Natasha: Kungiyar 'Yan Majalisun Duniya Ta Karbi Koken Sanata, Za Ta Ji Ta Bakin Akpabio

Natasha: Kungiyar 'Yan Majalisun Duniya Ta Karbi Koken Sanata, Za Ta Ji Ta Bakin Akpabio

  • Shugabar IPU, Tulia Ackson, ta tabbatar da cewa za a saurari dukkan ɓangarori kafin a yanke hukunci a dakatarwar Natasha Akpoti-Uduaghan
  • Sanatar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta kai karar Sanata Godswill Akpabio a kan zargin an tauye hakkinta saboda zargin shugaban da cin zarafi
  • Ackson ta ce IPU ba za ta yanke hukunci nan take ba, domin dole ne ta saurari duk ɓangarorin da abin ya shafa kafin ta ɗauki mataki na ƙarshe

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

New York, US — Shugabar Ƙungiyar Majalisun Duniya (IPU), Tulia Ackson, ta tabbatar wa da Natasha Akpoti-Uduaghan cewa za a bi doka wajen warware batun dakatarwarta daga majalisar dattawan Najeriya.

Ackson ta bayyana hakan ne a martani ga ƙorafin da Natasha ta shigar a gaban IPU da Majalisar Dinkin Duniya (UN), ta ce an dakatar da ita ba tare da adalci ba.

Kara karanta wannan

Sanata Natasha ta kai karar Akpabio ga kungiyar 'yan majalisun duniya

Natasha
IPU ta karbi koken Natasha Hoto: Natasha H Akpoti
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa a yayin taron mata ‘yan majalisa a taron IPU da aka gudanar a ranar Talata, Sanata Natasha ta bayyana yadda aka dakatar da ita saboda dalilan siyasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisa: Korafin Sanata Natasha a IPU

Leadership ta ruwaito cewa Natasha Akpoti Uduaghan ta shaidawa taron IPU cewa dakatar da ita da majalisar dattawan Najeriya ta yi ya nuna halin da 'yan siyasa mata ke ciki a Najeriya.

Ta ce:

"Na zo ne da zuciya mai nauyi daga Najeriya. Amma na fara ne da neman gafara daga mambobin wannan ƙungiya—ba don in kawo wa ƙasata kunya ba, amma don neman taimako ga matan Najeriya."

Natasha ta bayyana cewa dakatarwar ta ta samo asali ne daga ƙorafin da ta shigar kan Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, kan zargin cin zarafi.

Natasha
IPU za ta saurari bangaren Akpabio kan zargin da Natasha ta yi Hoto: Godswill Obot Akpabio/Natasha H Akpoti
Asali: Facebook

A cewarta:

"Na yi imanin cewa shigar da ƙorafi zai haifar da bincike mai gaskiya da adalci, amma maimakon haka, an dakatar da ni kuma an hana ni yin magana."

Kara karanta wannan

Dalilan da suka ja matan da ke majalisar dattawa suka juyawa Natasha baya

Sanata Natasha ta kuma bayyana cewa dakatarwar da aka yi mata ta janyo mata takunkumi masu tsanani, ciki har da cire mata jami’an tsaro, kwace motar aiki, hana ta albashinta.

IPU ta amshi koken Sanata Natasha

A martaninta, Shugabar IPU, Tulia Ackson, ta tabbatar da cewa ƙungiyar za ta yi nazari kan batun Natasha, amma sai ta saurari ɓangarorin biyu kafin ta yanke hukunci.

Ta ce:

"Mun saurari ƙorafinta, kuma a matsayinmu na ƙungiya, za mu ɗauki matakan da suka dace. Amma dole ne mu ji ta bakin ɗayan ɓangaren ma, kamar yadda al’adar IPU ta tanada."

Haka kuma, Ackson ta bayyana cewa wata wakiliyar Najeriya da ke wajen taron ta nemi yin magana kan batun, amma ba a ba ta dama ba saboda ƙurewar lokaci.

Matakin IPU na duba batun Natasha daga dukkan ɓangarori na nuni da cewa ana sa ran cigaban al’amari yayin da ƙungiyar majalisun duniya ke ci gaba da nazarin shari’ar.

Kara karanta wannan

Akpabio: Majalisa ta lissafo manyan zunuban da suka sanya aka dakatar da Natasha

Natasha ta kai karar Akpabio

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Natasha Akpoti-Uduagha, ta shigar da kara a gaban kungiyar 'yan majalisu ta duniya kan dakatarwar da aka yi mata daga majalisar dattawa.

A yayin jawabi a taron IPU da aka gudanar a hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York a ranar Talata, Sanatar ta zargi Shugaban majalisa, Godswill Akpabio, da saba doka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel