Gwamnatin Katsina Ta Kare Matakin Kulle Makarantu a Ramadan, Ta Tura Sako ga CAN
- Gwamnatin jihar Katsina ta yi ƙarin haske kan matakin da ta ɗauka na rufe makarantu a lokacin azumin watan Ramadan
- Ma'aikatar ilmin firamare da sakandare ta jihar ta bayyana cewa an ɗauki matakin duba da irin wahalhalun da ake sha a azumi
- An ɗauki matakan da za su rage tasirin da daina karatun zai yi ga harkar ilmi a jihar ta hanyar fito da tsarin darussa na musamman
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dikko Umaru Radda, ta kare matakin da ta ɗauka na rufe makarantu a lokacin watan azumin Ramadan.
Gwamnatin ta Katsina ta bayyana cewa ta ɗauki matakan da za su rage tasirin dakatar da karatun zai yi ga harkar ilimi.

Asali: Facebook
Jami'in hulɗa da jama'a na ma’aikatar ilmi firamare da sakandare ta jihar, Sani Danjuma, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa aka rufe makarantu a Katsina?
Ma'aikatar ta bayyana cewa wannan matakin rufe makarantun, an ɗauke shi ne domin daidaita gudanar da ibada da tabbatar da karatu ya samu ci gaba.
Sani Danjuma ya bayyana cewa gwamnati ta yi la’akari da matsanancin yanayin zafi da ake fuskanta a Arewacin Najeriya, da kuma irin wahalhalun da dalibai da malamai ke fuskanta yayin azumi.
"A matsayin martani ga muhawarar da ake yi kan gudanar da makarantu, ma’aikatar ta ƙirƙiro wata dabarar da za ta rage cikas ga harkar ilmi, tare da fahimtar ƙalubalen da ake fuskanta a lokacin Ramadan."
"Umarnin da muka bayar ya tabbatar da cewa ɗalibai, musamman masu shirin rubuta jarabawa masu muhimmanci, za su ci gaba da shirye-shiryensu na karatu."
- Sani Danjuma
Ya ƙara da cewa gwamnati ta tsara darussa na musamman domin ɗaliban da ke shirin jarabawar kammala sakandare (SSCE) a makarantu masu zaman kansu, na gwamnati, da na al’umma, domin taimaka musu su cike giɓin karatun da suka rasa.
Katsina na da doka kan rufe makarantu
Ma’aikatar ta kuma tunatar da jama’a cewa akwai doka a jihar Katsina da ke tilasta rufe makarantu a lokacin watan Ramadan.
"Domin amsa ƙorafe-ƙorafen da wasu masu ruwa da tsaki suka gabatar, ciki har da ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), ma’aikatar tana tabbatarwa da jama’a cewa an fara darussa na musamman daga ranar 3 ga watan Maris, 2025."
"Waɗannan darussan za a tsara su yadda za su dace da dalibai da malamai masu azumi, tare da yin la’akari da yanayin muhallin da ake ciki."
- Sani Danjuma
Muna goyon bayan matakin
Wani malamin makarantar firamare a Katsina mai suna Aminu Umar, ya bayyana cewa matakin kulle makarantun ya taimakawa malamai.
"Mu muna maraba da wannan matakin, kuma dama ai mu a Katsina ba yanzu aka fara ba, ya riga ya zama doka tuntuni."
"Koyarwa a lokacin azumi ana shan wuya, amma da aka kawo wannan tsarin, muna samun sauƙi."

Kara karanta wannan
Rikicin sarauta ya ƙara tsanani, Sarki ya yi sabon naɗin da zai iya tayar da ƙura
- Aminu Umar
Sowore ya soki rufe makarantu a Arewa
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan Najeriya, Omoyele Sowore, ya yi magana da kakkausar murya kan rufe makarantu da wasu jihohin Arewa suka yi saboda azumi.
Omoyele Sowore ya bayyana cewa ko kaɗan bai kamata addini ya hana ilmi ba, ya bayyana matakin rufe makarantun a matsayin jahilci da wawanci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng