'Shi ne Matsalar Rivers': Malami Ya Fadawa Tinubu Ministan da Ya Kamata Ya Dakatar
- Archbishop King Benny Danson ya bukaci shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Nyesom Wike, yana mai sukar ayyana dokar ta-baci a Rivers
- Danson ya ce matakin dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da ‘yan majalisa ya saba wa doka, sai ya bukaci a janye dokar ta-bacin nan take
- Limamcin cocin ya yi kira ga Tinubu da ya dawo da gwamnan kan aikinsa tare da tilasta ministan Abuja da ‘yan majalisa 27 su bi umarnin kotu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaban kungiyar Archbishops ta kasa (ICA), King Benny Danson, ya bukaci Bola Ahmed Tinubu da ya dakatar da Ministan Abuja, Nyesom Wike
A wata hira da manema labarai a Abuja ranar Alhamis, Archbishop Danson ya soki matakin Tinubu na ayyana dokar ta-baci a jihar Rivers, ya na mai cewa hakan ya saba wa doka.

Asali: Facebook
"Ka janye dokar ta baci a Rivers" - Malami ga Tinubu
Malamin addinin ya ce an dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da mambobin majalisar dokokin jihar na watanni shida ta haramtacciyar hanya, inji rahoton The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Archbishop Danson ya bukaci shugaba Tinubu da ya janye dokar ta-bacin tare da daukar matakin da ya dace don warware rikicin siyasar jihar cikin lumana.
A cewarsa malamin addinin:
"Cikin girmamawa, ya kai shugaban kasa, ayyana dokar ta-baci da ka yi a jihar Rivers ya sabawa kundin tsarin mulki.
"Abin da ya fi dacewa shi ne ka ja hankalin ministan Abuja, mambobin majalisa 27, da kuma gwamna, ba wai daukar matakin da zai haddasa rikici ba."
Malami ya nemi Tinubu ya dakatar da minista
Ya bayyana cewa an kafa kwamitin bincike domin shawo kan matsalar, amma ministan Abuja, Wike, ya ki mutunta kwamitin, tare da raina matakan Fubara.
Danson ya ce idan akwai wanda ya kamata a dakatar, to ya kamata a fara da Nyesom Wike ne, don shi ne matsalar jihar, ko kuma a hada har da shi gwamnan, a dakatar da su tare.

Kara karanta wannan
Rivers: Atiku ya sauya salo, ya roƙi ƴan Najeriya bayan Tinubu ya sanya dokar ta ɓaci
Ya kara da cewa dakatar da gwamna da mataimakinsa yana nufin babu shugabanci a jihar, kuma naɗa tsohon hafsan soja a matsayin shugaban rikon kwarya ya saba wa dimokuradiyya.
Danson ya ce hakan tamkar komawa ne zamanin mulkin soja, wanda ke iya haifar da karin rikici a jihar da ma kasa baki daya.
Malami ya fadi ministan da shi ne matsalar Rivers
Ya ce shi da wasu shugabannin addini sun tuntubi Gwamna Fubara da wasu daga cikin ‘yan majalisar jihar domin tabbatar da zaman lafiya.
Danson ya ce tsohon gwamna Wike da ke tsoma baki a harkokin mulkin Gwamna Siminalayi Fubara, shi ne ke haddasa rikici a jihar, wanda kowa ya san yin hakan ba dai dai ba ne.
"Ranka ya dade, ya ya za ta kasance idan shugaban Muhammadu Buhari ya fara tsoma baki a mulkinka?
Ya za ka ji? Na san ba za ka so hakan ba. Don haka, cikin girmamawa, ina fatan za ka fahimce ni.
"Muna fatan za ka janye matakin da ka dauka, ka dawo da gwamnan kan aikinsa, sannan ka kwabi ministan Abuja da ‘yan majalisa 27 su bi umarnin Kotun Koli."
Majalisa ta amince da dokar ta bacin Rivers
Tun da fari, mun ruwaito cewa, majalisar wakilai ta amince da bukatar shugaba Bola Tinubu na ayyana dokar ta-baci a jihar Rivers yayin zaman da aka gudanar ranar Alhamis.
Daga cikin ‘yan majalisar 243 da suka halarta, dukkansu sun kada ƙuri’ar amincewa da bukatar shugaba Tinubu ba tare da sabani ba.
Haka kuma, majalisar ta yanke hukuncin dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa, da ‘yan majalisar dokokin Rivers na tsawon watanni shida.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng