfanonin AIICO da Lafarge Africa sun tashi a kasuwar makon nan.
Hannun jarin Bankin nan na WEMA ya kara daraja da fiye da 8.5%. Bankin Fidelity sun ga karin darajar 8.28% a hannun jarinsu a jiyan nan idan aka kamanta da kasuwar a Ranar Juma’a.
A karshen bara ne hannun jari su ka yi daraja sosai a Najeriya. Dama can masu hasashen tattalin arziki sun ce kasuwa za ta bude bayan shugaba Muhammadu Buhari ya zarce a kan mulki.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng