Saukaka Sufuri: Za a Samar da Motoci Masu Aiki da Lantarki 10,000 a Arewa
- Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnatin Tarayya ta amince da samar da motocin lantarki a jihohin Arewa maso Gabas
- A karkashin haka ne gwamnatin Bola Ahmed Tinubu za ta fara jigilar jama’a da motocin lantarki a yankin baki daya a nan gaba
- Majalisar zartaswa ta kasa ta amince da kashe kusan Dala miliyan 100 don sayen motocin lantarki da gina wuraren cajin batir
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta shirya kaddamar da motocin lantarki 10,000 a yankin Arewa maso Gabas.
Hakan na zuwa ne bayan majalisar Zartaswa ta kasa (FEC) ta amince da aiwatar da shirin bayan tattaunawa a makon jiya.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan shirin ne a cikin wani sako da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar gwamnatin tarayya, an ware kusan Dala miliyan 100 domin sayo motocin lantarki da gina wuraren cajin batir saboda rage hayakin da ke gurbata iska.
Za a sayo manyan motoci da Keke Napep
Gwamnatin Tinubu ta amince da kulla yarjejeniya da kamfanoni daban-daban da za su samar da motocin lantarki a Arewa maso Gabas.
Kamfanin Bluecrest Integrated Concept zai samar da manyan motoci masu wuraren zama 17 guda 10 a cikin watanni shida a kan N2.9bn.
Har ila yau, kamfanin Mutual Commitment zai kawo Keke Napep na lantarki 4,000 cikin watanni tara a kan kudi N49.6bn.

Source: Facebook
A daya bangaren, kamfanin shanghai Integrated Infrastructure Development zai kawo Keke Napep 3,000 a kan kudi N37.2bn.
A karshe, kamfanin Sinoma Investment International Limited zai samar da karin Keke Napep 3,000, kuma dukkansu za su rika daukar fasinjoji tara da direba daya.
Za a gina wuraren cajin batir
Bayan sayen motocin lantarkin, an kulla yarjejeniya da kamfanin HNCEGC domin samar da motocin lantarki nau'uka daban daban har guda 237 a kan kudi N16.3bn.
Haka kuma, kamfanin KB Lamah Motors Nigeria Limited zai gina wuraren cajin motocin lantarki a yankin a kan kudi N8.4bn domin tabbatar da aikin ya gudana ba tare da tangarda ba.
Shirin rage hayaki mai gurbata iska
An shirya aiwatar da wannan tsari ne karkashin Hukumar Cigaban Arewa Maso Gabas (NEDC) domin rage hayaki mai gurbata iska da bunkasa makamashi mai dorewa a yankin.
Shugaba Bola Tinubu ya amince da shirin sayen motocin lantarkin tun a watan Oktoban bara. Haka nan ya duba samfuran motocin da batir dinsu a yayin wata ziyarar aiki.
Ana fata hakan zai samar da ayyukan yi ga matasa da rage wahalhalun da suka shafi sufuri a Arewa maso Gabas.
An fara yi wa Tinubu kamfen a Arewa
A wani rahoton, kun ji cewa wasu manya a jam'iyyar APC sun fara nemawa Bola Ahmed Tinubu goyon bayan mutanen Arewa a zaben 2027.
Duk da cewa ba a fara yakin neman zabe a hukumance ba, jiga jigan APC a Arewa sun fara kiran jama'a domin su nuna goyon baya ga shugaba Tinubu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.#
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


