An Tsinci Gawar Babban Jami'in Dan Sandan Najeriya a Dakin Otel, Bayanai Sun Fito
- An gano gawar Sufeta Haruna Mohammed a dakin wani otal a Ogun, bayan shigowarsa tare da wata mace da misalin karfe 1:00 na dare
- Manajan otal din ta tsinci gawar jami'in da safe, yayin da aka gano cewa macen da suka shigo tare ta bar dakin tun da sanyin safiya
- Rundunar ‘yan sandan Ogun ta tabbatar da lamarin, tana mai cewa an fara bincike don kamo wace ta gudu da gano dalilin mutuwar jami’in
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ogun - An tsinci gawar Sufeta Haruna Mohammed a dakin wani otal da ke jihar Ogun, lamarin da ya jawo jami’an tsaro suka fara gudanar da bincike.
Rahotanni sun nuna cewa Sufeta Haruna, wanda ke aiki a sashen ‘yan sanda na Ishashi, Legas, ya isa otal din Super G Royal tare da wata mace da misalin karfe 1:00 na daren Asabar.

Asali: Twitter
An tsinci gawar dan sanda a otel
Manajan otal din, Deborah Adejobi, ta ga dakin a bude da misalin karfe 8:52 na safe. A ciki, ta tarar da gawarsa, amma ba a ga macen da suka shigo tare ba, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ‘yan sanda ya nuna cewa mai otal din, Abiodun Olagunju, ya kai rahoton lamarin, yana mai cewa matar da ta gudu ta fito wurin karfe 6:00 na safe don neman ruwa.
Rahoton ya nuna cewa an dauke gawar Sufeta Haruna zuwa dakin ajiye gawa na Life Channel da ke Olambe domin adanawa da bincike.
'Yan sanda sun fara bincike
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta Ogun, ta ce:
“A farko, abin da aka samu a cikin jakarsa shi ne kakin ‘yan sanda, don haka ba za a iya cewa jami’in dan sanda ba ne. Ba a samu katin shaidarsa ko wani abu da zai tabbatar da hakan ba.
“Amma bincike ya nuna cewa mamacin dan sanda ne mai mukamin Insfeto da ke aiki a sashen Ishashi na rundunar ‘yan sandan Lagos.
“An tuntuɓi DPO, kuma an tabbatar da gawarsa ce.”
Odutola ta bayyana cewa jami’an tsaro sun fara bincike don gano macen da ta gudu, yayin da ake ci gaba da kokarin gano hakikanin dalilin mutuwarsa.

Asali: Twitter
Binciken ya tabbatar da cewa Sufeta Mohammed yana aiki a sashen ‘yan sanda na Ishashi da ke a jihar Legas.
Duba labarai da suka shafi 'tsintar gawar dan sanda'
An tsinci gawar ɗan sanda, matarsa da ƴaƴansu 5 a cikin gidansu
An tsinci gawar wani jami'in dan sanda a gidansa a Abuja
An tsinci gawar dan sanda cikin 'yan bindiga da sojoji suka kashe a Filato
An tsinci gawar dan sanda a otel din Abuja
A wani labarin makamancin wannan, mun ruwaito cewa, an tsinci gawar wani jami'in dan sanda, Lawal Ibrahim a wani dakin otel da ke Abuja.
An gano cewa Lawal ya haɗu da wata budurwa Maryam Abba a shafukan sada zumunta watanni uku da suka gabata, inda suka yi sharholiya a otel din.
Asali: Legit.ng